Yaushe ne Kwamitin gano Maboya da Hana sumogal na abinci da Gwamnan Sokoto ya kafa zai fara aiki?

Yaushe ne Kwamitin gano Maboya da Hana sumogal na abinci da Gwamnan Sokoto ya kafa zai fara aiki?

Gwamnan Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu Sokoto ya kafa Wani kwamitin mutum 12 karkashin jagorancin daya daga cikin jigogin jam'iyar APC a jiha  Alhaji Dalhatu Sidi Mamman don gano wurararen da aka boye abinci da hana yin fasakwabrin abinci zuwa kasashen ketare ko hakan zai sa jama'a su samu saukin rayuwa.


Kwamitin da aka kafa kwana uku da suka  gabata har yanzu bai soma aiki ba duk da lamari ne gaggawa ganin yadda ake cikin tsadar rayuwa.


Gwamnan Sakkwato ya bayyana abubuwa biyar da yake bukatar kwamitin ya aiwatar kamar yadda takardar da gwamnati ta fitar da sahannun Mai magana da yawun Gwamna Abubakar Bawa.


"A gano hanyoyin da masu fasa kwabri ke bi da kuma hanyoyin dakile su."


Na biyu "a gano in da ake boye abinci a fitar da shi a sayarwa mutane. A binciko masu boye abinci da masu yin sumogal na abincin a Kuma hukunta su."


A takardar ya bayyana na hudu dana biyar "a dauki matakin wadata jiha da abinci. A rika sanar da sakataren gwamnatin jiha aiyukkan kwamiti lokacin bayan lokaci.


Don sanin dalilin da ya Kawo tsaikon soma aikin wakilinmu ya nemi jin ta bakin shugaban kwamitin sai dai hakan bai samu ba domin wayarsa ba ta shiga.