Zaɓen Ƙato Bayan Ƙato: Rigimar Gwamnoni Da 'Yan Majalisar Tarayya Ta Ƙara Ƙamari

Zaɓen Ƙato Bayan Ƙato: Rigimar Gwamnoni Da 'Yan Majalisar Tarayya Ta Ƙara Ƙamari
 
Zaɓen Ƙato Bayan Ƙato: Rigimar Gwamnoni Da 'Yan Majalisar Tarayya Ta Ƙara Ƙamari
Kungiyar Gwamnonin APC sun kadamar da sanya kafar wando guda tsakaninsu da 'yan majalisun tarayyar Nijeriya da suka ci gajiyar zaben fitar da gwani na delegate amma yanzu suka yi a kawo zaben kai tsaye waton kato bayan kato.
Kungiyar Gwamnonin a jam'iyar APC sun ga laifin 'yan majalisar tarayya da suka yi sumogalin dokar da ke da rikitarwa a cikin tsarin yi wa dokar zabe gyaran fuska.
Babbab Darakta na kungiyar Dakta Salihu Muhammad Lukuman ya sanar da hakan a Abuja ya ce shigo da wannan dokar a tsarin fitar da dan takara akwai kasawa a lokacon samar da dokar.