'Yan Bindiga Sun Hallaka Sojoji 5, Jikkata Wasu 11 a Katsina

'Yan Bindiga Sun Hallaka Sojoji 5, Jikkata Wasu 11 a Katsina

 

Mummunan fada ya kaure tsakanin dakarun sojoji da kuma 'yan bindiga a jihar Katsina. Lamarin ya yi sanadin mutuwar sojoji biyar da raunata 11 yayin harin a sansanin sojoji da ke karamar hukumar Faskari a jihar. 
Harin ya faru ne da misalin karfe 2:00 na rana a ranar Lahadi 12 fa watan Mayu inda fararen hula suka rasa rayukansu da wani dan banga, cewar Leadership.
Premium Times ta tattaro cewa hatsabibin ɗan bindiga, Ado Aleiro shi ya jagoranci maharan kusan 200 zuwa sansanin a kauyen Yar Malamai. "Yan ta'adda sun kai farmaki sansanin sojoji a jihar Katsina wanda ya yi sanadin mutuwar sojoji da dama." 
Daga cikin wadanda suka rasa ransu akwai ɗan banga mai suna Tukur Ali wanda bai wuce shekaru 30 ba a duniya. Farmakin wanda ya shafe tsawon awanni biyu ya tilasta dakarun sojojin ja da baya domin tsira zuwa wani wuri amintance. Har ila yau, ƴan ta'addan sun tafka asara suma a bangarensu yayin da suka kawo farmakin.