Cire Tallafin Mai: Jihohin Arewa Ne Suka Fi Shiga Wahala

Cire Tallafin Mai: Jihohin Arewa Ne Suka Fi Shiga Wahala

 

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa an samu karin farashin litar mai zuwa N545 a watan Yuni. Karuwar ya kai kashi 210 idan aka kwatanta da yadda dan Najeriya ke shan litar mai akan N175 a watan Yuni na shekarar 2022. 
Hukumar ta fitar da wannan kiddigar ce bayan bincike tare da wallafa bayanan a shafinta kamar yadda Legit.ng ta tattaro.
Tsadar man fetur din ya samu dalili ne tun bayan cire tallafin mai da Shugaba Bola Tinubu ya yi a watan Mayu. Hukumar ta fitar jerin jihohin da suka fi siyan mai tsada da kuma wadanda ke siya da araha. Jihar Taraba ta fi kowa ce jihar siyan mai da tsada akan N562.86 akan kowa ce lita, sai kuma jihar Yobe akan N562.31 sai kuma Kano akan N561.82. A daya bangaren, jihar Anambra ta fi kowa ce jiha siyan mai din da sauki akan N534.44 sai kuma jihar Ebonyi akan N535 da kuma jihar Oyo akan N537.43. 
. 1.Taraba - N562.86
 2. Yobe - N562.31
 3. Kano - N561.82
 4. Gombe - N560.83
 5. Borno - N557.14 
6. Jigawa - N556.67
 7. Abia - N552.73
 8. 8. Adamawa - N551.25
 9. Kogi - N550.83
 10. Kaduna - N549.53
 11. Zamfara - N549.09