Barnar 'Yan Bindiga Na Karuwa Sun Sace Hakimi Tare  Da Mutum Biyar  a Jihar  Zamfara

Barnar 'Yan Bindiga Na Karuwa Sun Sace Hakimi Tare  Da Mutum Biyar  a Jihar  Zamfara

 

'Yan bindiga sun sace hakimin garin Ruwan Rana a karamar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara, Magaji Makau da wasu mutane biyar a safiyar ranar Asabar. 

Hakazalika, an kuma kashe wani mutum yayin harin. 
Wani mazaunin garin, Muhammad Musa, ya fada wa The Punch cewa, yan bindigan biyu da suka taho kan babur sun shigo garin Rana da asubahin ranar Asabar. 
Musa ya ce yan bindigan, wadanda suka iso garin misalin karfe 3 sun fara harbe-harbe sannan daga bisani suka fara zuwa gida-gida suka sace hakimi da wasu fitattun mutane biyar, Vanguard ta rahoto. 
Ya kuma yi bayanin cewa sun kashe wani mutum daya da ya ki yarda a tafi da shi. 
Ya ce: "Mun ji karar harbi misalin karfe 3 na safe kuma koya ya boye saboda mun san yan bindigan sun taho sace mutane ne. "Sun rika zuwa gida-gida kuma suka sace mutane biyar ciki har da hakiminmu, sun harbe mutum daya, daga baya suka koma daji. 
"Ban san wadanda suka sace ba sai da gari ya waye na fito na ji cewa hakimi, Alhaji Makau na cikin wadanda aka sace.
Wani dan majalisar jihar mai wakiltar yankin, Hon. Hamisu Faru, ya nuna barin ransa kan lamarin yana mai bada tabbacin za a ceto wadanda aka sace. 
Ya ce: "Jami'an tsaro na kokarin ceto hakimi da sauran mutanen biyar." 
Ba a samu ji ta bakin kakakin yan sandan jihar, ASP Yazid Abubakar ba, don ba a same shi ba lokacin hada wannan rahoton. 
A bangare guda, Kabiru Ahmadu, dan majalisar tarayya mai wakiltar Gusau da Tsafe a Zamfara ya fadi abin da yan bindiga ke bukata daga gwamnati. 
A cewarsa yan bindigan sun tsananta hare-hare ne don suna neman gwamnati ta nemi yin sulhu da su.