An nemi haƙƙin  garkuwa da kashe ƙaramin yaro ɗan shekara huɗu a Sakkwato

An nemi haƙƙin  garkuwa da kashe ƙaramin yaro ɗan shekara huɗu a Sakkwato
Gamanyar kungiyoyin farar hula a jihar Sakkwato sun yi tir da yin garkuwa da tare da kashe  karamin yaro mai shekara hudu Ayman Abubakar a unguwar CBN Quarters dake birnin Sakkwato, an zargi wani makwabci  da wata mata dake cikin unguwar da aikata laifin na yin garkuwa da kashe yaron aka kuma jefa shi a cikin sakawe(ramen tara ruwan bayan gida).
Kungiyoyin suna neman bin hakkin yaron da aka ci zarafin sa domin kare hakkin yara da dokokin kasa suka aminta da su.
A bayanin hadinguiwa da shugaban kungiyoyin na kasa(NACTAL) Abdulganiyu Abubakar da Usman Ahmad Suka, Kodineta na kungiyar kare hakkin yara da Rabi'u Bello Gandi Shugaba a hukumar kare cin zarafin jinsi, suka sanyawa hannu sun bayyana kashe yaron cin zarafi ne da take hakkin yara.
Kungiyoyin sun gabatar da bukatu guda hudu da suke neman biyan bukatarsu, ta hanyar binciken gaskiya da adalci, a hukunta duk wanda ke da hannu wurin  kashe yaron, a rika sanadar da al'umma sakamakon bincike lokaci bayan lokaci, a yi azamar kare hakkin yara.
Sun yi kira ga gwamnatin Sakkwato da Sarakunan gargajiya da hukumomin tsaro su hada kai don tabbatar da gakiya kan yaron da aka kashe.
"Kare hakkin yaron dan Nijeriya lamari ne da yakamata a baiwa fifiko a kasa, a daina wasa da shi,"kalamansu.
Mahaifin Ayman Dakta Abubakar ya roki al'umma su ba shi goyon baya a kwato hakkin dansa, ya fadi yanda dansa ya bata a 29 ga watan Maris bayan ya dawo sallar La'asar.
An gano gawar yaron a ramen sakawe a cikin unguwa bayan sati bakwai da batansa, an kama wadanda ake zargi suna hannun 'yan sanda a tsare.
Kungiyoyin farar hular sun sha alwashin biyar lamarin kai da fata tare da mahaifan yaron yin adalci ga Ayman adalci ne ga kowa."