ANA BARIN HALAL.....:Fita Ta 44
ANA BARIN HALAL.....
*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE*
*®️GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
_(Gaskiya Dokin Ƙarfe
Burin Mu Faɗakar Da Al’umma Domin Ribatar Duniya Da Lahira.)_
*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*
Idan kana/kina sha’awar:
_**Updates akan tallafin gwamnati (Grant & Loan)._
_**Hanyoyin samun kuɗi ta kasuwanci na online._
_**Sana’ar hannu da za ki iya yi daga gida._
_**Dabarun amfani da waya wajen samun kuɗi._
_To wannan group ɗin na Business/Grant/Loan naku ne! Zaku samu labarai kai tsaye + shawarwari masu amfani in sha Allah._
*Join yanzu don kada ku rasa sabbin damarmaki*
https://chat.whatsapp.com/C64wC3IDhW6FtwjSpWWDiL?mode=ac_t
*Page 44*
*INA UWARGIDAYEN SUKE? NACE INA UWARGIDAYE MASU CAPACITY SUKE, IDAN BAKI YI MATSA GA MASU* *AUTHOURITY, NACE TSAYA IDAN BAKIYI GA AMARE MASU AUTHOURITY,* *IDAN KIN SHIRYAH GWANGWAJE SHINFIƊAR MAIGIDA,* *TOU KI ƘYALE ƳAN LOCALLITY KI MATSO KI SAYI NAKI,* *BEDSHEETS ƳAN GASKE, KU MATSO KU YAƘI PORVERTY DAGA TASKAR HALIMA YISUF GWARZO, INA MAI TABBATAR MIKI IDAN KIN SHIMFIƊA ZAKI ZAMA MAI CAPACITY MAI AUTHOURITY,* *DOMIN KI WANKE ZUCIYAR MAIGIDA YA HASKAKA,*
*MUNA AIKAWA DA SHI KO'INA A FAƊIN ƘASAR NAN.*
*DOMIN SAYEN ƊAYA KO SARI, KU TUNTUƁE NI TA WANNAN LAMBAR*
08064586559
**********
Wurin buɗan kan ya cika maƙil da ƴan'uwa da abokanan arziki, gefen mu M.G ne zaune da amaryar shi, sun sha ankon blue shaddah shida A.G, haka wurin ɗaurin aure sunyi ankon white shaddah, gefen shi Heedayah ce zaune fuska a rufe, nima gefen A.G aka zaunar dani,
M.G ne yafara buɗe fuskan amaryar shi, bayan ya liƙa mata kuɗi ya koma ya zauna, sannan A.G ya tashi ya biɗe nawa fuskan, ina jin shi yana liƙa mun kuɗi yana ɗan taka ƙafana a hankali, haka na share shi dai ban motsa ba.
ƴan uwana da nashi suna ta aikin liƙa mana kuɗi, gefe ɗaya ma ƴan'uwan M.G suna ta liƙa musu, Yayah Ahmad ne ya shigo shida wani aboki, M.G suka fara liƙawa, sannan suka dawo kanmu, liƙa ma A.G yayi, amma daya dawo kaina key ɗin mota ya ɗaura mun a tafin hannu na, aiko gaba ɗaya fili ya ɗauki tafi, har sai da A.G ya miƙe tsaye ya rungume yayah Ahmad, M.G ma tashi yayi ya rumgumeshi fuskan su duka cike da farin ciki, hannu A.G ya miƙo kan cinya na ya ɗage key ɗin, aljihun shi ya saka, gaskiya buɗan kan ya ƙawatar, ko dan motan da nasamu abun ya mun daɗi sosai.
Daga nan motoci ne suka ɗauke mu zuwa kallon hawa da zasuyi, shima hawan babu laifi yayi kyau sosai, ni dai dayake bai dame ni ba ko kaɗan, so ba wani burgeni sosai abun yayi ba, A.G nah yayi kyau da shigan da yayi, a ido na ma kaman yafi kowani namiji a wirin kyau.
Zuwa ƙarfe 10:00pm na dare dukkan jama'a sun watse, kowa ya kama gaban shi an gajji da ganin gidan amaren, haka ƙawaye da dangi duk sun tafi gida, daga ni sai hadiza da zainab, sai hafsy da Aunty j da suke jiran yayah Ahmad yazo ya ɗauke su, sun ƙara gyara gidan sun saka turaren wuta, ko ina ƙamshi mai daɗine yake fita, nima daidai lokacin na fito a wanka, Aunty j tana tayani kintsawa sai ga yayah ya ƙirata akan su fito yana waje, batayi saurin fita ba sai dana shiryah acikin wata doguwar rigar atamfah mai kyaun gaske, ta gyara mun fuska da ɗan light make-up, ta yafa min gyale ya rufe mun fuska bayan ta fesa mun turare duka jikina, ina jin su duka suka fita suka barni ni kaɗai, nidai ban iya nace musu komai ba sai hawaye na da nake sharewa, ga wani irin fargaba da nakeji yana cika zuciyata, bayan wasu ƴan lokuta masu ɗan tsawo sai naji an buɗe ƙofan ɗakin baki cie da sallama, A.G ni ya shigo ina jin shi ya mayar da ƙofan a hankali ya rufe, ya ɗan daɗe kaɗan abakin ƙofan, daga baya kuma sai naji takun tafiyan shi yana shigowa cikin ɗakin, duk wani sautin takun shi haka nake jin sautin bugun zuciyata, kafin ya ƙaraso na haɗa wani uban zufa kaman nayi gudun ceton rai.
Zama yayi a bakin gadon ya ƙura mun ido, chan kuma ya saka hannun shi ya yaye lulluɓin kan, runtse idona nayi naƙi kallonshi, ajiyan zuciya ya sauƙe mai ɗan ƙarfi kaɗan, sannan ya sunkuyo da kanshi saitin fuskana ya sumbaci goshina, "*MARABA DA KYAKKYAWAR SALIHAR MATANA, MARABA DA RAYUWAR A.G, MARABA DA HASKEN ZUCIYA DA GIDAN A.G, MARABA DA ƊAWISUN A.G*"
ya ƙarasa faɗa yana haɗa fuskanshi da nawa, nidai har lokacin ido na duk suna kulle, sai hawaye ne kawai suke bin kumatuna, harshen shi ya saka ya fara lashe hawayen, hakan da yayi ya sakani fashewa da kuka, shiru yayi ya dakata da abun da yakeyi, muryah a hargitse yace, "Eeshan A.G meyake faruwa? Kukan kewan su ummie ne ko kuma na farin cikin kasancewa da A.G? Idan na kewa ne nima na koma gefe nayi tagumi na kewan mummy nah, idan na farin cikine don Allah ki jirani muyi tare".
Ido na duka na buɗesu akan shi, wai kukan farin cikin ganina a gidan shi? Lallai ma, shi bai san kewan ƴan'uwana da iyaye na nakeyi ba ko? Rufe idona na sakeyi na ƙara sautin kukan, rungumoni yayi jikin shi sosai ya na lallashi na, da kyar dai ya samu nayi shiru, daga nan ya kamo hannu na muka fita zuwa parlor.
Kan kujera ya zaunar dani ya kunna mun T.V, sannan ya dawo gefe na ya zauna hannun shi riƙe da nawa yace, "kiyi kallo zanje nayi wanka na dawo, zaki bani labarin abunda kika kallah, ko zaki rakani nayi wankan"?
Juyar da kaina gefe ɗaya nayi na ƙi kallon shi, murmishi yayi ya miƙe ya wuce side ɗin shi, yakai kusan 45mns kafin ya dawo parlon cikin wasu white kayan bacci, three quater ne da riga armless, sai wani ƙamshi a hankali da yake tashi a jikin shi, kitchen ya wuce ya ɗauko ledan da ya bansan lokacin da ya kai kitchen ba, a saman tray ya ɗauro da filet da cups, ƙamshin kajin ne ya cika parlon wanda jin hakan yasaka ni wani mummunan faɗuwar gaba, wanda har sai da naji alaman kaman fitsari ya ɗan biyo jikina, ɗan gyara zama nayi ina mamakin tsoron da nakeji mai sakani mummunan faɗuwar gaba irin haka, duk yadda yayi naci naman nan kasawa nayi, daya takurani ma kuka nasaka mishi, haka ya haƙura yaci naman yasha jus ɗin shi, daga nan ya tattare su ya wuce ya kai kitchen.
Bayan ya dawo ne yazo gabana ya miƙo mun dukka hannayen shi akan na miƙo nawa ya tayar dani tsaye, kawar da kaina gefe nayi na tashi tsaye ni kaɗai, hannu ya saka ya riƙo ni, muryan shi chan ƙasa yace, "Beauty kina tsoro nane? Kini cin komai? Tou muje narakaki ki chanja wannan kayan ki saka na bacci a ɗakina," ɓata rai nayi ina kallon shi nace , "zan iya zuwa ni kaɗai," idon shi cikin nawa yace, "kayan suna ɗakina ne, su nake so ki saka bana son musu", shiru nayi kaman ina tunani sai kuma na bishi, duk jikina a tsarge da fitsarin da naji kaman yana shirin zubuwa.
muna shiga ɗakin shi naji kaman an kwaɗa mun guduma a tsakar kaina, dole naja ƙafana na tsaya na dafa kan, a ɗan furgice yace, "kan yana miki ciwo ne"? Kai kawai na ɗaga mishi alaman ehh ban buɗe baki ba, kuma hannun yana dafe da kannawa, kamoni yayi yana shirin zaunar dani a bakin gadon shi sai naji wani sarawan kan ya ƙaru, dole na ja na tsaya naƙi, "bana son zama kaina yana ciwo sosai,"
"shiyasa nake son ki zauna ae princess, ina son ki ɗan ji sauƙin ciwon kan ne"
Raina ne naji yana ɓaci, ga wani tafasa da zuciyana yakeyi lokaci ɗaya, ƙwace hannu na nayi na fice a ɗakin da sauri, ina jin idan ban gita ba zuciyata zata buga, da sauri na koma side dina ina harhaɗa ƙafafu, ina shiga ɗakina na wuce direct zuwa toilet, ina cire panta ɗina sai naga period ɗinane ya dawo, abun sai ya ban mamaki domin banfi 9dys dagamawa ba aka ɗaura aure na, yanzu dai inaga 10dys ne ko 11dys da gamawa, dama babu abun da basu saka mun a toilet ɗin ba, sbd haka gyara jikina nayi na cire kayan na ɗaura towel, domin ganin ya ɓata mun har dogon rigan da nasaka, ɗakin na dawo na ɗauki kayan bacci mai riga da wando na saka, shafa jikina nayi gaba ɗaya da humrah, ina juyowa naji ya buɗe ɗakin ya shigo, gaba ɗaya sai naji kaina ya sake sara mun, gefen gadona naje na zauna na ɗaure fuskana, takowa yayi ya zauna dab dani, "nikan ka tafi ɗakinka bana son ganinka, kaina ciwo yakeyi sosai idan na ganka,", na faɗa mishi ina jin wasu hawayen ɓacin rai suna zubo mun, ido ya ƙura mun sannan yace, "beauty don Allah kidai na kukan nan, wallahi babu abinda zan miki da babu yaddan ki, kizo muje gobe zan kaiki ki sake ganin ummien",
"ummimato" da iya ƙarfina naji bakina ya buɗe na furta mishi, wanda tsabar firgitan da yayi sai da ya ja baya, har wani hakki nakeyi na tashin hankali nace, "kafita ni bana son ganinka, wari kake mun, kafita kaina zai gashe idan ina ganinka", na faɗa murya na cike da ihuu mai ƙaran gaske, wanda har sai da ya toshe kunnen shi ya miƙe tsaye.
Kuka na fashe da shi na baƙin cikin ganin ya ƙi fita a ɗakin, Aunty nice a cikin ƴan lokuta kaɗan naji babu abinda bana son gani irin A.G, gashi wani wari mai ƙarni nakeji yana mun, don har zuciyata tashi takeyi, shi kuma gaba ɗaya hankalin shi tashi yayi sosai, "Eeshaa don Allah akwai laifin da na miki ne da na shigo? Ko tafiyan danayi na barki zuwa wanka ya ɓata miki rai ne baby"? Ya ɗan ƙara matsuwa kusa dani kaɗan da nufin rarrashi na, aiko na taƙarƙare na zabga uban ihuu mai ƙaran da sai da ya miƙe da sauri yana furta, "innalillahi, Ayshaa me na miki ne please? Ko gida kike son na kaiki ne"?
Harara na zabga mishi nace, "kalan ace banida hankali yau ankawo ni na dawo gida? Kawai ganinka ne bana sonyi, kuma kana tare mun numfashi mai kyau, kawai ka fita kada na mutu", na faɗa da ƙarfi sosai ina miƙewa tsaye ina zare mishi ido.
Hannu ya ɗan ɗaga mun alaman rarrashi, "tou shikenan Eeshaata zan fita amma don Allah kiyi addu'a ki kwanta, kada kiyi kuka kiyi bacci", hararan shi nayi wanda ban taɓa tunani a rayuwa zanyiwa wani ɗa namiji ba ballantana A.G dana samu kaina dumu-dumu a ƙaunar shi, don kawai bana so a gane irin son da nake mishi ne kawai nake sharewa, amma sai yanzu nagane ashe M.G hiran shi da kulawan da yake nuna mun ne ya ja hankalina da shi, amma zuciyata A.G take muradi, haka yafice a ɗakin cike da damuwa yana waiwayo wa yana kallona, yana fita naji nutsuwa yazo mun, har wani ajiyan zuciya na sauƙe a lokacin, sannan kuma chan ƙasan zuciyata inajin ban kyautawa A.G ba, amma kuma a zahiri kuma ina jin kaman lafiya na samawa kaina, haka dai cike da damuwan abunda na mishi na kwanta.
Baccin da na kwanta ba mai daɗi bane ko kaɗan, domin wani mafarki nayi marar kan gado, mafarkinayi na ganni cikin wani forest mai ɗan duhu kaɗan ina tafiya ni kaɗai, ta baya na kuma ina jin taku mai ɗan ƙarfi a bina a baya da na juya sai naga wani narkeken mutum ne ke biye da ni, babu riga ajikin shi sai gajeren baƙin wando, gashi dogo a murtuƙe, wuyan shi da sarƙan mai ɗauke da hutun doki a jiki, ganin yana nufoni sai nayi sauri nayi gaba na ɓuya a jikin wata bishiya, ina kallon shi har yazo ya wuce bai ganni ba, ina ganin yayi gaba yana ta dube-dube bai ganni ba sai na fito na koma da baya na fita a cikin bishiyoyin, ina fitowa kuwa sai na haɗu da mamie da ƙawarta surkuwar raliya da ƙanwarta sun saita ni da bindiga a hannun su, juyawa nayi zan koma ciki kuma sai naga zabgegefn mutumin tsaye ya ƙura mun munanan jajayen idanun shi, a daidai nan na farka a firgice, duk da A.Cn da yake aiki a ɗakin amma na haɗa uban zufa a fuskana har zuwa wuya na, tashi nayi na zauna cike da tsoro, waiwaya wa nayi na ƙarewa ɗakin kallon amma banji alaman komai ba, naso na koma na kwanta amma naji ajikina pad ɗina ya ɓaci, haka na lallaɓa na shige toilet na gyara.
Da safe tun kafin 7:00am na tashi na gyara ɗakina na shige nayi wanka, dogon rigan lace cotton na saka a jikina mai ruwan ganye, ɗinkin yayi kyau sosai ya kuma zauna ajikina, turare na saka na wuta a cikin burner na koma na zauna cike da zulumin yadda zanyi na fito zuwa parlon, ina haka har wurin 9:00am sai ga driver gidan su da wata ƴar'uwan mummy sun kawo mana breakfast, har ɗakina ya shigo ya gaya mun na fito mu gaisa da matan, jiki duk a sanyaye na yafa gyale nabi bayan shi, cike da fara'a a fuskanta ta amsa mun gaisuwan, sannan tace mummy na gaishe mu, nima cike da girmamawa na mata godiya, inaji tana gayawa A.G zasu shiga gidan M.G ne su miƙa musu nasu, har wajen parlon na rakota, anan na tsaya nace ta gaida mummy.
Ban daɗe da zama ba naga ya shigo ɗakina, a bakin ƙofan yaɗan dakata, fuskan shi cike da damuwa da alaman rashin bacci akai, murya ƙasa-ƙasa cike da rauni yace, "morning my dear", kunya naji ya ɗan rufe ni, kaina na sunkuyar ƙasa sannan ni na gaishe shi, "fito kizo muyi breakfast ko, idan babu matsa kafin mutane su fara sintirin zuwa"? Cike da jin kunyan shi da abunda na mishi jiya na miƙe nabi bayan shi, zama mukayi akan dinning muka fara break tare, duk kunya lulluɓe dani muka ƙarasa karyawan tare, nidai tunda nayi ƙasa da kaina ban yadda na ɗago ba har muka gama, gashi ban iya na ci wani abun kirki ba, baice mun uffan ba ya ci abincin shi sosai, ina ankare da shi peppesoup ɗin yafi maida hankali akai, muna gamawa na tattare komai nayi kitchen da su, wanke abubuwan da muka ɓata nayi, sannan nazo na ɗan goge parlon na saka turaren wuta, fitowa na baya parlon shiyasa ina gamawa na koma nawa parlon na kunna t.v na zauna, nidai ba kallo nakeyi ba tunani kawai na tafi mai dogon zango, ban san shigowan shi ba sai zaman shi a gefe na kawai naji, a razane na kalle shi, murmushi yayi mun mai kyau a fuskan shi, "M.G ya angonce yabar twin brother shi da kwanan fargaban me yayiwa amaryah take ihuu da kuka haka?"
Sun kuyar da kaina ƙasa nayi ina wasa da zoben hannu na, don duk maganan shi sai tasaka naji kunya sosai.
"Any way babu matsala idan amaryah ta furgice a rananta na farko a gidan ta, sai dai hankalina ya tashi daga nin irin razanatan da nayi, har sautin muryanki fa ya chanja gaba ɗaya kaman bake ba", ya faɗa yana kamo hannaye na da nashi hannun, ban iya nace komai ba sai kallon yatsuna da suke sheƙin lalle a hannun shi.
"Beauty akwai wani abu da ranki bai so bane wanda na miki shi a jiya"? Najiyo muryan shi yana mun tambaya, duk kunya ta lulluɓeni na girgiza kaina alaman a'a, lumshe idon shi yayi ya tashi ya matsu kisa dani sosai, hannun shi yasaka ya ɗagoni dukka na ya ɗaura a saman cinyan shi, ban neme tashi daga jikin shi ba sai dai fama da na fara da faɗuwan gaba da kuma sarawan kai, a hankali yakwantar da kanshi a kafaɗa na yana murza mun hannaye na da suke cikin nashi hannun.
"Beauty ina so ki buɗe baki kigaya mun duk wani abu da baki so na miki marar kyau a zaman takewar mu, sannan me kika fi so a zamanmu da zamuyi tare? And nima kuma zan gaya miki meye nake so meye bana so, fatan zaki bani dukka hankalin ki wurina"?
Ɗaga kai nayi na kalle shi, sai naji son shi da tausayin shi sun cika mun zuciya, narasa dalilin dayasa jiya na mishi abun da na mishi.
Dukkan hankalina da nutsuwata na maida shi kanshi.
*AUNTY NICE*
managarciya