WATA UNGUWA: Fita Ta 31
BABI NA TALATIN DA ƊAYA
Matashiyar budurwar ta yi murmushi ba ta ce komai ba, sai takowar da ta fara yi zuwa gaban teburinsa.
"Wai me na faɗa miki a ranar farko ta haɗuwarmu ko kin manta ne, na tuna miki?"
Ta wadata fuskarta da murmushi sannan ta zauna akan kujerar dake fuskantarsa ba tare da ta ɗauke ido akansa ba, ta ce
"Taya zan manta da kalmomi na farko da suka ratsa tsakanina da abin begen zuciyata?"
Kallonta kawai yake cike da takaici ganin tana bata masa lokaci da shirmenta ya ce "Wai meke tafe dake ne? Me kike so da ni da kike bibiyar rayuwata? Wanene ma ya nuna miki nan wajen?"
Ta ƙara yin murmushi sannan ta ce "Acikin tambayoyin da ka mun a yanzu guda biyu ne kaɗai zan iya amsa maka a yanzu." Ta gyara zama tare da canza salon maganarta, cikin sauti irin na salon jan ra'ayi ta ce
"Abin da ke tafe da ni kyakkyan albishir ne zuwa gare ka, Abin da nake so da kai kuma shi ne Kai kanka."
Cikin mamaki da rashin fahimtar inda kalamanta suka dosa ya kafe ta da ido "Ban fahimce ki ba Malama."
"Ka kira ni da Sofi ba Malama ba." Ta ɗan tsagaita sannan ta ɗan girgiza kai kaɗan ta ce "Ina nufin na zo nan ne don na yi maka albishir cewa ka samu tsuntsuwar da zata maye maka gurbin wacce ka rasa. Ita wannan tsuntsuwar idan ka yi Sa'a kai ne da kanka zaka gasa namanta sannan ka cinye abinka ba tare da an samu wani tasgaro ba, saɓanin waccen tsuntsuwar da ta hiranye maka, ka kasa kamawa."
Ya miƙe tsaye "Sofi kike kowa? Na gaji da sauraren wannan shirmen banzan naki, idan abin da ke tafe dake kenan, zaki iya tafiya domin ba ni da lokacin batawa."
Ta sake ƙayata fuskarta da murmushi sannan ta ɗora kafa ɗaya akan ɗaya.
"Kada ka damu, ina gama faɗar abinda ya kawo Ni zan tafi, duk da cewa bana ƙosawa da kallonka tamkar dai yadda mage bata gajiyawa da farautar ɓeraye."
Ta ja fasali sannan ta ɗora da cewa "Ka tambaye ni dalilin da ya sa nake bibiyar rayuwarka, to Bakomai ba ne fa ce Ina sonka, kuma na yiwa kaina alƙawarin mallakarka a matsayin miji duk rintsi."
Ya zazzaro ido a mamakince ya ce "What? Anyah kanki ɗaya kuwa? Wai ni kike so zaki aura?"
Ya shiga girgiza kai "Inah! Yarinya kin makaro, a yayin bincikenki akaina kin bar wata kafa mai matukar muhimmanci, da ace kin lalubo ta ba zaki yi gigin zuwa nan ba." Ya ɗan zagaita yana kallonta a rai ne.
"Wai shin kin kalli kanki a madubi kafin ki baro gida kuwa? Kalle ki fa da kyau sannan ki sake kallona, ai ko ba Rayuwata Mahee ke ba Ajina ba ce."
Ya sauke zancen a hasale.
Nan fa Sofi ta miƙe cike da jin zafin kalamansa ta shiga ƙare wa suturar dake jikinta kallo, wai ko zata hango wata makusa a jikinta ko a shigarta. Sai dai da yake yan magana sun ce gwano baya jin qarfin jikinsa bata iya hango aibinta ba.
Ita ana ta ganin ta ƙule adaka domin atamfar sallarta ce ma ta sako, kuma sai da ta tsaya ta tsantsara kwalliya da take jin cewa ko gasar sarauniyar kyau zata je ko bata zo ata ɗaya ba, zata fito a cikin uku mafiya zarra. Kowa a gari sai zuzuta kyaun shigarta yake yi. Amma shi wannan tsabar rainin hankali ita yake faɗawa haka?
Wannan dalilin ya saka ta ɗago ƙananun idanuwanta ta zuba mishi su tana yi masa murmushin yaƙe.
"Ban ga wani aibi a tattare da ni ba, ko ba komai nasan nafi waccen kilakin da kake taƙama da ita mutunci."
A zafafe ya taso mata kamar zai ya galgala namanta "Ke wa kike kira da Kilaki? Ba dai matar tawa ba."
"Korarriya nake nufi, wacce labarinta ya bazu a gari, wa yasan ma ko can inda ta je tallar jikin nata ta ke a ......"
Bata samu damar ƙarasa maganar ba saboda saukar wani zazzafan mari da ta ji a kuncinta. Ta dafe kuncin da hannu ɗaya ya matso yana huci "Ki fice ki bar mini office dina bana ƙaunar sake ganinki a rayuwa, idan kika sake kika sake nuna mini wannan mummunar fuskartaki, duk abinda ya faru kece sila."
"Ni ka mara akan wata kucaka?" Ta faɗa tana jijjiga kai, sannan ta ɗauki jikarta daga kan teburinsa ta nufi hanyar fita har ta kai ƙofa ta dakata tare da juyowa.
"Ka da ka yi tunanin wasan ta ƙare daga nan, yanzu ma aka fara, ina matuƙar sonka kuma sai na mallake ka duk rintsi, sai na yi nasara akan Maheerah ka ajiye wannan a ƙwaƙwalwarka."
Ta fice tare da banka ƙofar da ƙarfe har sai da ya tsorata, ko da yake ba iya shi ba dai dai da sakatariyarsa ta razana da jin wannan ƙarar.
A haka Sofi tabar ofishin Irfan cike da ƙunar zuciya da tunanin ɗaukar ƙwaƙƙwaran mataki akansa.
******"
Ta isa gida cike da ɓacin rai da damuwa a dai-dai lokacin kuma ta riski mummunan labarin da ya birkita ƙwaƙwalwarta har ya saka ta Mantawa da babin rayuwar Irfan.
Bakomai ta riska a gidan ba face labarin mutuwar yayarta Hanifa wanda hakan ya dugunzuma hankalinta ainun.
"Shi kenan wai da gaske Hanee ta mutu ba zata dawo ba Maryam?" Ta faɗa tana kallon Maryam idonta cike da hawaye.
Cikin kuka Maryam ta ce "Sai haƙuri yaya Sofi, kowa lokaci yake jira, mutuwa rigar kowa ce idan baka saka ta a yau ba zaka saka ta watarana."
Nan fa Sofi ta shiga zubar da ƙwalla tana sambatu kala-kala.
"Yanzu ba ni da abokiyar faɗa kenan? Da nasan da zuwan wannan ranar dana roƙi gafarki kafin ƙasa ta rufe idonki yayata. Ki yafe mini, Allah ya gafarta Miki zunubanki."
Duk mutanen dake zaune a gidan makokin sun tausayawa Safiya ganin halin da ta shiga har suna yi mata fatan shiryuwa a zuƙatansu.
Dai dai da Mankas ya nutsu a wannan ranar, har da shi da abokansa a yan zaman makoki, duk sun sha jallabiya kamar yaran arziƙi....
Inna da Baba Mudi kuwa a ranar ba a cewa komai a yanayinsu sai godiyar Allah "mutuwa mai wa'azi."
Ummu Inteesar ce