HAƊIN ALLAH
Labari da rubutawa
*Hauwa'u Salisu (Haupha)*
Page 8
Barka da sallah ɗauka cin jama'ar musulmi baki ɗaya. Allah Ya amsa ibadarmu Ya azurta mu da dacewa tun a duniya har zuwa lahira ya ƙara mana soyayyar juna ga masoyanmu Yasa mu gama da iyayenmu lafiya. Amin.
Jikin kowa ya yi sanyi, da gudu aka kinkimi Bello zuwa shagon wani ƙaramin Likita ya duba shi. Mutane nata faɗin albarkar bakinsu, wasu na cewa Iyami ta kyauta daman sace yaran tai amma tace sun ɓace? Kai lallai Iyami ta cika ƴar rigima satar yara mata har biyu musulmai kina Kirista? Bello ya jima bai dawo hayyacinsa ba, sai kuka yake rigis yana cewa ba zai taɓa yafewa danginsa ba, su ne silar rasa farin cikinsa matarsa Fatima da ɗiyarsa Alawiyya. Ba yadda Yayansa bai ba gun ba shi haƙuri ba amma ina dare nayi ya rubuta takarda ya aje ma Yayan nashi ya gudu shima.
Asubar fari Yayan Bello ya farka yin Sallah yaga bai ga Bello ba, da farko bai damu ba sai da ya je masallacin ya dawo yaga bai ganshi a can ba kuma bai gidan da suka kwana, idanunsa suka sauka kan takardar sai da gabansa ya faɗi zuciyarsa ta raya ma shi mugun abu game da Bello.
Hannunsa na karkarwa ya buɗe takardar cike da tashin hankali ya fara karanta ta a bayyane kamar haka...
"A gaskiya Yaya kun riga kun cuci rayuwata kun gama takaita min rayuwa, don haka na yanke shawarar zan bi duniya neman yarinyata, ba zan dawo gare ku ba har sai naga Alawiyya, tabbas idan zan mutu ban ganta ba, to ku ma zaku mutu baku ganni ba. Ina so idan ka koma gida ka gayama iyaye da sauran dangi na tafi neman ɗiyata uwa duniya da sukai min silar rasa ta, sannan nayi alƙawarin ba zan sake aure ba har sai naga Alawiyya ko mahaifiyarta Fatima, don Allah ina neman gafara gare su, su yafe min duk abin da nayi masu, sai watarana.
Daga ɗan'uwanka Bello Baban Alawiyya."
Tausayin ƙaninsa ya turniƙe shi, hawaye masu zafin gaske suka zubo mai, tabbas ba su yi ma Bello adalci ba, haka basu tuna darajar aure da haihuwa ba, suka tsige shi daga cikin zuri'arsa saboda kawai taƙamar bai auri wadda suka sani ba, sun manta da cewar duk gidansu shi ne ƙaramin cikinsu amma ya fisu natsuwa da hankali, haka Allah Ya yi shi mai son neman na kansa, bai laru da kowa ba, abin kowa bai dame shi ba, ko da ake cewa duk wanda ya je Lagos neman kuɗi shaye-shaye kawai yake koyowa to ban da Bello, domin shi a nutse yake, sai ma tarin arziƙi daya tara masu yawan gaske duk da cewar Fatima ya barwa kuɗaɗensa a lokacin amma ya dawo da tarin baiwar iya gyaran mota,da mashin, wanda ya buɗe gareji kamar wasa sai ga shi manyan masu kuɗi na kawo mai gyara suna kiransa kuma, cikin lokaci kaɗan ya tara yaran da yake koya ma aikin, kowa yasan garejin Baban Alawiyya a Kano da kawayenta, sunansa ya tumbatsa saboda iya gyaran sa. Jiki a sanyaye Yayan Bello ya kimtsa ya juya Kano yana cike da tausan Bello, tabbas sun yi abin da bai dace ba gare shi, ko da yake su kansu za su gane kurensu tunda Bello na matuƙar taimakon su duk da cewar suna da rufin asiri amma bai damu ba, komi ya samu kan yaransu yake ƙarewa, yanzu sun ja ya bi uwa duniya, kuma ba shakka su ne sanadin faruwar komai. Har ya sauka Kano yana jinjina abin a ransa, lokacin da iyayensu suka ji labarin komai sun yi kuka sun yi nadamar abin da su kai, ƙarshe suka fawwala Allah lamurran suna masu addu'ar Allah Ya bayyana masu Bello da zuri'arsa.
Garejin Baban Alawiyya kuwa ba a rufe shi ba, babban yaronsa ya ci-gaba da kula da garejin yadda ya kamata ribar da aka samu yana turawa Bello a account ɗin shi suna raba sauran su kuma.
Baban Jiddah tun daga lokacin sai da ya shafe kwanaki goma yana jin ɗacin ɓatar ƴarsa, da takaicin cin amanar da Iyami tai ma shi, lokacin da kwanakin suka cika goma a lokacin ya manta da wata yarinya Jiddah, duk da cewar mutane na damunsa da zancen ya kamata ya dawo da yarinyarsa gida yanzu domin ta girma duk inda take,ko kallo ba wanda ya ishe shi idan ana maganar, domin yasan ba inda zai ga Jiddah saboda duk wanda ya kamata ya tambaya garinsu Iyami ya tambaya amma ba sahihiya ba, kowa cewa yake bai san garinsu ba, hakan yasa ya manta da shafin wata Jiddah ya ci-gaba da kula da yaron da matarsa ta haifa kawai.
Tunda mahaifiyar Jiddah ta samu labarin ankai mata yarinya Lagos gun Kirista take kukan ɓoye bata da yadda zatai saboda tana da kunya kuma ita ce ɗiyarta ta farko ba yadda za ai ta nuna damuwa a fili aga rashin kunyar ta , sai dai ta shige ɗaki taita kuka tana addu'ar Allah Ya kare mata yarinya a duk inda take ya tsare ta daga dukkan sharri da abin sharri, Ya kare ta daga maƙiya a duk inda take. Tana cikin tsananin tunanin inda yarinyarta take aka ce ta bada ƙanin Jiddah Abdul da take goyo, abin da ya ƙara karya mata zuciya kenan ta shiga rama ta lalace hakan yasa Babanta ba da aurenta ga wani likita dake zuwa duba su idan basu lafiya mai suna Salman ba tare da ya yi shawara da ita ba, kawai ji tai an ɗaura mata aure da wani ko saninsa ba tai ba amma saboda haƙuri da biyayyar iyaye ta amince ko ja batai ba aka kaita gidan Salman don ma ita kaɗai ce a gidan bai da mata kuma yana matuƙar ƙaunarta komi yana taka tsantsan-tsantsan don gudun ɓacin ranta.
Duk da haka tunanin yaranta na cikin ranta ko da yaushe cikin kukan ɓoye take, har dai Salman ya ankara ya je da kansa ya nemi alfarmar a bata yaronta ta ci-gaba da kula da shi gunta saboda tana cikin damuwa sosai don kawai tana kawaici yasa ba a gane damuwarta da farko hanata yaronta ya yi Uban dawa sai daga baya ya bata shi, hakan ya rage mata ciwo da raɗiɗin zuciyarta saboda jin daɗin halarcin Salman gareta ta yakice damuwarta a bayyane ta adana ta a zuciyarta tai ta rayuwa cikin aminci da samun kulawa daga mijinta amma son Jiddah na maƙale a ranta.
KANO
Cikin tsoro-tsoro suka bi mutumin wanda ya nufi wani tsohon lungu yana waige-waige yana cewa su ƙara sauri kar a gansu. Kawai sai su kai ma juna inkiyar su ruga domin basu yarda da cewar taimakon Allah da Annabi zai masu ba don haka suka watsa da gudu suka bar shi tsaye yana kallonsu yana ci je yatsa. Suna cikin gudun wani Kare ya biyosu abin da ya razana su kenan kowace ta kama hanyarta daban kamar wasa suka ɓace ma juna, kowacce ta ganta a cikin waje daban.
Alawiyya garejin gyaran motoci ta gani gabanta don haka ta kutsa ta inda ƙauren rufin ya ɓalle ta shige hankalinta a tashe tana zare idanuwa hawaye ya wanke mata fuska. Tsabar gajiyar gudun da tai har gari ya waye tangaram bata sani ba barci kawai take ba ji ba gani. Aliyu ne ya buɗe garejin da zummar fitar da kayan aiki su fara ya ci karo da yarinya kwance tana barci ƙafafuwanta duk sun kumbura ga jirwayen hawaye kan kumatunta.
Ya jima yana kallonta ya rasa gane inda yasan fuskar yarinyar, yana tsaye ya kasa gane inda yasan fuskar sauran yaran garejin suka shigo suma suka ci-gaba da kallon yarinyar suna mamakin ganinta a nan tana barci.
Aliyu ya tada ta, firgigit ta farka tana kiran "Jiddah.! Amma ganin ba Jiddah sai maza sai ta fashe da kuka tana neman hanyar guduwa. Haka kawai Aliyu ya ji tausayin yarinyar a ransa don haka ya ji yana son sanin abin da ke damunta, hakan yasa ya sausauta murya ya dubeta yace, "Haba ƴan mata kukan ya isa haka, me kike nema ne? Ina Jiddar take ne? Ya akai kika kwana nan shagon ko baƙuwa ce ke ɓata ki kai?" Jin kalamansa yasa Alawiyya dakatawa da kukanta tace, "Daga wani gari muka zo ni da ƴar'uwata Jiddah mun gudu daga gidan marayu ne muna neman iyayenmu sai wani ya biyo mu jiya da dare muka rugo shi ne Jiddah ta ɓace min." Su duka sun fahimta hakan yasa suka maida kallonsa ga Oga Aliyu tunda yanzu shi ne mai wajen suna jiran hukuncin da zai yanke.
Jiddah kuwa wani gida ta gani buɗe ta afka tana ta nishin wahala ƙafafunta sun kumbura kai tsaye ɗakin data hango buɗe ta afka ta maido ƙofar ta rufe ta fashe da kuka mai cin rai.
Hajjo na kwance tana tunanin inda Autanta ya yi dare ta ji an shigo an rufe ƙofar ga kuka ana yi sai tsoro ya kamata ta ɗaga kanta kenan aka ɗauke wuta ba tare da ta ga ko miye ba. Kawai ranta ya bata aljanu ne ke son zautar da ita, hakan yasa ta yi shiru tana zare idanuwa ta ɗauke numfashi a zatonta ba za su gane ta ba, tunda ta ɗauke numfashinta. Amma jin kukan ya yi yawa yasa sam ta kasa daurewa ta buɗe idonta tana karanta duk abin da kama a bakinta.
Shigowar Autanta yasa ta ji sanyi ko banza ya korar mata su tunda ya iya karatun Alkur'ani mai girma yadda ya kamata. Salim na shigowa ya ga ɗakin Hajjo rufe ya yi murmushi watau ta yi barci yau ta fasa cin naman tabdijam abin da mamaki Hajjo tasan da zuwan nama tai barci! Yana matsowa ya ji kuka-kuka kamar na yara kamar na manya, haka nan ya buɗe ɗakin ya haska wayar hannunsa sai kuwa yaga yarinya tsugunne ta kife kanta sai kuka take. Hajjo ta zaburo tace, "Don Uwaka daina haska mutanen ɓoye kar ka ja mana masifar cikin dare tafi guyaba da bala'i." Tsam ya yi yana kallon yarinyar ga maganar Hajjo na yi ma shi yawo cikin kunne, amma sai ya daure ya sake haska yarinyar yana hailala a cikin ran shi, ya nufi yarinyar ya kai hannu zai taɓa ta Hajjo ta rarumo filo ta jefe shi da shi, "Kai hauka kake zaka taɓa jinnu ?" Salim ya daure ya taɓa ta, jininsa kan akaifa, sai ya ji lafiya lau ba wani tashin hankali daya biyo bayan taɓa ta da yai, don haka ya matsa sosai yace, "Wacece ke? Daga ina kike ne?". Jiddah jin ana mata magana ta ɗago kanta cikin kuka tace, "Wani ne ya biyo mu." Hajjo ta zaburo ta sauko daga kan gado tace, "Au da gaske mutum ce Auta?" Dariya ya yi yace "Tabbas amma bari mu ji daga ina take? Cikin kuka Jiddah ta bayyana masu labarinta, tana rufe baki ana maido wuta, Hajjo ta ƙura mata ido, zuwa can ta rungumeta ta saki kuka tana cewa "Auta baka gane ɗiyar Yayarka bane? Allah mai amsa addu'a ai Jiddah ce ta wajen ɗiyata Umma ko? Wadda ubanta ya kai ma Kirista Lagos riƙo aka ce kuma ya koma ɗauko ta arniyar ta gudu da ita, tabbas Allah abin godiya kullum sai na ji tausan Umma saboda rasa ɗa ba ƙaramin abu bane ba."
Salim ya washe baki yace, "Allah sai yanzu naga kamar ta da Yaya Umma Hajjo." Ko da Jiddah ta ji cewar gidan ƴan'uwar Mamarta ne sai ta miƙe zumbur ta nemi rugawa, domin ta tsani duk wanda ya shafi danginta na uwa dana uba duk ta yafe su. Hajjo ta riƙe ta gam tana cewa "Ina kuma za ki muna ta barka kin bayyana Jiddah?" Ta fashe da kuka tace, "Ƴar'uwata zan dibo Alawiyya ban san inda take ba yanzu don Allah ku barni ban san ku ban san dangina na tsani Mama na tsani Baba!
Su duka su kai ajiyar zuciya tabbas akwai matsala yaro ya tashi da ƙin iyayensa, amma wasu iyayen su ke ja ai, sai dai ko da wasa Umma bata da laifi a lamarin Jiddah. Da ƙyar suka samu ta natsu kan cewa za su dibo Alawiyya kuma ba za su gayama dangi an ganta ba, balle a zo a kaita gun Babanta.
Ba inda basu haska ba a cikin daren amma basu ga Alawiyya ba, dole suka koma gida suna lallashin Jiddah sai kuka take tana ambatar Alawiyya.
Washe gari haka suka dasa neman Alawiyya bata ba labarinta, dole Jiddah ta haƙura ta zauna gidan Hajjo bayan an gaya mata yadda suke watau Hajjo matsayin Kakarta take, domin da wadda ta haifi Mamarta da Hajjo uwa ɗaya Uba ɗaya suke.
Sai da Jiddah tai shekara guda sannan Hajjo ta shirya mata kaya tace ta rakata unguwa basu zame ko'ina ba sai garinsu, cikin ikon Allah da Baban Jiddah suka fara cin karo, ko da Hajjo ta gama ba shi labarin yadda Jiddah ta zo gunta ƙaryata wa ya yi yace su suka aika aka sace mai yarinya nan take ya kira ƴan sanda suka tafi da Hajjo da Salim shi kuma ya tafi da Jiddah gidansu sai kuka take.
To masu karatu mu haɗe a shafin gaba don jin yadda zata kaya.
Daga taku Haupha