Ƙungiyoyin Matasa Sun Goyi Bayan Takarar Barista Sa'adat Yanusa A Sakkwato

Ƙungiyoyin Matasa Sun Goyi Bayan Takarar Barista Sa'adat Yanusa A Sakkwato
Kungiyoyin matasa a jihar Sakkwato sun yi kira da dattijai da shugabannin jam'iyar APC da sauran jama'a da su goyi bayan Barista Sa'adat Yanusa Muhammad ta zama 'yar majalisar Tarayyar Nijeriya.
 Barista ita kadai ce mace a cikin masu neman  wakiltar kananan hukumomin Bodinga da Tureta da Dange Shuni a Sakkwato.
Jagoran kungiyoyin matasan Alhaji Yusuf Sani a wurin taron manema labarai da ya kira a Jumu'ar nan ya ce Yanusa tana da kwarin guiwar da za ta iya cin zabe in aka yi la'akari da nasarorin da ta samu da gudunmuwar da ta bayar a yankinta da jihar Sakkwato baki daya.
  Barista wadda ita ce ta samar da Gidauniyar Sa'ar  Mata wadda a ƙarƙashinta a samarwa matasa aikinyi mata an koya masu sana'ar dogaro da kai tare da masu lalura ta musamman da mabuƙata.
Sani ya bayyana 'yar takarar tana ba da gudunmuwa domin cigaban ilmi in da take taimakawa ɗalibbai a manyan makarantu bayan sun kammala karatu takan yi kokari a samar musu aiki ko gurabun karatu a ciki da wajen Nijeriya.
 
A cewarsa duk wanda yake da tunani irin nata in aka goyi bayansa ga samun zama mamba a majalisar tarayya al'ummarta za su samu cigaba.
"akwai buƙatar mu goyi bayan mutum irinta dake da sadaukarwa da fahimta da mutane a cikin zuciyarta," a cewar Sani.
Kungiyoyin da suka goyi bayan Barista akwai Gamji Women and Youths Forum, Progressive Network for Democracy (PND), N-Power Volunteers Forum of Tureta local government area.
 
Sauran sun haɗa da APC Door-Door Mobilization of Tureta, Dange-Shuni and Bodinga local government areas, Area Youths Council from the three local government areas among others.
 
Kowace ƙungiya ta goyi bayan ne a daban-daban don nuna abin na cikin zukatansu.