Yau Tinubu zai fara kare nasarar zaɓensa a gaban kotu

Yau Tinubu zai fara kare nasarar zaɓensa a gaban kotu

 

A yau Talata ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai bude kariya a kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa, PEPC, domin kare nasarar da ya samu a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

 
Wannan na cikin karar da jam’iyyar PDP da dan takararta na shugaban kasa, Abubakar Atiku su ka shigar.
 
Lauyan Tinubu, Wole Olanipekun, SAN, ne ya bayyana haka a jiya Litinin bayan da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta kammala bada bayanan karar ta da shigar a kan Atiku bayan ta kira wani mai shaida ƙwaya ɗaya tilo.
 
Hukumar zaɓen ta bude tare da rufe karar da ta shigar a kan masu shigar da karar bayan da ta kira sheda daya tilo, Lawrence Bayode tare da gabatar da wasu takardu a cikin shaida.
 
Mai shari’a Haruna Tsammani, shugaban kwamitin sauraron ƙararrakin mai mambobi biyar ne ya sanya yau Talata a matsayin ranar da Tinubu zai fara kare nasarar zaɓen na sa a kotun.