Basira Ta Tafi: Barista Mu'azu Liman Yabo Ya Rasu A Abuja

Basira Ta Tafi: Barista Mu'azu Liman Yabo Ya Rasu A Abuja

Hakika Allah ya yi Gaskiya, Dukkanin Mai Rai Mamaci Ne!

Managarciya ta  samu labarin Allah Ya yi wa Barrister Muazu Liman Yabo rasuwa a Birni Tarayya Abuja!

Kafin Rasuwarsa, Barrister ya kasance daya daga cikin masu sharhi akan lamuran Yau da kullun a jihar Sokoto da Najeriya baki daya, mutum ne mai matuƙar basira da kaifin tunani.

Tabbas al'umma sun shede shi da tsage gaskiya da Kokarin yiwa kowa adalci.

 Kafin Rasuwarsa Yana fama da ciyon shuga inda a watannin baya ya kwanta a asibitin UDUTH daga bayan nan aka tafi dashi Abuja.

An samu giɓi sosai a farfajiyar sharhi kan lamurran yau da kullum a jihar Sakkwato.