HAƊIN ALLAH:Labarin Cin Amana Mafi Muni Fita Ta Biyar 

HAƊIN ALLAH:Labarin Cin Amana Mafi Muni Fita Ta Biyar 
 
   Labari da rubutawa
       
   *Hauwa'u Salisu (Haupha)* 
 
 
 
          Page 5
 
Sai da muka iso shagonmu muka daina gudun, sai dariya muke tamkar wasu zararru, da farin ciki muka afka shagon bakina ɗauke da kalmar "Babana?" Kamats! Naji saukar kyakkyawan mari kan fuskata ko ban tambaya ba nasan hannun Iyami ne, domin na gama haddace kalar marinta. Zaman daɓas nayi ƙasa ina kallon shagon na jujjuyawa, ban dawo hayyacina ba naji saukar dundun da yasa na dawo cikin hankalina.  "Shege tsinene kana saurin ubanwa ne?"  Alawiyya dake tsaye tana zare idanuwa tace, "Ce mana akwai Babanta ya zo Iyami."  Fau ta buge bakin Alawiyya tace, "Ubanka ne ya gayama zuwansa?" 
Alawiyya tai tsit kar ta sake samun rabonta na marin ita ma.
 
Gabanmu ta ɗauki jakarta ta rataya ta fice tana cewa mu ci-gaba da kula da shagon sai ta dawo. Bata jima ba da tafiya Sule ya shigo ranshi ɓace ya zauna ya kasa mun magana sai kallona kawai da yake bai ko ƙyabtawa. "Jiddah ki ci-gaba da haƙuri tabbas ko da laifin Iyami akwai laifin Oga Dawa kana babba ace kana kama maganar mace wadda ke cike da son zuciya da munafurci, Babanki ya zo nan ganinki amma sai Iyami tace mai kina yawan ce mata duk ranar da ya zo tare za ku tafi, bayan kina nan zamanki lafiya kin iya karatu kin iya aikin girki komai cikin jin daɗi amma kin rantse sai kin bishi duk ranar da ya zo. Hakan yasa yace to kar a kira ki ba sai kin zo ba ya ganki tunda kina lafiya shike nan ai komai ya yi daidai. Shi ne fa ya tafi gidanta ya ci abinci ya huta yanzu haka fitar da tai wajen shi ta nufa suka tafi ta nuna ma shi abin da kike buƙata ya sai maki ya wuce abin sa sai kuma watarana idan da rabon ku sake ganawa." Sai yanzu kukan baƙin ciki ya zo min wanda ke tafe da tsanar mahaifina tabbas bai sona da yana sona ba zai kawo ni uwa duniya gun kafura ba yace ta riƙe ni ba, har nai shekaru huɗu bai ganni ba kuma ya zo ya tafi bai ganni ba kan wata magana marar tushe, nan take naji cewar ni da Alawiyya bamu da bambanci duk kanwar ja ce bamu da iyaye don haka na rungume ta na fashe da kukan tausan kanmu.
Mun jima muna kuka Sule na bamu haƙuri har muka haƙura muka dangana amma tsanar mahaifina na cikin ƙasan zuciyata fal, na ji a raina ba zan sake furta kalmar data shafe shi ba, haka ba zan sake furta kalmar ina da uba ba zan zauna a yadda Allah Ya yi ni kawai.
 
Iyami kuwa ta samu kuɗaɗe da kayayyaki gun Baban Jiddah sosai ta ƙara samun jari mai tsoka, tai ta nuna ma shi kayan da take siya tana aikawa da su ƙauyensu ana saida mata na yara tana cewa duk na Jiddah ne, shi kuma yai ta jin daɗi yana murna da godiya gareta har ya gama abin da zai ya koma bai damu ba don bai ga ɗiyar shi ba sam.
 
Sai da Iyami ta tabbatar da tafiyarshi ta dawo shagon fuska fal farin ciki da walwala saboda tasan ta gama da babin ba kuma zata taɓa yarda ya rabata da Jiddah ba tana da burin ta maida yarinyar addininta ta haɗa ta aure da ɗan mijinta idan lokaci ya yi zata gudu da ita garinsu tunda ba wanda yasan garin data fito daman.
 
Alawiyya tun tana kukan rashin Inna Kande har ta haƙura ta shafawa kanta lafiya ta rumgumi ƙaddara, ta amince cewar bata da kowa kaf faɗin duniya da zata nuna tace shi ɗin ahalinta ne, jama'a da dama na kiranta shegiya ce wasu ma jam'i suke har da Jiddah kira suke duk shegu ne,don ma sauƙin da suka samu guda ne Iyami tayi matuƙar fice gun rashin mutunci da masifa ba baƙon abu bane gunta ta hunce ta yi dambe da ƙato ba tai mai lilis. Tunda wani ɗan iska ya taɓa nuna zai taɓa Jiddah ta hunce tai mai duka gaban mutane ta ci mutuncinsa sai kowa ya maida maitarsa ya ɓoye suka shafawa Jiddah lafiya ko maganar banza babu mai tarar ta da ita, duk da ƙanƙantar ta takan gane mutumin banza dana kirki yarinya ce natsatstsa da tasan ciwon kanta yadda ya kamata kasancewar Alawiyya itama halinsu guda sai tasu ta zo ɗaya har abota ta shiga tsakaninsu.
 
Yau da gobe kayan Allah. Inna Kande tai shekara bata ba labarinta sai Iyami ta kira Alawiyya ta gaya mata kuɗin da Inna Kande ta bari nata tuni sun ƙare don haka ba zata ci-gaba da ci da ta da bata wajen kwana ba sai dai ta dinga haya idan bata iyawa ta kama gabanta. Wannan magana ta girgiza mu sosai ta sa mun kwana kuka muna neman mafita kan lamarin domin mun fi kowa sanin halin Iyami indai ta ce abu to tabbas sai ta aikata shi take jin daɗi kuma ba wanda ya isa ya hanata aikata abin sai fa idan an biyo ta hanyar manyan mutanen nan masu kima da daraja a idanun kowa da kowa watau ƴan dubu-dubu abin shan iska!  To mu kuma waye gare mu da zai zo mata da mutanen nan masu taurin kima da daraja a gunta? Sule ne kuma shima yana shirin tafiya garinsu wai aurensa ya matso don haka zai koma garinsu da sana'arsa, har sai da Alawiyya taban shawarar na bishi na je gun mahaifiyata amma na ƙi saboda ba zan iya barin Alawiyya ba a halin yanzu kuma ita mahaifiyata me yasa bata taɓa nema na ba? Me yasa bata taɓa zuwa inda nake ba? Tabbas itama bata sona don haka nima duk bana son su!
Iyakar tashin hankali da rashin imani da rashin tausayi mun ganshi gun Iyami domin hatta ni sai ta hana kwana ɗakinta sai bakin ƙofar ɗakin wai na taya ƙawata kwana tunda bata da kuɗin biyan haya ai itama kuɗi take biya take kwana ɗakin. Abinci kuwa sai idan an siya an rage muke ida cinyewa gwara masu bara da mu domin su suna samun abinci da kuɗi ko da yaushe amma mu fa muke abincin amma ba a bamu wanda zai ishe mu sam. Balle kuɗi da sai dai mu riƙe na aike ba dai namu ba.
Sule yai bankwana da mu ya tafi bayan ya bamu Naira dubu yace mu raba. Innalillahi! Bayan kwana biyu da tafiyarsa mu ka fitar da kuɗin muka sai takalmi silifas saboda bamu da shi ƙasa muke yawo a ranar Iyami ta kusa haukacewa tana cewa kuɗinta ne muka sata muka kashe ta fito tsakiyar layi tana ta ihu tana hauka kamar kamun baƙaƙen aljanu. Zuwa can bayan ta gama haukan da zage-zagen ta rarumo mu tai ta jibga ta gwarancin da nasan ba makawa zagi ne da yarensu. Sai da tai mana lilis sannan ta ƙwace takalman ta ɓoye tace sai tayi sati biyu bata ban abinci ita daman Alawiyya bata bata nawa ne idan na kankare ƙanzo muke ci tare, shi kanshi ƙanzon don masifa ba duka take ban ba shanyar shi take yana bushewa wai tarawa take tana aikawa garinsu.
Rayuwa tai mana zafin gaske har mun fara shawarar ya kamata mu gudu daga hannun Iyami mu je wani gun tunda gari da yawa maye bai cin kansa gwara mu matsa gaba ko barar ce gwara mu yi kawai da zaman rashin ƴancin da muke kara zube kamar kamun turawa (Bayi) 
Kamar Iyami tasan shawarar da muka yanke na guduwa sai ta daina zuwa ko'ina baki ɗaya ta natsu ta saka mana ido kan lamurranmu bata barin mu matsa ko nan da can, hatta kasuwa tare muke zuwa ta sai abin da zata siya ta jibga mana kamar wasu ƙatti ba tausayi haka zata haye mashin tace a bi sannu tare take da mu. 
 
Watarana muna zaune muna gyaran kayan miya Iyami ta shigo shagon a ruɗe sai yarensu take na alamar tana cikin tashin hankali, mu dai bamu kalleta ba muka ci-gaba da abin da muke don babu wautar da zata saka mu tambayeta mu ja ma kanmu bala'i, don sai ta sauke fushinta kanmu. Daɓas ta zauna ƙasa ta ɗora hannu saman kanta ta dinga fasa ihu tana kiran,
"Jesus! Jesus! Jesus!  Ganin abin nata kamar taɓin hankali yasa muka miƙe a hankali da zummar barin wajen saboda yau ne farkon ganinta a irin wannan yanayin, ko ranar da taita hauka da muka sai takalma abin bai kai haka ba ai. Muna niyyar fita sai ga ƙawarta Sebo ta shigo itama a ruɗen ta faɗa jikinta tana kuka da kiraye-kirayen Jesus ɗin itama. Kasancewar yanzu babu abin da banji na yarensu saboda yau da gobe da Iyami ke mun yasa na gane abin da Sebo ke cema Iyami har ma na fahimci sanadin tashin hankalin da Iyami ke ciki. Sebo ta dafa cinyar Iyami tace, "Kar ki kuskura ki haƙura da abin da Jerry ya yi maki, akan me zai maki haka? Duk ƙoƙarin da kike ma shi bai gani ba shi ne sai ya saka maki da mugun tukuicin kishiya? Ba kwanaki nace ki ƙara farashin kuɗaɗen da kike tura ma shi ba... Me yasa baki ƙara ba...kin dai san yadda Jerry yake da masifar son kuɗi bai kamata ki dinga ma shi ɗan aike ba, to yanzu ga inda ta kai ku nan ai ya aiko ma ki da saƙon ƙarin aurensa."   Na fahimci damuwar don haka na kama hannun Alawiyya muka fice don na samu damar yi mata ƙarin bayani duk da nasan ta fahimci kaɗan. 
Muna zagayawa bayan shagon muka kwashe da dariya, duk da ƙarantar mu muna mamakin yadda su al'adar su Iyami mace ce ke neman kuɗi tana ba mijinta shi ba ruwansa sai dai yana zaune gida mace tai noma ko ta nemi wata sana'ar tai ta yi shi iyakarsa ta ba shi kuɗaɗe yana bin mata yana shaye-shaye.  Duk yadda Iyami ke dunƙule kuɗaɗe tana turamai don su zauna lafiya hakan bai sa ya tausaya mata ba sai ya tara kuɗin ya yi aure da su. Gaskiya maza ba dama (in ji Alawiyya) nan muka buɗe shafin rayuwar aurensu Iyami muna ta dariya.
 
Kwana uku da faruwar abin Iyami ta haɗa kayana da nata tace na shirya zamu tafi garinsu ta gama zama Lagos don haka Alawiyya ta san inda dare ya yi mata ba inda zata je da ita ni kaina don akwai burin da zata cika kaina ne yasa zata tafi da Ni.
 
 
Kwana guda mu kai muna kuka muna neman yadda za mu yi ƙarshe dai daren ranar da zamu tafi da Iyami muka bi dare muka gudu ni da Alawiyya.
 
 
To fa ina za su je guduwa cikin babban gari irin Lagos wanda kana zuwa zaka ga an maƙala THIS IS LAGOS saboda abubuwan dake cikinsa.
 
 
Taku dai a kullum Haupha.