WATA UNGUWA: Fita Ta Shidda

Kai tsaye ta wuce gidan baba tsoho mai ice, da yake a gidan akwai yan haya biyu da ya saka a ɓangaren da ba kowa, to ɗaya daga cikin yan hayar ne ke siyar da abun kwalam na yara don haka ta nufi can don ta agaji cikinta da ke ƙugin neman agaji. Gidan shiru kamar ba kowa, haka yarinyar ta shige, har ta sa kai za ta  wuce can ƙuryar don siyen abun da ya kawo ta.

WATA UNGUWA: Fita Ta Shidda

P 6

 

BABI NA SHIDA

 

"Daga yau ba na son ƙara ganinka a cikin gidan nan, ka ji dai abun da na gaya ma ko?"

Nura cikin rawar baki ya ce "Eh yaya na ji." Domin dai ya san halin Habibu duk da bai cika kula da abubuwa ba, amma duk ranar da ka shige masa hanci da gudundune tabbas zai fyatoka.

 

Sake masa hannu ya yi. Tun da Nura ya ji hannunsa ya samu 'yanci ba tare da ɓata lokaci ba ya ranta ana kare.

 

Shi kuwa Habibun a zuciye ya ƙarasa gun da 'yarsa ke kwance cikin wani irin yanayi, ya saka hannu ya ɗauke ta tare da saɓa ta a wuya ya yi cikin uwar ɗaka da ita ba tare da ya ko kalli Biba ba.

 

Biba da har a lokacin ta ƙasa motsawa, zaren tunaninta ya tsinke a daidai lokacin da ta kasa samawa kanta mafita, kallo ɗaya zaka yi mata kasan a ruɗe take.

 

Da ƙyar ta yunƙura tana kama zaninta dake suɓalewa ta bi shi cikin ɗakin tare da zama ƙasa kusa da ƙafafunsa yayin da shi kuma yake zaune a kan gado.

 

Da ya so ya sanya duwatsu ya taushe zuciyarsa, sai dai yanayin tafasa da azalzalar da zuciyarsa ke masa sun hana harshensa dakatawa daga faɗar "Ke wace irin mata ce Biba? Gidan mijinki kika mayar matattarar marasa jin unguwa? Da kuruciyarki da komai amma ki zauna ki na aikata aikin da ko wata dabba ba zata yi ba?"

 

Sadda kanta ƙasa ta yi, duk da ta ji zafin maganganunsa matuƙa, amma ta sani laifinta ne da ta kasa lura da lokacin dawowarsa tsaɓar daɗin Hira, ga shi tana so ta ɗebo ruwan dafa kanta, yau idan Habibu ya tsinka sauran igiyoyi biyun da suka rage ina ta dosa?

 

Tunawa ta yi da farkon zamansu bayan haihuwar Salma da shekara ɗaya ta taɓa yin Yaji zuwa gida, ko da Abbansu ya zo ya tarar da ita ya ji kuma meke tafe da ita sai ya ce "Biba ki tattara ki koma gidan Mijinki, ku ci gaba da rufawa juna asiri. a yanzu dai ba ni da mazauninki a nan gidan, wallahi kika sake kika kashe aurenki za ki gano cewar ɗan kare dukiya ne."

 

Ai kuwa ta tabbatar da hakan bayan Abban na su ya tabbatar da rabuwar auren, da kansa ya kora  ta ya ce duk ma inda zata je ta je amma ba zata zame masa ƙaramar bazawara a gida har ta ɓata masa tarbiyyar ƴaƴa ba." Da ƙyar da siɗin goshi aka samu yan'uwansa suka lallaɓa shi ya bar ta ta zauna a gidan har zuwa lokacin da Habibu ya mayar da aurensu, amma fa ta sha wuya a tsakankanin lokacin, domin an bautar da ita a gidan tamkar ba gidan ubanta ba....

 

"Biba wai ba da ke nake magana ba ne?"

 

Muryar Habibu ce ta tsinke mata tunanin da ta zurfafa a koginsa.

 

"Na...'am, yi haku...ri ban ji ba.. ne." Ta faɗa muryarta na karkatsewa.

 

"Ki mayar da hankalinki a mazauninsa, ki nutsu sosai ki saurare ni Biba, na fara gajiyawa da irin abubuwan da kike mun, ban da Shashanci irin na ki ya za'a yi ki bari ƙato kamar Nura ya shigo mun gida har ya yi rashe-rashe haka kamar ɗakin tsohuwarsa, kuma a tsakiyar mata ma, kenan ke ce ke ƙara ɗaure masu ƙugu suna abun da suka ga dama ko?."

 

"Yi haƙuri mai gida wallahi ban yi tunanin shigowar Nura nan gidan zai baƙanta ma rai ba, na ga shi ɗan uwanka ne shi ya sa....."

 

"Dakata Biba! Idan shi ɗan'uwana ne amma ai ba muharraminki ba ne ko? Nasan cewa shi jinina ne duk da ba ciki ɗaya muka fito ba, amma ba hakan ke nuna zan bar ƙofar gidana sake ga kowanne ƙaton unguwa ba."

 

Rausayar da kai ta yi cikin wani irin ladabi da ko ita bata san tana da shi ba ta ce "Don girman Allah ka yi haƙuri mai gida insha'allah daga yau ba za a ƙara ba."

 

Jin hakan ke da wuya ya yi kwanciyarsa kan gadon tare da rungume yarsa ba tare da ya ce mata kanzil ba.

 

 

Washegari tun ƙarfe takwas na safe Habibu ya fito da shirin fita, sai kuma ya tsaya cak yana ƙarewa ƙazamin gidan nasa kallo.

 

"Biba!" Ya kira sunanta da ƙarfi, da sauri ta fito gudun kar a kuma.

 

Ya dube ta ya ce "Don Allah kalli gidan nan ki ga yanda ya yi dagaje-dagaje ga shara nan ko'ina kamar bolar cikin gari, wai ni kam sai yaushe za ki san ciwon kanki ki fara tsafta ne? Ita fa tsafta da kika gani tana cikin addini."

 

Bata ce masa komai ba kawai sai ta hau sosa bayan ƙeyarta tana kallon gidan a ranta ta ce"kai wannan mutumin ya cika rigima, yau fa kwana biyar kenan da na yi shara ko sati ba a yi ba, amma yake faɗar wai gida ya yi datti, bayan ko shekaranjiya waccen Sofi tamun shara da ta zo."

 

"Ni zan tafi don Allah ki tabbatar da kin tsaftace gidan kafin na dawo." Ya na gama faɗa ya sa kai ya wuce abunsa.

Ita kuwa tsabar jin haushi ko Addu'ar Allah ya tsare ba ta masa ba.

Juyawa ta yi zuwa ɗaki tana faɗar "Bari Hanee ko Sofi su zo sai in saka su share mun don ni ba zan iya da kayan duƙe-duƙe ba, mutum da ƙuruciyarsa ana neman tsofar da shi ƙarfi da yaji."

Ko da ta shige ɗakin guri ta nema kan gado tana shaƙar barcinta, haka ta bar ƙofar gidan buɗe.

Can bayan rabin awa Salma ta farka tana kukan yunwa ga kuma tsamin jiki. Sai dai me duk ihun kukan da take Biba bata ko sani ba domin tuni ta kai birnin sin a duniyar barcinta, Allah ya jarabceta da masifaffen barci kamar kasa.

Salma da ta ga haka, sai ta hau jijjiga ta tana faɗar "Mama tashi, yunwa nake ji, Mama." Ganin cewa duk abin nan da take yi mamanta bata yi ko gezau ba bare ta tashi, kawai sai ta sauko daga gadon tana neman abinda zata ci.

 

Nan ta shiga duddubawa tana buɗe duk wani kwano ko kofin da ta gani bata ga komai ba, ga shi Madafar a rufe take ba za ta iya buɗewa ba.

Kawai sai ta koma ɗakin Maman nata inda ta ga kuɗi ɗazu, ta saka hannu ta dau Hamsin ta fice daga gidan.

Kai tsaye ta wuce gidan baba tsoho mai ice, da yake a gidan akwai yan haya biyu da ya saka a ɓangaren da ba kowa, to ɗaya daga cikin yan hayar ne ke siyar da abun kwalam na yara don haka ta nufi can don ta agaji cikinta da ke ƙugin neman agaji.

Gidan shiru kamar ba kowa, haka yarinyar ta shige, har ta sa kai za ta  wuce can ƙuryar don siyen abun da ya kawo ta.

Baba Tsoho dake zaune ƙofar ɓangarensa da kasance a farkon gidan, ya saka baki ya kira ta "ke yarinya zo."

Ba musu ta tako zuwa inda yake "Ga ni Baba."

"Me kike so?" Ya tambaya yana wani shu'umin murmushi irin na tsoffin Banza.

"Awara ko carbin malam zan siyo." Ta ba shi amsa cikin rashin maida hankali don kuwa hankalinta na can kan abin da za ta siya.

"Tun safe haka, waya aiko ki?" Ya faɗa yana ƙoƙarin janyo hannunta.

"Ba kowa yunwa kawai nake ji." Ta sake mayar masa.

Wani murmushin ya yi mai ma'anoni ya ce "Zo mu shiga cikin gidana na baki abinci ki ci sai kin ƙoshi kuma ina da carbin Malam ɗin ma duk zan haɗa miki."

Ko da jin haka sai yarinya ta hau tsalle-tsallen murna, ba musu ta bi bayansa. Suna shiga ya garƙame ƙofar gidan, da yake dama shi kaɗai ke rayuwa a gidan don ba shi da mata ta rasu, ƴaƴansa kuwa duk sun yi aure wasu har sun fara aurar da ƴaƴansu.

Biba tana can tana barcin asara ba ita ta farka sai wuraren 10:40 na safe ko da ta farka ba ta ga Salma kwance a kusa da ita ba, hakan bai dame ta ba, ta fito tsakar gidan a nan ta tarar da Salma rakuɓe can gefe tana kuka. A madadin ta matsa ta saurari matsalar 'yarta kawai sai ta ce "Ke wane irin iskanci ne kike yi wa mutane kuka tun da safe kamar wacce aka daka?"

Ɗagowa yarinyar ta yi hawaye duk ya wanke mata fuska har wani ya bushe, ta tako zuwa gun mahaifiyarta tana wata kalar tafiya a wawware.

"Ke Salma! Yau wane irin iskanci ne ya same ki, ji wata tafiyar iskanci, maza ki gyara ko na ɓaɓɓalaki yasin." Ta faɗa cikin hargagi.

Salma ta fashe da kuka tana faɗar "Zafi nake ji idan ina tafiya."

Kallon yarinyar ta yi a sheƙe, tana ji kamar ta wanke ta da mari "Je ki nemi guri ki zauna, ni bari na fara wani abu, sauri na ke zan je gidan yaya Hanne."

Yarinyar ta kalle ta ta ce "Mama kin san wannan mutumin mai itace na can gidan, shi ne ya......" Ba ta jira yarinyar ta ƙarasa zancen ba ta katse

"Ke ni don Allah je ki nemi guri ki zauna kin cika ni da surutu, Haba! Yarinya ƙarama sai iya gulma." Ta faɗa cikin tsawa.

Sum-sum Salma ta ja ƙafafunta ta je ɗaki ta rakuɓe, ita kaɗai ta san abin da take ji.

Daga waje Biba ce ke ta sababben surutun nata ita kaɗai tamkar hauka sabon kamu.

"Wai yau ya aka yi ne mutanena ba su zo ba kamar dai jiya? Gaskiya bari na nemo su ina da yunwar ganin su musamman Hanee da nake so ta sammun tsamiyar dake jakarta."

Miƙewa ta yi ta ja yalolon hijabinta duk ya cukurkuɗe ya yi duƙun-duƙun ta nufi ƙofar gida, sai da ta je soro sannan ta sanya hijabin, yau ma daga ita sai ɗaurin ƙirji take zaune tun da mai hali baya fasa halinsa. A hakan kuma ta fice ba tare da ta yi tunanin sakko da zanin ƙasa ba.

Kai tsaye gidansu Sofi ta wuce, a nan ta samu labarin abin da ya faru a bakin yaran gidan da suke shaida mata suna asibiti da abin da ya faru da su.

Girgiza kai kawai ta yi ta fito tana ƙwaƙular hanci, ɗaya hannun kuma tana soshe-soshen kai "Gaskiya abu bai yi daɗi ba sam, duk da na so a gabana komai ya faru na ɗebe ƙeyar ido." Ta faɗa tana murmushin da ba za ka iya tantance na miye ba.

Har ta ɗau hanya kamar za ta koma gidanta sai kuma ta miƙi hanya zuwa gidan yayarta tana Faɗar "Bari na ga ko da ragowar ɗumame na sake ci ko na samu ƙarfin aiki, don ruwan tea ni basa riƙe ni." Haka ta ci gaba da jan ƙafafu kwashal-kwashal kamar mace doki har ta ƙarasa gidan yayar tata.

"Assalamu alaikum" ta shiga gidan da sallamarta "Wa Alaikumus Salam ƙaraso." Yayar ta faɗa tana daga ciki kan tela.

"A'ah! Yayata ana nan ana tara mana kuɗin ne? Kin san fa ranar bikin Hafsarmu akwai shagali ba, don ko Abba ba ya so sai mun yi bidi'ar nan."

Dariya yayar ta yi sosai kafin ta ce "Tsiyata dake kenan, mayyar bidi'a ce har kin manta waye Abbanmu, kuma kike yi da shi." Martani dariyar ta mayar mata yayin da take ƙarasawa cikin gidan tana faɗar

"Manta da zancen ko waye shi yaya, kawai in kina da ɗumame ba ni in ci dama shi ya kawo ni." Ta ƙarashe zancen tana nufar madafa.

Yayar ba ta ƙara cewa komai ba sai girgiza kai da ta yi a ranta tana alawadai da halaye irin na ƙanwar tata.

Da kanta ta zubo dai-dai wanda ya ishe ta ta zauna tana ci sai zuba surutu take, bayan ta yi naƙ ta miƙe ta nufi hanyar gidanta.

 

A can gidan nata kuwa bayan fitarta Zubairu ya shiga gidan da Sallamarsa "Biba kina ina? Zo ki ji yau fa ta samu." Shiru ya ji alamun ba kowa, har ya juya zai fita ya jiyo sautin shessheƙar kuka a ɗaki da sauri ya nufi can don ganin miye. Kuma da yake dai ba su da shamaki da kowanne ɗaki a gidan tamkar ɗakin iyayen su.

A falo ya yi kiciɓis da Salma ta haɗe kai da gwuiwa tana kuka ƙasa-ƙasa. Nan ya tsaya yana kallonta a ransa yana wassafa abubuwa. 'Gaskiya yarinyar nan kyakkyawa ce, idan ta zama budurwa ba ƙaramar kyakkyawa za a yi ba, don har zarta mahaifiyarta a kyau, sosai za a huta a nan.'

Har ya juya da nufin fita daga ɗakin zuciyarsa ta kwaɓe shi, wani ɓangare na zuciyar tasa ya fara kimsa masa mugun nufi 'Zubairu kada ka ɓata damarka, tunda uwar ba ta nan ka rage zafinka a nan, dama abin da ya ci doma ba ya barin awai duk da ba abun kirkin da za ka tsinta a nan ɗin."

Sosai ya gamsu da shawarar zuciyarsa don haka ya matsa kusa  "Salma me ya same ki ne?" Ya faɗa tare da ɗaukar yarinyar ya ɗora ta kan cinyarsa a daidai lokacin ne kuma Biba ta Kunno kai a cikin ɗakin.

 

Tsayawa ta yi cak kamar an dasa ta a wurin, ta zazzaro ido domin abin da idonta ya gane mata a yau ya razanata matuƙa....