Juyin Mulkin Nijar: Shugabannin ECOWAS Sun Dauki Mataki Na Gaba Don Wa'adin Da Suka Bayar Ya Cika

Juyin Mulkin Nijar: Shugabannin ECOWAS Sun Dauki Mataki Na Gaba Don Wa'adin Da Suka Bayar Ya Cika

 

Shugabannin ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS) da ƙungiyar tarayyar Afirika (AU) sun yi taron gaggawa a ranar Lahadi, 6 ga watan Agusta. 

Shugabannin sun gudanar da taron ne domin tattaunawa kan mataki na gaba da za su ɗauka bayan juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar.
Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, taron gaggawar an gudanar da shi ne bayan wa'adin miƙa wuya da da ƙungiyar ECOWAS ta ba sojojin juyin mulkin ya ƙare a jiya Lahadi. 
An tattaro cewa ƙungiyar ECOWAS za ta sake shirya wani taron a cikin kwanaki masu zuwa domin cimma matsaya kan matakin da za su ɗauka na gaba. 
"Shugabannin za su sake zama domin cimma matsaya kan mataki na gaba da za su ɗauka. Amma ba a sanya ranar da za a sake yin taron ba inda za a ɗauki matakin ƙarshe kan yadda za a magance matsalar dake faruwa a Jamhuriyar Nijar." 
Sai dai shugabannin sun yi shiru kan abin da suka tattauna a taron ba tare da an sanar da duniya ba har yanzu babu bayani kan abin da suka tattauna kan kasar Nijar.