Zargin Bata Suna: Hamdiyya Ta Fadi Abin da Faru da Ita a Sokoto bayan Fitar da Bidiyo

Hamdiyya ta faro yadda ta samu mai garin Sabon Birnin Daji, inda ta bukaci yin bidiyo kan abubuwan da ke faruwa har ya amince mata. 

Zargin Bata Suna: Hamdiyya Ta Fadi Abin da Faru da Ita a Sokoto bayan Fitar da Bidiyo

Al'ummar Najeriya suna cigaba da tofa albarkacin bakinsu kan cafke 'yar TikTok, Hamdiyya Sidi Shareef da aka yi. 
Hakan ya biyo bayan wallafa wani faifan bidiyo da ta yi kan hare-haren yan bindiga da kuma cin zarafin mata da yara da ke yi a Sakkwato. 
A cikin wani faifan bidiyo da shafin Brekete Family ya wallafa a Facebook, Hamdiyya ta yi bayanin yadda lamarin ya kasance. 
Hamdiyya ta faro yadda ta samu mai garin Sabon Birnin Daji, inda ta bukaci yin bidiyo kan abubuwan da ke faruwa har ya amince mata. 
A cikin bayaninta, Hamdiyya ta ce bayan wallafa bidiyon yan banga sun zagaye gidansu da motoci da babura inda suka yi ta dukan yan uwanta har sai da suka bar numfashi. 
Daga bisani an dauke ta a mota domin zuwa ofisoshinsu suka yi ta dukanta a mota da cewa ta bata sunan Gwamna Ahmed Aliyu. 
"Sun yi ta zagina inda wani ya ce mani jaka, dabba ko ubana bai kai ya ɓaci gwamna ba bare ni, na ce ni ba bacinsa na yi ba idan har shi zai ji haushi su wadanda abin ke faruwa a kansu fa." 
"Ya ce lokacin da Hon. ya sa a nemo ni da ya hadu da ni harbe ni zai yi a haka rami a birne ni a ce yan bindiga ne suka yi ajalina." 
 Hamdiyya Sidi Yar gwagwarmayar ta kara da cewa yan banga sun kai ta bayan kanta, suka tube mata hijabi da barazanar yi mata fyade idan ya so ta je ta ba da labari. 
Ta ce jagoran yan bangan ya ce mata sai ta je gidan yari ko kuma duk inda suka hadu, shi ne ajalinta saboda a kan Gwamna bai san rayukan da ya dauka ba. 
Daga bisani, Hamdiyya ta ce an wuce da ita ofishin yan sanda a Wurno, aka ci zarafinta sannan wani dan sanda ya yi mata barazanar kisa idan ta fadi abin da suka yi mata. 
Hamdiyya ta kara cewa daga bisani an kai ta kotu har aka ba da belinta amma ta koma gidan kakarta kafin kurar da ta taso ta lafa da kuma tseratar da rayuwarta.