Ƙungiyar NRC Da IFRC Sun Horas Da Matasa 30 A Sakkwato
A lokacin horaswar jami'in da ke kula da Lahiya na kungiyar Dakta Salisu Buhari na Jami'ar Usmanu Dan fodio ya gabatar da kasidu da hotuna domin samun fahimtar aikin da za su je su yi. Anasa jawabin sakataren kungiyar dake nan jihar sakkwato Malam Shehu Dake ya ja hankalinsu da su jajirce su yi abun da aka koyar da su.
Kungiyar bayar da agajin gaggawa ta Duniya NRC da IFRC sun horas da matasa 30 a yankunan ƙananan hukumomin Yabo, Shagari da Bodinga domin su shiga lungu da sako su fadakar da jama'a hanyoyin kariya da ɗaukar matakin kan annobar gudanawa da amai watau (cholera) a yankunansu.
managarciya