ƘASAR KAMOLIYA: Labarin yadda ta magance matsalar tsaron da ta yi fama da shi

Zare farin tabaraun dake  manne a idonsa ya yi yana faɗar "Innalillahi wa innailaihir raji'un. Haka matsalar tsaro ta ta'azzara a ƙasata? Tabbas gwamnatin da ta shuɗe ta yiwa wannan ƙasar babbar illah ko da yaushe sai labarin kisa kake ji."

ƘASAR KAMOLIYA: Labarin yadda ta magance matsalar tsaron da ta yi fama da shi

ƘASAR KAMOLIYA


Rukayya Ibrahim lawal

Wani tsoho da ba zai haura shekaru tamanin da biyar ba a duniya ne zaune a kan wasu luntsuma-luntsuman kujeru na alfarma. Idonsa sanye yake da siririn farin tabarau yayin da idonsa ke kafe a kan ƙatuwar talabijin ɗin bango dake manne a bangon falon ya na kallon Labaran duniya da ake haskawa ƙarfe tara na dare.
Wannan mutumin ba kowa ba ne face Dr Abubukar Muhammad Mamalawa (Shugaban ƙasar Kamoliya)
Zuwa jimawa kaɗan aka hasko Labarin matsalar tsaro a ƙasar, inda aka hasko hoton gawarwakin mutane bila adadin da ƴan bindiga suka yiwa kisan gilla ta hanyar zuba masu ruwan alburusai a garin Manaliya.
Zare farin tabaraun dake  manne a idonsa ya yi yana faɗar "Innalillahi wa innailaihir raji'un. Haka matsalar tsaro ta ta'azzara a ƙasata? Tabbas gwamnatin da ta shuɗe ta yiwa wannan ƙasar babbar illah ko da yaushe sai labarin kisa kake ji."
Wayarsa dake gefensa ya janyo ya kira ɗaya daga cikin masu ba shi shawara kan sha'anin tsaro (Alhaji Aminu A Iyantawa.) Yana ɗagawa ya fara magana cikin yaren ƙasar ya ce "Gobe da misalin ƙarfe tara na safe ka same ni a babban Ofishina. Yana gama faɗa bai jira amsarsa ba ya kashe wayar ya ajiye ya na jimami.

Haka kuwa aka yi ƙarfe tara na safe daidai a Fadar Shugaban ƙasa dake babban Birnin tarayyar Analiya ta yiwa Alhaji Abubakar.
Kai tsaye ya isa har Babban Ofishi ba wanda ya yi yunƙurin dakatar da shi daga jami'an bada kariya dake Fadar. Bayan sun gaisa da mai girma shugaban ƙasa ya ce "Ranka ya daɗe ga ni na zo."
"Yawwa dama abinda ya saka na nemo ka, kai ne na fi aminta da kai duk a cikin masu ba ni shawara. Shin me kake ganin gwamnatin ƙasa za ta iya yi game da sha'anin tsaro a ƙasar nan?" Dr Abubukar ya faɗa.
Gyaran murya Alhaji Aminu ya yi sannan ya ce "Ranka ya daɗe, gaskiya gwamnatin da ta shuɗe ta yiwa ƙasar nan babbar illah ta yanda gyaranta sai an dage kuma an bi a hankali....." Shiru ya yi ya na tunani. Can kuma ya ce "Yawwa a garin Kunir akwai wani ɗalibin Fasaha da na samu labari ya na karatu a kwalejin Maheer Fasaha ta garin, akwai shi da kaifin basira sosai, ya kuma ƙware a harkar sarrafa na'ura ga shi da hangen nesa, mawuyacin abu ne ya bayar da shawara bata fita ba, sai idan shi za mu nemo."
Gyaɗa kai Dr Abubukar ya yi ya ce "Daidai kenan, na baka nan da kwana biyu ka nemo shi ka kawo shi nan a sirrance. Ba na so kowa ya san abinda muke shiryawa har zuwa sanda komai zai kammala, ka riƙe Amana. Kada ka manta rantsuwa na yi akan zan kare hakkin al'ummar dake rayuwa a wannan ƙasar, wannan nauyi ne a kaina."
"Insha'allah Ranka ya daɗe zuwa jibi zaka gan mu." Ya na gama faɗa ya nemi izinin tafiya, ya fice daga Ofishin.
barin Ofishin ke da wuya ya lalubo Abokinsa da ya samu labarin Matashin a gunsa don ya sada shi da Saifullahi Isah Annur. Ba musu Abokin nasa ya aiko masa da number Saifullahi sannan ya kira ya shaida ma Saifullahin.
Kiransa Ya yi ya bayyana masa buƙatar shugaban ƙasar sannan ya tura masa kuɗin abun hawa da alƙawarin gobe zai zo Birnin Analiya.
Saifullahi ya yi matuƙar mamaki da ya samu wannan kiran. Sai dai ba abun mamaki ba ne idan ya yi la'akari da tarin baiwar da Allah ya masa, Wannan baiwar ce ke janyo manyan mutane cikin rayuwarsa.
Ranar Lahadi da misalin ƙarfe huɗu na yamma Saifullahi ya dira Analiya. Waya ya kira ya shaidawa Alhaji Aminu ya ƙaraso.
Washegari tun ƙarfe tara Alhaji Aminu ya ɗauke shi a motarsa bayan Saifullahin ya rufe fuskarsa da Amawali, suka tafi Fadar shugaban ƙasa.
Basu jima da isa ba shugaban ƙasa ya bayyana a Ofishin. Bayan sun gaisa ya nemi  Alhaji Aminu da ya ba su guri don su yi tattaunawar sirri. Fita Alhajin ya yi ya kasance saura su biyu jal a Ofishin.
"Na samu labarin ƙwarewarka a fasaha da iya bada shawara shi ya sa na nemo ka don yin wani sirri tsakaninmu fatan zaka riƙe Amana."
"Insha'allah!" ya faɗa cikin sanyi.
"Game da matsalar tsaro a ƙasar nan meye mafita?" Dr Abubukar ya tambaya.
Gyara zama Saifullahi ya yi sannan ya ce "To Ranka ya daɗe, abu ne dake buƙatar lura da kuma kashe kuɗi kafin a samar da shi. Tsaro ba zai taɓa samuwa ba a ƙasar nan har sai an baiwa kowa haƙƙinsa, sannan a samar da waɗannan abubuwan; zaƙulo masu laifi daga kowanne ɓangare na ƙasa, sannan a hukunta su dai-dai da laifinsu. A samar da kayan yaƙi na zamani sa'annan a koyawa jami'an tsaro sabbin dabarun yaƙi da kama masu laifi cikin sauƙi. A tabbatar da an saka kishin ƙasa cikin zukatan jami'an tsaro sannan a kiyaye masu haƙƙoƙinsu. A dinga bada tallafi ga Manoma da Makiyaya, domin da ɗan gari akan ci gari. Samar da bayanan sirri daga al'ummar kowanne yanki a ƙasar nan da kuma ba su tabbacin riƙe sirrin waɗanda suka kawo bayanan sirrin, in son samu ne a samar da hanyoyin da ba lallai sai mutum ya je Ofishin jami'an tsaro ba. Ko a samar da lambobi na musamman da idan ka kira kai tsaye za su sada ka da ɗakin iko domin a kawo maka ɗauki cikin lokaci. Sai kuma a samar da hanya mafi sauƙi da za a iya bin diddigin kowanne layi da al'umma za su yi amfani da shi, ta yanda za a iya kama masu aikata laifi cikin sauƙi, ta hanyar amfani da na'ura. Haka Sarakunan gargajiya da Hakimai su sanya ido sosai akan shige da ficen al'ummarsu, idan sun ga baƙuwar fuska a bincike ta. Duk wata ƙasar da ta cigaba suna da irin nasu hanyoyin da suke magance matsalolinsu cikin sauƙi. A taƙaice dai wannan ita ce shawarata."
Jinjina kai Dr Abubukar ya yi ya ce "Hikima Zinariya, tabbas ka cika mai fasaha. Kai tsaye na naɗaka shugaban wannan tafiyar ta samar da hanyar tsaro. Sa'annan na baka wuƙa da nama."
"Ina godiya ranka ya daɗe."
"Shekarunka nawa ne?" 
"Talatin da biyar." Ya bada amsa.
Teburin dake gabansa ya janyo ya ciro wata ƙaramar waya ya miƙawa Saifullahi ya ce "Ka riƙe wannan a sirrance akwai layi a ciki, da ita za mu dinga magana saboda gudun matsala."
Godiya ya ƙara yi sannan Dr Abubukar ya kira Alhaji Aminu dake jira a ƙaramin Ofishi ya zo suka fice tare don gudun zargi.
Ranar talata Saifullahi ya koma Jiharsa sannan ya shiga shiri gadan-gadan. Da kansa ya zaɓo Amintattunsa ya sako su cikin shirin domin su taimaka masa ɓangaren aikin da za a yi da na'ura.
Tun daga ranar Saifullahi bai kuma taka ƙafarsa fadar shugaban ƙasa ba don kaucewa matsala.

A haka Saifullahi ya ci gaba da tara Ma'aikatansa. A kowacce Jiha dake ƙasar ya na da Ma'aikata sama da guda Ashirin ƙwararru akan harkar na'ura. Duk da cewa shi da Ma'aikatan nasa dake wata jihar basu san juna ba. 
Duk wasu kuɗi da zasu buƙata don yin aikinsu suna fitowa ne kai tsaye daga asusun gwamnatin ƙasa.
Ɓangaren shugaban ƙasa kuwa ya gyara lamurran jami'an tsaro, an ninka masu albashinsu akan wanda suke karɓa a baya.
Shugaban ƙasar tare da Saifullahi suna ci gaba da gudanar da aikinsu cikin sirri ta yadda ba wanda ya sani.

Cikin wata shida Madatsa suka zaƙulo duk waɗanda ke da sa hannu a cikin dagulewar tsaro a ƙasar. Saifullahi kuwa ya aika jerin sunayen kai tsaye wa shugaban ƙasa.
A haka Dr Abubukar ya bi jerin sunayen baya sassautawa duk wanda sunansa ya zo a cikin masu lalata masa ƙasa komai kusancinsu kuwa. Sa'annan duk wanda aka kama kai tsaye hukuncin kisa ake yanke masa. A cewarsa barin su a raye Babbar matsala ce, domin wake ɗaya ke ɓata iri.
Alhamdulillah! Wannan tsarin da Shugaban ƙasar Kamoliya ya fito da shi ya yi tasiri sosai. Cikin abunda bai fi shekara Uku ba ƙasar ta zauna lafiya, aka daina zubar da jini ba sauran ta'addanci.
Shugaban ƙasar ya yabawa ƙoƙarin Saifullahi da aiki tuƙuru da ya yi hakan ya saka ya ƙara masa matsayi akan wanda ya ba shi, domin duk sha'anin da zai yi sai ya nemi shawarar Saifullahin a sirrance.
Hakan bai manta da Alhaji Aminu ba shi ma ya ƙara masa matsayi.
A ƙarƙashin shawarar Saifullahi shugaban ƙasa ya samar da tallafi na musamman ga Matasa zauna gari banza, gajiyayyu da kuma Mata sa'annan an samarwa mafi yawan matasa da suka yi karatu ba aiki aikin yi . A cewar Saifullahi Matasa su ne ƙashin bayan Al'umma sa'annan rashin aikin yi ne ke janyo masu faɗawa aikin ta'addanci saboda kuɗi ƙalilan.
Hakan ya ƙarawa Shugaba Abubakar Muhammad Mamalawa farinjinin a gurin al'ummar ƙasarsa. Sai fatan alkhairi da gamawa da duniya lafiya da suke masa.


Tammat bi hamdillah.

08109634202