‘Yan bindiga sun kashe jami’an tsaron Sakkwato 7

‘Yan bindiga sun yi jami’an tsaro mallakar jihar Sakkwato kwantan bauna in da suka kashe mutum bakwai a karamar hukumar hukumar Gudu ta jih ar Sakkwato.
‘Yan bindigar da suke da yawan gaske sun kawo samamen ne a ranar Litinin data gabata, in da suka sace shanun wani Buzu a kauyen Karfen Sarki, suna a garin na Karfen Chana suka kashe jami'an ba tare da sun dauki komai ba.
Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Gudu da Tangaza Honarabul Sani Yakubu ya halarci janazar jami'an in da ya tabbatar da kashe jami'an tsaron su bakwai, ya ce mutanen suna kokari wurin tsare garuruwansu, abin da ya faru kadara ce don sun saba da aikin, barayin sun rinjaye su ne kawai domin matsalar kayan aiki da har yanzu ba a basu ba sama da wata biyar da yaye su, da yawan jami'an ba su da kayan aiki.
"Maharan sun shigo sun harbi manoma har suka kashe manoma biyar suka sace shanu da yawa, kashe gari suka sake dawowa abin da ya sa jami'an suka yi yunkurin kare al'ummarsu, 'yan bindigar sun fi su yawa da makamai anan ne suka fatattake su har aka kashe mutum 7.
"Muna ganin laifin gwamnati domin tana da abin da za ta yi ba ta yi ba domin akwai sojoji da 'yan sanda ga kuma kantoman karamar hukuma da yake wakilin gwamna a karamar hukuma," a cewarsa.
Ya ce a matsayinsa na wakili zai sake gabatar da kudiri a majalisa kan matsalar tsaron yankinsa domin a yi wani abu kan matsalar, ya tallafa wa iyalan mamatan, da alkawalin aika masu da abincin da za su yi amfani da shi.