MAMAYA: Labarin Soyayyar Mutum Da Aljani, Fita Ta 46 Zuwa 47

MAMAYA: Labarin Soyayyar Mutum Da Aljani, Fita Ta 46 Zuwa 47

Page 46---47

 

 

 

Luf tayi tana jin wani yanayi mai kama da sarewa ko sallamawa, sai dai taci burin duk daren daɗewa sai ta ɗauki fansar wahal da ita da mahaifiyarta da yayi.

 

Abduljalal bin Uwais ya ɗago kanta yana ƙare mata kallo.

 

Wani masifar sonta na yawo a cikin gaɓɓan jikinsa, cike da shauƙi ya ɗago fuskarta .

 

"Bilkisu kin MAMAYE NI da kika saka na afka sonki bayan ni da zummar ɗaukar fansa na zo gareki, amma kika ringayeni da kyawawan halayenki kika sa na wayi gari cikin ƙaunarki."

 

Ita dai batace ƙala ba, jin yanda tsanarsa ke yawo cikin jikinta baki ɗaya.

 

Sai da ta samu da ƙyal ta haɗiye baƙin cikin dake cike da bakinta tace.

 

"Yah Malam mi ne ne ya saka Inna cikin lamarin ɗaukar fansarka ?

 

Shin itama ta jefeka ne ?"

 

Murmushi yayi mai sauti ya shafi fuskarta yace,

 

"Ita kam laifinta guda ne, bata da ilimi tana fama da jahilci mai girman gaske, dan haka suke wasa da ita saboda tana sasu nishaɗi ko da yaushe.

 

Amma a yau zan sa a maida ta gida cikin ikon Allah, sannan nasata makaranta tayi ilimi yanda ya kamata a yanzu Huraira tasan daɗin addini yanda ya kamata, bata da matsala yanzu akan addini Huraira.

 

Ya ja hannunta sai gasu sun bayyana cikin wani ɗaki mai kyan gaske, Inna Huraira zaune tana duba Kur'ani sai da Bilkisu tayi mamaki jin yanda da gaske Inna ce ke karatu cikin natsuwa da ƙwarewa.

 

 

Ta jima tana kallon Innar ba tare da ita Innar tasu ta ganta ba.

 

 

Komawa su kai wata kyakkyawar fada duk kuyangi da bayi sunata hidima.

 

Kan kujerar data sha kayan ado ya kaita ya zaunar da ita .

 

Cike da girmamawa fadawan suka dinga kawo gaisuwa gareta ana mata kirari .

Duk abin nan zuciyar Bilkisu kamar zata fashe dan baƙin ciki da takaici, wai ita ce ta auri aljani? Allah ya saka mata ya fidda mata haƙƙinta jikinsa.

 

 

 

 

 

 

Yana zaune gaban kayan tsafinsa, ya kwarara ihu, ya fara zunduma ashar kala daban-daban, baki ɗaya ya fice daga hayyacinsa saboda tsabar ɓacin rai.

 

 Sarki kuma boka Zayyanul murrash bin zainul kenan, lokacin daya ga abin da ya faru ga tilon ɗiyarsa Aljana Raƙiyyatul Zayyanul murrash a cikin dajin Abduljalal bin Uwais.

 

Haƙiƙa da yasan da tafiyar Raƙiyyatul da bai barta ta kusa kai cikin dajin ba, domin duk wanda ya shiga dajin indai ba musulmi bane sandarewa yake a tsakiyar dajin.

 

Bai san da tafiyarba haƙiƙa da bai barta ta shiga cikin dajin ba sam, amma ko yanzu yayi alƙawarin samo hanyar da zai bi dan tsiratar da ɗiyarshi ko da hakan na nufin zai sake haifar da wani sabon yaƙi ne a tsakaninsu.

 

Madubin sihirinsa ya zubama ido yana wasu yarika marassa daɗin sauraro da furtawa, wata uwar walƙiya ta bayyana jikin madubin, sai ga wata kyakkyawar Aljana na tafiya a fusace, cikin ɓacin rai da fusata, daga yanayin rafiyarta kawai zaka iya gane yanda take a hassale.

 

 

Ko da ganinta sai Aljani Zayyanul murrash bin zainul ya gaggaɓe da wata shu'umar dariya, baki ɗaya dajin amsa amom muryar dariyarsa ke tashi.

 

Sai da yayi mai isarsa ya haɗe rai ya turɓune fuska ya miƙe tsaye a fusace yace,

Ko ban aikata komi ba na tabbata masoyiyarka zata aikata irin abin da zan aika domin nasan ita ce zata kashe Bilkisu kowa ya huta ya zauna lafiya, na rantse da wanda raina take hannunsa ni zan taimaka mata ta kashe Bilkisu domin ɗaukar fansar abin da kai ma ɗiyata Raƙiyyatul Zayyanul murrash.

 

Haka yayi ta cin alwashi yana rantsuwa da abin bautarsa akan Abduljalal bin Uwais  na tsawon lokaci kafin ya shige ɗakinsa na aiwatar da tsafe-tsafensa .

 

 

Cike da ɓacin rai Aljana Suwaibatul Zabbar ta isa bakin dajin tana matuƙar jin ciwo mai raɗaɗi a cikin zuciyarta.

 

Babu shakka a yau take san ta nuna ma masoyinta Abduljalal bin Uwais kuskuren faɗawa soyayya da wata jaririyar bil'adama, bayan yasan akwai alƙawarin aure a tsakaninsu, shin bai san yanda take kishinsaba, bata kishin ko da kanta ba?

 

Haƙiƙa tun kafin ta isa garesa take jin turirin ƙunar abin da ya aikata gareta, wai soyayya da bil'adama ! Lallai wannan abin jimami da takaici ne a gareta da sauran rayuwarta baki ɗaya.

 

Amma kuma laifin na munafukan kuyanginsa ne ai, domin sun san da cewa ita ce kawai masoyiya a garesa, mi ya hana su je su gaya mata da lamarin ya bayyana ?

 

Tabbas akansu zata fara ɗaukar fansa kafin ta isa ga Bilkisun, ta rantse da Allah ko shi Yah Malam ɗin ya nemi dakatar da ita daga sabauta rayuwar Bilkisu sai sun kafsa ƙazamin yaƙi na ban mamaki da shi, domin yasan cewar shi ɗin yana da matuƙar kafiya akan abin da yake so, to wai ma yana nufin ya manta da babinta kenan da ya afka soyayya da wata bil'adama ?

 

Wani uban ihu tayi wanda baki ɗaya dajin ya amsa kuwwa, tsuntsayen dake cikinsa suka ruɗe suka dinga faɗowa ƙasa suna tashi a firgice.

 

 

Kasancewar ya samu abin da yake so dan haka ya bada umurnin a ɗauki Inna Huraira a maidata gidanta, ya tura wata Aljana da nufin ta fatattaki aljanun da Raƙiyyatul Zayyanul murrash ta aje a cikin gidan.

Ya basu umarnin su fita daga cikin rayuwar Inna Huraira baki ɗaya domin yanzu matsayin suruka take a garesa .

 

 

 

 

 

   Nasir ......

 

 

 

Tunda ya razana yayi ƙara shike nan bai sake sanin inda kansa yake ba, sai farkawa yayi ya gansa a cikin wani ɗaki mai kama da bukka a tsakar dokar daji shi kaɗai.

 

Kasancewar kansa yayi masa nauyi sosai yasa baki ɗaya ya kasa miƙewa zaune daga kwancen da yake.

 

 

Wata mahaukaciyar dariya ta gauraye dajin baki ɗaya, kafin daga bisani ya ji tsit.

 

"Nasir haƙiƙa kayi wauta da kake son abin da nake so, dole ne hukuncinka yayi tsanani domin nayi maka kashedi ta hanyoyi masu dama amma kayi biris da lamarina kasancewarka mutum mai taurin kai, to yau haka inda taurin kanka ba zai amfana maka komi ba.

 

"Ka sani a yau zan haɗa hatsarin ƙarya na nuna ma duniya ka mutu, kai kuma zaka cigaba da rayuwa a cikin wannan tsaunin har ƙarshen rayuwarka.

 

"Sannan ina san ka sani a yanzu haka na auri Bilkisu na ɗauke ta na kaita wani bigiren da babu wanda ya isa ya shiga cikinsa balle ya ƙwato ta, daga ƙarshe zan baka labarin Aljana Raƙiyyatul Zayyanul murrash dake bibiyar rayuwarka tana taimaka maka, dan kawai tana sonka itama tana a hannuna cikin mummunan yanayi na azabar rayuwa mai raɗaɗi."

 

 

Sautin dariyarsa ta karaɗe dajin baki ɗaya na tsawon lokaci kafin daga bisani ta ɗauke.

 

 

Kamar a mafarki haka yake tsammanin lamarin dan haka ya sake runtse idanunsa da tunanin idan ya sake buɗewa zai farka daga mummunan mafarkin da ke addabarsa a kwanakin nan.

Sai dai abin da gaske ne ba a mafarki ba, dan haka ya samu kansa a cikin yanayi mai ban tausayi, baki ɗaya ya dinga tunano abubuwa da dama da suke faruwa da shi, sai a lokacin ya aminta da cewar anyi abubuwa da dama da ya kamata ace ya gane inda lamarin ya dosa tuni amma ya kasa gane hakan.

 

To kenan Ibnah taci wahala ta ga abubuwa da dama kenan na tsoratarwa ?

 

Yanzu shike nan ya ɗauke Ibnah kamar yadda ya ɗauke sa ?

 

Ashe daman ciwon Inna Huraira duk ƙarya ne, ba ita ce ba ma aljana ce ?

 

Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un !

 

Haƙiƙa akwai abin da ke faruwa wanda ba wanda yasan da faruwarsa kuwa.

 

Yanzu haka zan zauna a nan kenan ba tare  da mutane ba ?

 

Haƙiƙa dole na tashi na fice daga dajin nan domin zuwa ƙwato Bilkisu a duk inda ya Boyeta."

 

 

Yana gama yanke hukuncin ya fice daga cikin ɗakin bukkar yana jin ƙarfin gwiwar tunkaran duk abin da zai tsaida sa a hanya .

 

 

Sai dai dole yayi tsaye domin baki ɗaya dajin ba wani alamar a kwai hanyar da mutum zai bi ya fice lafiya .

 

 

Naman dawa ne ke ta yawo, wasu na ta wasa ba abin da ya damesu da ko kallon inda yake .

 

Ganin haka ya fara ratsawa ta cikinsu da nufin ficewa daga cikin dajin duk da bai san hanyar da zai bi ta fidda shi daga cikin dajin ba.

 

 

 

 

 

 

      Gidansu Bilkisu....

 

 

 

Malam Ahmad tunda akai saukar Bilkisu sai ya samu kansa da farin ciki wanda hakan yasa ya daina koya mata karatun Alƙur'ani da su ke yi tare da ƙannanta, haka ya manta da sabgar Inna Huraira shi a nashi ganin ba sauran abin da za ai mata ta warke sai addu'a da jiran lokacin warkewarta.

 

Saboda haka baki ɗaya ya raja'a gun kasuwancinsa, wanda kuma ba laifi abubuwa nayi masa kyau a kwanakin nan, domin kyautar da Bilkisu ta samu ta kuɗi masu kauri shi ta ba su, tace ya ƙara jarinsa, hakan yasa yanzu ba ɗai-ɗai yake saidawa ba gwanjunan dila-dila yake saidawa, dan haka yake matuƙar samun alheri daga kasuwancin nasa yanda ya kamata.

 

Lokacin da aljanun suka maido Inna Huraira gidan ba kowa yara sun tafi makaranta, Babansu yana kasuwa dan haka su ka kacame da azabebben faɗa a junansu, ita dai Huraira bata san duniyar da take ba.

Cikin layin aka dinga jin wani irin kuka, da gunji amma an rasa daga ina yake fitowa, ga shi kukan bai kama da na mutane ba, a taƙaice ma dai kukan ba a san da ko kukan mi yayi kama ba, zuwa can kuma a ka dinga jin wani irin gurnani da gunji marar daɗin ji, hankalin mutanen unguwar ya tashi amma ba wanda yasan daga ina kukan da gunjin ke fitowa, dan haka kowa yayi ta kansa ya shige gidansa ya rufe yayi tsit.

 

A cikin gidan kuwa aljanun Abduljalal bin Uwais sun samu nasarar fatattakar Aljanun Raƙiyyatul Zayyanul murrash ba, sun masu raunuka sosai duk da dai kusan Kare jini akai Biri jini a artabun nasu.

 

Dole aljanun Raƙiyyatul Zayyanul murrash suka fice daga gidan ba dan sun so ba sai dan anfi karfinsu .

 

 

Kusan awa guda sannan aljanun suka aje Huraira su ka juya su ka ɓace bat ba tare da sun bar alamar da zata sa a gane ansha artabu a cikin gidan ba.

 

 

Bayan awa ɗaya da ɓacewarsu sai hannun Huraira ya fara motsawa, a hankali bakinta ya fara motsawa, cikin natsuwa take furta,

 

"La'ila ila ha illallah Muhammadan Rasulullah sallahu alaihi wa sallam.

 

 

Cikin natsuwa ta buɗe idanuwanta, kanta taji yana ɗan sara mata kaɗan-kaɗan dan haka ta dafe kan tana karanto Fatiha tana tofawa.

 

Ta jima kafin ta sauka daga kan gadon ta fice daga ɗakin zuwa tsakar gida, sosai take jin jikinta ba daɗi duk yayi wata kala dan haka ta samu ta watsa ruwa ta dubi lokaci taga anyi sallar la'asar dan haka tayi alwalla ta kabbara sallah.

 

 

Tana cikin sallar Malam Ahmad ya dawo, saura kaɗan ya faɗi dan mamaki.

 

 

Samun waje yayi ya zauna yana jiran ta gama sallah ya tabbatar da ita ce ɗin kuwa ?

 

Bayan ta gama sallah ta dinga jero addu'a cikin natsuwa da kwanciyar hankali.

 

 

Kawai Malam Ahmad fashewa da kuka yayi yana godema Allah, yau Huraira ce ke sallah harma tana addu'a ?

 

Lallai Allah na sansu da rahama sosai da hanzari ya sake ficewa dan siyen abin sadaka, sai dai ba kowa a cikin layin nasu, shi bai ma kula ba da gidajen a rufe su ke ba sai yanzu .

 

Dan haka shima baki alaikum ya koma gidansa ya maido ya rufe yabi layin sauran, yana tunanin ko lafiya kuma yau layin nasu kowa ya shige gida ya rufe ?

 

Bai da amsar dan haka ya rufe nasa gidan ya yi alwalla shima ya fara nafila ta godiya ga Allah da ya ba Huraira lafiya, ciwon ya zama hanyar shiriyarta kuma.

 

 

Huraira na gama sallah ta nufi ɗakin Malam ɗin dan taji motsin rufe gidan da yayi da shigowarsa ma .

 

Sallah ta iske yana yi dan haka ta samu gefe guda ta zauna tana jiran ya gama sallah taji abin da yasa ya rufe gidan yau kuma.

 

 

Shi kam malam ai sallame sallar yayi bayan yayi raka'a biyu ya juyo ya kalleta fuska ɗauke da farin ciki.

 

"Huraira jiki yayi sauƙi kenan ?

 

Cike da ladabi a muryarta ta ba shi amsa da cewar,

 

"Jiki ya yi sauƙi malam sai fatan Allah ya bamu ladar jinya."

 

Ai sai Malam ya ji kamar ya ɗauke ta yayi ta rawa dan murna.

 

Kasa daurewa yayi ya dubeta yace, "Huraira naji daɗi da kika dawo hayyacinki sannan ga alama kin watsar da duk wani jahilci kin koma ga Allah."

 

Murmushi tayi tace,

 

"Ai dole malam domin ni kaɗai nasan irin azabtar dani da akai akan jahilcina sai dai ince Allah ya yafe mun ya kyauta gaba kuma."

 

 

Nan dai su kai ta labari har lokacin da yaran suka dawo daga makaranta amma ba Bilkisu ba alamarta har zuwa magrib bata dawo ba, hakan yasa Malam yabi islamiyar dan ya dubo ko lafiya, amma bai iske kowa ba dan an tashi tun kafin shida.

 

Haka ya juyo ya dawo ya iske layin nasu mutane nata wani labari wanda bai ma san kansa ba, kuma yana cikin tunanin ina Bilkisu take yanzu yasa ya raɓa su ya wuce nasa gidan.

 

 

Huraira tayi zugudum tana tunani wanda ita ba zata ce ga abin da take tunaninba sam.

 

Malam ya dawo ya gaya mata ba kowa makarantarsu Bilkisu yaje .

 

Tashin hankali kam sun ganshi domin ko shakka babu Inna Huraira ta shiga damuwa ƙwarai da ɓatan Bilkisun.

 

 

 

A gidansu Nasir ma haka aka wayi gari babu shi ba alamarsa, kuma abin mamaki shi ne anga wayarsa komi nasa an ganshi amma shi ba a ganshi ba.

 

Malam Ahmad ganin zaman ba zai masu ba yasa yace ma Huraira taje gidajen ƙawayenta ko tana can Bilkisun.

 

Haka kuwa aka yi Huraira ta nufi gidansu Shema'u Yahaiya dan tasan ita ce ƙawar Bilkisu ta kusa .

 

Sai dai abin mamaki Shema'u ta ruɗe sosai da ganin Huraira na neman Bilkisu ta shaida mata yau Bilkisu bata je makaranta ba ma sam ai.

 

 

Dan haka tare da Shema'u su ka sake fita sun zo dai-dai gidansu Nasir Shema'u tace ma Inna Huraira "bari naje nan na gani ko tana nan Inna."

 

Sai dai abin da ta iske ya bata mamaki ya razanata kuma jin ɓacewar Nasir shima, hakan yasa wani sabon tunani ya ɗarsu a zukatan mutanen gidan .

 

 

Cikin sanyin jiki Shema'u ta fito ta gayama Inna abin da ke faruwa.

 

 

Kasancewar daman tun farko Inna ba san Nasir take ba Sai ta faɗi a gun ta saka kuka tana cewa ya sace mata yarinya ya gudu da ita .

 

Hankalin mutane ya fara yowa kanta dan haka Shema'u ta samu ta jata suka nufi gida.

 

 

Nan da nan labari ya watsu cewar Nasir da Bilkisu sun gudu ba da sanin iyayensu ba.

 

Nan dai wasu suka dinga cewa ƙilama ciki yayi mata suka gudu kar asirinsu ya tonu, kowa dai da labarin dayake bayarwa akan lamarin na ɓatan Nasir da Bilkisu.

 

 

 

 

Zuwa yanzu Bilkisu ta gama shirya duk wani tsari nata da zata bi ta kansa ta rama abin da Abduljalal bin Uwais yayi mata ita da mahaifiyarta.

 

 

Sai dai bayyanar Aljana Suwaibatul Zabbar ya rikita komi, domin ta kula Aljanar bata da imani bata da mutunci, sau tari ta sha zuwa da nufin kashe ta Abduljalal bin Uwais ke ƙwatarta sannan ta kula Aljanar jaruma ce domin duk sanda suka haɗu da shi suka gwabza yaƙi sai ta yi masa raunuka sosai.

 

Tun tana addu'ar Allah yasa Aljanar ta kashe shi har yanzu ta fara tausaya masa, domin ta kula da gaske yake matuƙar ƙaunarta, haka bai san yaga ta shiga damuwa ko da ta lokaci ƙalilan ne.

 

 

Sannan tana jinjina ma yanda ta dinga hantararsa tana disga shi a gaban fadawansa tana masa abubuwa masu ciwo amma yana ɗauke kai, ko da yaushe magana ɗaya yake furta mata ita ce,

 

"Bilkisu ina ƙaunarki ba zan iya rabuwa da ke ba ko da zan rasa rayuwata ne."

 

 

Idan kuwa har zai iya rasa rayuwarsa akanta, ita mi zai hana ta mara masa baya ta rasa tata rayuwar akansa ?

 

Zuwa yanzu ta jima tana jin mugun tausayinsa, da tunanin kyawawan halaye irin nasa, gaskiya tayi matuƙar dace da samun miji masoyi kamar Abduljalal bin Uwais ɗin.

 

Kamar yau tana zaune cikin wani keɓeɓɓen waje mai matuƙar kyau da abubuwan more rayuwa, tana zaune ta tsoma kafafunta cikin wani ruwa dake gun tana tunanin kyakkyawar fuskar Abduljalal bin Uwais ɗin, baki ɗaya hankalinta ya yi nisa gun tuna kyawunsa da irin mayyar soyayyar da yake nuna mata, ta rufe idonta tana ta doka murmushi taji kamar ana shafa mata jikinta a hankali, ko ba ta faɗa ba tasan rabin ranta ne Abduljalal ɗin dan haka ta sake lumshe ido tana mai ƙara jin ƙaunarsa na yawo a cikin jikinta.

 

Ruwan ya sauya kala daga fari zuwa jajir kamar jini, sai murtukewa yake irin na jini mai kauri .

 

A hankali ya fara ɗumi yana zafi gwanin daɗi a kafafunta, cikin dariya take cewa,

 

"Barka da fitowa masoyina abin son zuciya da gangar jikina, haƙiƙa zaman nan da nake kai ne kawai nake tunani nake ƙara jin ƙaunarka na yawo a cikin sassan jikina baki ɗaya.

 

 

Bata ji ya tanka ba, dan haka ta sake kashe murya tace,

 

"Kada dai a ce masoyina ya ji ba daɗi dan kawai na fito waje ina ƙara tunzura ƙaunarmu mataki na gaba ba ?

To kaina bisa kafafuna ina mai neman sassauci daga farar zuciyar masoyina ga jaririyar zuciyata dake cike da ƙaunarka."

 

 

Wani matsiyacin zafi taji ya ziyarci kafafunta wanda hakan yasa ta buɗe idanunta ba shiri tana zare idanuwa.

 

 

Da karfi ta kwala ihu ganin ruwan sun koma jini sai turirin zafi suke, da sauri ta janye kafafunta da nufin rugawa, sai dai tana juyawa taci karo da wani ƙaton maciji fari fat ba ɗigon baƙi ko wani kala a jikinsa, hatta idanunsa fari ne ya fasa kansa ya buɗe bakinsa yana niyyar haɗiye ta baki ɗaya.

 

 

Idonta ta rufe tana mai ƙwalama Abduljalal kira da karfin gaske.

 

 

Kawai ganinsa tayi gabanta ya bayyana fuskarsa ɗauke da azabar ɓacin rai, ya dubi ƙaton macijin yace a cikin tsawa.

 

"Suwaibatul Zabbar shin ban maki iyaka da Bilkisu ba ?

Shin ban bayyana maki cewar ita ce mafi girman daraja a cikin idanuwana ba ?

 

Shin ban sanar da ke cewar ita ce matata wadda baki ɗaya na aminta da ita fiye da kowace mace a faɗin Duniyar nan ba ?

 

Shin ban gaya maki cewarba akanta zan iya rasa rayuwata ba ?

 

Haƙiƙa yau shi ne kashedina na ƙarshe da zan maki akan shiga sabgar Bilkisuna ."

 

 

Wata mahaukaciyar dariya ta saki mai amo da amsa kuwwa, kafin kuma ta haɗe rai ta dubeshi tace,

 

"Na rantse da Allah ko da sama da ƙasa za su haɗe a yau sai na halaka yarinyar nan kaima na halaka na halaka kaina kowa ya rasa Jalal.

 

Ba zan taɓa aminta da rayuwa babu kai acikin ta ba Jalal.

 

Ko da kowa ya haƙura da kai ni ba zan taɓa haƙura da kai ba Jalal.

 

 

Kasan cewar nafi kowa fushi da mugunta da ƙeta a kaf cikin jinsin mu dan haka ka sani a yau ji nake ba zan iya ɗaga maka ko da ƙwayar zarra ba daga cikin fushina ba Jalal.

 

Akan bil'adama zaka wulaƙanta ni Jalal ?

 

Akan bil'adama zaka juya min baya Jalal ?

 

Na rantse da wanda raina ke hannunsa ayau zan shafe babin rayukanmu baki ɗaya sai dai a sake samun wasu a wata rayuwar Jalal .

 

Zuwa yanzu ta koma wata irin halitta marar kyan gani ta tunkaro su ba tare da sassauci ba akan fuskarta ba sam.

 

 

Bilkisu ta rungume Abduljalal tana mai addu'ar Allah ya bashi sa'ar cin galaba akan wannan matsiyaciyar Aljana mai neman ganin bayan soyayyarsu .

 

 

Ko ya zata kaya kenan ?

 

 

Ina labarin Aljana Raƙiyyatul Zayyanul murrash ne ?

 

Yaya labarin Nasir a cikin dajin can ?

 

 

Yaya Malam Ahmad zai ji idan ya ji cewar Nasir ne ya gudu da Bilkisu ?

 

Duk amsar na ga Haupha dan haka kuci gaba da bibiyar alƙalamin ta.

 

Haupha