Kwamitin Ilmi Na Sarkin Musulmi Za Su Kashe Miliyan 38 A Kwalejin Nagarta Ta Sakkwato

Kwamitin Ilmi Na Sarkin Musulmi Za Su Kashe Miliyan 38 A Kwalejin Nagarta Ta Sakkwato

 
Daga Muhammad Nasir.

Kwamitin bunkasa ilmi a jihar Sakkwato karkashin jagorancin Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar sun amince da kashe sama da miliyan 38 domin gyara wasu gine-gine da suka lalace a kwalejin Nagarta wadda tana cikin dadaddun sikandare dake birnin jihar Sakkwato.
Manufar aikin domin kara samar da yanayi mai kyau ga dalibai da malaman makaratar.
Shugaban kungiyar tsoffin dalibban makarantar(NOBA) Alhaji Sani Musa shi ne ya sanar da hakan a Sakkwato ya ce kungiyar ta kashe sama da miliyan 97 dalibban makarantar a fannoni daban-daban a harkar karatu, haka ma kungiyar ta kashe sama da miliyan 50 a wurin gyara wasu gine-ginen makaranta da samar da ruwa a makarantar.
Babban taron da ake gudanarwa a duk shekara an samu nasarar a bana ta  gudunmuwar miliyan 24 na kalandar da aka kaddamar da sitika da mujalla.
Haka ma shugaban a jawabin bayan taro da suka fitar ya yabawa Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal kan gudumuwa da goyon bayan da yake baiwa makarantar da kuma umarnin da ya bayar na cire duk wani shago  da aka lika a ginin makarantar ba bisa ka'ida ba.