Ku Fara Duba Jinjirin Watan Shawwal Ranar Alhamis----Sarkin Musulmi 

Ku Fara Duba Jinjirin Watan Shawwal Ranar Alhamis----Sarkin Musulmi 

Mai Alfarma Sarkin musulmi kuma shugaban majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ya fitar da sabuwar sanarwa yayin da watan Azumi ya zo ƙarshe. 

Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya roƙi ɗaukacin al'ummar Musulmai a lungu da saƙon kasar nan su duba jinjirin watan Shawwal ranar Alhamis, 29 ga watan Ramadan, 1444AH. 
Daraktan gudanarwa na majalisar kolin harkokin Addinin Musulunci a Najeriya, Arc. 
Zubairu Haruna Usman-Ugwu, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata. 
"Bayan shawarin da kwamitin duban wata ya bayar, Sarkin Musulmi kuma shugaban NSCIA ya roki Musulmai su duba jinjirin watan Shawwal bayan faɗuwar rana a ranar 29 Ramadan, 1444AH daidai da 20 ga Afrilu, 2023." 
"Idan Musulmai suka ga jinjirin watan kuma ya cika sharudɗan kwamitin duban wata, daga nana Mai Marataba Sarkin Musulmi zai sanar da Jumu'a 21 ga watan Afrilu a matsayin 1 ga watan Shawwal, 1444AH kuma ranar Idul Fitr."
"Haka nan idan jinjirin watan ya ɓuya ba'a gan shi ba a wannan rana, ranar Asabar 22 ga watan Afrilu, 2023 zata zama ranar ƙaramar Sallah." 
Daga ƙarshe ya roƙi al'ummar Musulmai, bayan hanyoyin sanar da ganin wata da aka saba a kowane yanki, zasu iya tuntubar mambobin NMSC domin kai rahoton ganin jinjirin watan Shawwal. 
.