Wasu miyagu da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne sun ƙona wata mata da surukarta da kuma ƴaƴanta biyu da ransu a wani harin da suka kai a jihar Sokoto.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ƴan bindigan sun kai harin ne a ƙauyen Kurya da ke ƙaramar hukumar Rabah a jihar Sokoto da misalin ƙarfe 8:30 na daren ranar Lahadi.
Rahotanni sun ce ƴan bindigan sun kashe mutanen ƙauyen 12 tare da sace mata uku a yayin harin.
Wani mazaunin yankin, Yusuf Garba ya ce ɗaya daga cikin wadanda aka sace ta rasa mijinta a harin, rahoton Trust Radio ya tabbatar.
“Daga cikin wadanda aka kashe akwai wata mace ɗaya da aka ƙona ta mutu tare da surukarta da ƴaƴanta biyu a cikin ɗakinsu.” A cewarsa.
A cewarsa, daga baya maharan sun yi wani ƙazamin faɗa da sojoji. “Muna zargin su ma sun yi asara mai yawa saboda mun ga tabon jini a inda suka ajiye babura. Amma ka san ba sa barin gawarwakinsu a baya.” A cewarsa.
Sai dai rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da mutuwar mutum bakwai ne a yayin harin.





