INA DA HUJJA: Labari mai sosa Zuciya, Fita Ta 14    

Daram ! Gaban Lantai ya faɗi, "Yau kam Yaya Isah ya kwabsamin na rantse da Allah, gaban Malam Muntasir zai ambaci littafi?" Tunanin Lantai kenan a zuciyarta amma da yake ba a binta bashin magana sai ta ce,  "Tabbas yau ne amma sai dare ai, daya ke kuma ga Malam ya dawo sai ya dinga karanta mana ai mu duka muna koya."

INA DA HUJJA: Labari mai sosa Zuciya, Fita Ta 14    

Page 14

 

 

Turus Lantai tayi ganin Malam Muntasir zaune yayi kicin-kicin da fuska, babu alamar fara'a ko kaɗan akan fuskarshi.

 

Ayarin Barbushe kuwa suka dinga ihu suna karta wuƙaƙe tartsatsin wuta na tashi, yadda hankalin mutanen wajen zai tashi sosai.

 

Mai gari ya rarrafa ya kamo hannun Lantai cike da karayar zuciya yace, "Don darajar Allah Lantai ki mana haƙuri ni Wallahi ban san Uban da ya kwashe maganarki ya gayama Lado ba."

 

"La"ila ! Mai gari daga maida magana sai ka zageni ?

 

Ba mai gari ba hatta mutanen gun cikinsu sai da ya juya, idan ka cire Malam Muntasir dake ta kallonsu, musamman Barbushe.

 

Barbushe ya daka uwar tsawa cike da muryar ƙauraye yace, "Ina Lado mai ƙarar kwana daya taɓa min ƙanwa Nuratu ? Su waye iyayensa a ƙauyen nan ? Su waye maƙwabtansa a ƙauyen nan?

To baki ɗaya yau ƙanwata Nuratu ta ce duk ku ji bala'i da masifa tare da ƙuncin da taji a ranta akan abin da Lado yayi mata.

 

Kun san da a taɓa min Nuratu gyara an mareni, da kuwa a mareni gwara an kashe ni .

Duk wanda ke da jarumtar kashe Barbushe kuwa har zuwa yanzu Kakan Ubansa bai zo duniyar ba."

 

 

Waje yayi tsit, kowa na karanto duk addu'ar da ta samu a ranshi.

 

"Nuratu Kabir zo nan." Cewar Malam Muntasir.

 

Sai kallo ya koma kansa baki ɗaya.

 

Lantai kuwa sadda kanta ƙasa tayi tana jin bata ji daɗin zuwansa ba, so tai yau a saka mutanen ƙauyen sharar garin da wanke bishiyoyin ƙauyen yadda sai sun gaji don kansu suna bata haƙuri suna kuka, to amma zuwan Malam Muntasir ya wargaza komi, domin dai duk yadda take son Barbushe bai kai yadda take son Malam Muntasir ba.

 

Shi kuma Barbushe sai ya ɗauka Yayanta ne na birni Hafiz da take yawan magana don haka sai ya share bai tanka ba, saboda yana son duk abin da Nuratu ke so.

 

"Nuratu Kabir yaushe kika zama ƴar daba mai kashe mutane ?

Nuratu a she rashin jin naki har yayi yawa haka ?

Nuratu me yasa kika haka ne ?

Kina so mu ɓata da ke ne ?

 

Da sauri ta kalleshi, ("taya zan bari mu ɓata bayan gunka nake samun littafan Jarumi Nasimat? Ai kai duk inda kake dole na zama inuwa a gun na rantse da Allah ƙafarka-ƙafata Malam.")Tunanin da take a zuciyarta kenan wanda ko shakka babu da gaske take.

 

Zumɓura baki tayi, "Yo ni Malam ramanin za ai dukan da yayi min ai.

Kuma ai daman nace ka daina dukansa nayi Allah ya isa ne daman saboda nasan ta nan zan farke ai, domin ba a Allah Ya isa sai ga wanda kake jin tsoro ni kam ai ba tsoronsa nake ba kasan.

Malam Muntasir sai abin ya ba shi dariya ma.

"Kenan duk wanda kaima Allah Ya isa tsoronsa kake ji ko Nuratu ?"

"Tabbas Malam shi ya sa kaga ban yin Allah Ya isa ni duk gumu sai na fitar da haƙƙina."

 

"To yanzu abin da nake so ki tarkata ƙaurayenki su koma inda suka fito ko ranki ya ɓaci yanzu Nuratu."

 

Marairaicewa tayi tana son yin kuka.

"Shike nan yanzu Lado ya daki banza ya yaga min littafi a wofi ?"

 

"Yawwa, wai ni kam ina littafin da aka yaga ɗin ne Nuratu ?"

 

"Cab nan fa ɗaya, Malam ai ko me za kai baka ganin littafin nan Wallahi...

"Nuratu ina magana kin banza da ni."

 

"Malam ai saboda mugun jin haushin an gaya littafin na toyeshi don duk sanda na ganshi raina ɓaci zai, Yayana Barbushe kuwa yace da raina ya ɓaci gwara ruwa ya cinye ƙauyen nan."

 

Idan ya fahimci yarinyar so take ta ba shi tsoro da maganar Barbushe.

 

Murmushi kawai yayi ya nufi gun Barbushen .

 

Sai da hantar cikinta ta kaɗa ganin yadda ya doshi gun Barbushe ba alamar tsoro.

 

Ko da ya isa ya miƙa ma Barbushe hannu, sai da yaran Barbushe suka runtse ido cikin tsorata domin sun san duk wanda ya miƙa ma Barbushe hannu karya hannun yake ba ruwansa.

 

Kasancewar Lantai tasan hakan yasa ta rugo da gudu ta shiga tsakaninsu fuska cike da razana ta ce, "Yayana ga wanda nake baka labarinsa Malamin da yake matuƙar kulawa da ni a makaranta bai barin kowa ya dake ni, ko da Lado na duka na shi ne ya kama Lado da duka, fatan zaka so shi tunda yana sona shima?"

 

Sai kawai Barbushe ya dafa kafaɗar Malam Muntasir.

 

Hatta Musa dake zaune da wutarsa ta ɗauke baki ɗaya har ya fara jin me yasa ya kira bawan Allah haka kawai za a karya shi a banza.

 

"Da kyau Malamin mu fatan zaka cigaba da kulamin da ƙanwata idan ta koma makarantar ?"

Cewar Barbushe yana kallon Malam Muntasir.

 

Murmushi yayi domin ya yadda da abin da Musa ya gaya ma shi yanzu, Lantai ke juya Barbushe don haka shiga komar Lantai tamkar shiga ramin Kura ne.

 

Tabbas ya fahimci yadda gayen yayi niyyar aikata masa wani abin amma zuwan Nuratu da maganarta yasa nan take ya fasa har murmushi ya ƙwace a kan fuskarsa nan take.

 

Cike da nuna boko Malam Muntasir ya dubi Barbushe yace,  "Abokina ka daina biyema yarinyar nan tana saka aiki tana datse maka naka aikin indai Nuratu ce to kullum sai ta saka aiki bata san ta ga an zauna baki alaikum."

 

Murmushi yayi "Ai ni Nuratu birgeni take, don tamkar ƙanwata ta jini haka nake kallonta don haka ba zan gajiya ba akan dukkan lamurranta ba." Cewar Barbushe.

 

Su mai gari sai zare ido suke, Lantai na masu gwalo.

Malam Muntasir ya sake murmusawa, "Abokina ka daina biye mata, ai ta kusa fara zuwa makaranta kowa ya huta da fitinarta ma."

 

"Haba dai Malam ai mai lafiya shi ke abin da ya so, Allah dai ya ƙara ma Nuratu lafiya shi ne fatana."

 

Ko da su mai gari suka ga Barbushe ya sauya bai da alamar yi masu rashin mutuncin sai suka miƙewa ɗaya bayan ɗaya suna kai gaisuwa gareshi.

 

Fuska a ɗaure Barbushe ke tambayar ina yaron daya daki Nuratu?

 

Mai gari kuwa bai zo gidansu Lantai ba sai daya kai Lado ya ɓoye, don haka yayi wuƙi-wuƙi da idanu ya rasa amsar da zai ba da.

 

Lantai tai murmushi ta ce, "Yayana ƙyaleshi ya ci arziƙin Malam wata rana za mu haɗe ai."

 

Barbushe ya dubeta dan gane tilasta wa ne yasa ta ce hakan don taga Malam ɗin koko ra'ayin kanta ne ?

Ganin tana ta fara'a yasa ya amince, ya dubeta yana murmushi yace, "Nuratu yau ne fa za ki fara karatun nan ko ?"

 

Daram ! Gaban Lantai ya faɗi, "Yau kam Yaya Isah ya kwabsamin na rantse da Allah, gaban Malam Muntasir zai ambaci littafi?" Tunanin Lantai kenan a zuciyarta amma da yake ba a binta bashin magana sai ta ce,  "Tabbas yau ne amma sai dare ai, daya ke kuma ga Malam ya dawo sai ya dinga karanta mana ai mu duka muna koya."

 

"Nuratu me ake koyarwa ne ?" Cewar Malam Muntasir.

 

"Oh Malam Muntasir ka cika son jin ƙwab Wallahi." Ta ce a cikin ranta.

 

Amma da yake tasan ko gabas da yamma za su haɗe ba zata bari yasan gaskiyar wane littafi bane sai ta ce "Bari na ɗauko maka littafin ka gani Malam."

 

Littafinta na BARI WA BIBA ta dauko ta kai masa.

 

"Kallon littafin yake yana jinjina fitinar Nuratu.

 

Ganin mutane duk sun zauna jininsu akan akaifa yasa yace, "Ya kamata Nuratu kowa ya tafi gun al'amuran shi kinga rana tayi sosai duk kin tara mana mutanen ƙauyen saboda gatan da abokina ke baki ko ?"

Sunkuyar da kanta tayi tana kowa ya tafiyarsa ta daina.

 

Har rige-rigen fita suke suna zunduma Malam Muntasir albarka.

 

Lantai ta kalli Musa ta buga masa harara, sai ya sadda kansa ƙasa yasan haushi ta ji daya kira mata Malam Muntasir.

 

 

Kowa na ficewa Inna Kande ta ɗauko sauran naman da suke ta ci wanda Lantai tai ma mai gari fashin dabbobi hada su Barbushe labari ya katse tsakaninsa da Malam Muntasir ana ne ya dubi Inna Kande yace, "Kwanakin baya Nuratu ta ce min kin je Kano ko ? Kuna da dangi ne a can ?"

 

"A"a ko ɗaya yaron ƙanin Musa ne aka kai can asibitin ƙashi ba lafiya shi ne muka je ganinsa can."

 

"Allah Sarki, ai kuwa nima a Kano nake Inna."

"Kano kake daman Malam ? Don Allah idan zaka koma ka tafi dani a kwai abin da can kawai ake saidawa zan siyo don Allah."

 

"Ke kam ƙanwata me za ki siyo har Maraya haka ?" Cewar Barbushe.

 

Shiru tayi kada fa ta jama kanta. Domin dai littafan Jarumi Nasimat zata je nema a Kano ta gani yayi kwatancen shagon da ake saida littafan a cikin littafinsa.

 

 

To wace amsa zata ba su kenan?

 

 

Haupha