Ɗan sanda ya mutu a otel yayin saduwa da budurwarsa

Ɗan sanda ya mutu a otel yayin saduwa da budurwarsa

Wani dan ɗansanda, Lawal Ibrahim daga ofishin 'yan sanda na Kwali, ya rasu a yayin da ake zargin suke tarayya da wata budurwa a  Otel din Palasa Guest Inn da ke yankin Gwagwalada, Babban Birnin Tarayya Abuja.

Abuja Metro ta rawaito cewa lamarin ya faru ne ranar Alhamis da ta gabata, da misalin karfe 6:00 na safe, lokacin da marigayin ya shiga dakin otal tare da wata budurwa mai suna Maryam Abba.

An samu labarin cewa marigayin ya gayyaci budurwar daga Dutse, Jihar Jigawa, bayan sun fara haduwa ta hanyar sadarwar zamani watanni uku da suka gabata.

Wani shaida ya bayyana cewa marigayin, mai muƙamin sifeto ya yi tarayya da budurwar a daren Laraba har zuwa misalin karfe 6:00 na safe, lokacin da budurwar ta tashe shi kuma suka sake yin wata tarayyar karo na biyu.

An samu rahoton cewa bayan wannan karo na biyu, budurwar ta lura cewa numfashin marigayin ya fara rikewa  kuma daga baya ya daina motsi. Ta yayyafa masa ruwa, amma duk da haka bai motsa ba.

Budurwar ta hanzarta yin ihun neman agaji sannan ta sanar da manajan otal ɗin, wanda aka bayyana sunansa a matsayin Danlami Palasa, wanda kuma ya gaggauta sanar da sashen ‘yansanda.

Manajan otal ɗin ya garzaya zuwa sashen ‘yansanda na Gwagwalada inda ya ba da rahoto game da lamarin, sannan aka tura jami’an tsaro zuwa otal din, inda aka tarar da gawar jami’in a cikin dakin.

Rahotanni sun ce an kama budurwar nan take, yayin da aka dauki gawar jami’in zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa sannan aka ajiye gawarsa a dakin ajiye gawarwaki na asibitin.