Gwamnonin PDP 5 Sun Kafa Sabuwar Kungiya, Sun Ce Ba Zasu Yiwa Atiku Kamfen Ba

Gwamnonin  PDP 5 Sun Kafa Sabuwar Kungiya, Sun Ce Ba Zasu Yiwa Atiku Kamfen Ba
 

Fusatattun gwamnonin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da aka fi sani da G-5 sun sanar da kafa sabuwar kungiya mai suna ‘Integrity Group’ wato kungiyar mutunci a cikin babbar jam’iyyar adawar a ranar Lahadi, 20 ga watan Nuwamba. Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa a yayin ganawar da tayi a gidan tsohon mataimakin shugaban PDP, Cif Olabode George, kungiyar ta ce babu gudu babu ja da baya a kan hukuncinta na kin shiga kamfen din dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar. 

Gwamnonin karkashin jagorancin Wike sun bukaci shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu yayi murabus domin adalci da daidaito, Daily Nigerian ta rahoto.
Baya ga Wike sauran gwamnonin kungiyar sun hada na jihar Benue, Samuel Ortom, Seyi Makinde na Oyo, Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu da kuma Okezie Ikpeazu na Abia. Gwamnonin sun gana ne da wasu fusatattun shugabannin jam’iyyar adawar a jihar Legas domin sanin matakin da za su dauka. 
Makinde wanda ya zanta da manema labarai kafin ya shiga cikin ganawar, ya bayyana cewa kungiyar ‘Integrity Group’ ita ke jan ragamar fafutukar da a cikin jam’iyyar. Jawabinsa na cewa: “Mun kasance a nan da safen nan don yin wata ganawa ta kungiyar ‘Integrity Group a cikin jam’iyyarmu, ta PDP. Ta kasance na kungiyar G5 wato gwamnonin PDP biyar. G5 ya kasance kungiyar ‘Integrity Group. Kuna iya ganinmu, gwamnoni biyar masu ci, a matsayin fuskokin wannan fafutuka amma shugabanni da dattawan jam’iyyar da kuka gani a nan sune a bayan wadannan fuskokin.