ZAMAN JIRA: Fita Ta Uku

ZAMAN JIRA: Fita Ta Uku

ZAMAN JIRA


               *NA*
*HAUWA'U SALISU 




                          Page 3

Jabeer ya dubi Likitan a kunya ce ya girgiza kansa, domin abin da Nusaiba tai bai kamata ba, ana cikin yi masu bayanin abu mai muhimmanci za ta fice ko kallon Likitan ba tai ba fuska ba yabo ba fallasa.  Kafin su ce wani abu sai gata ta dawo ta koma gunta ta zauna ta dafe kanta, ganin kallon da Jabeer ke mata ya sa ta haɗe rai ta dubi Likitan tace, "Doctor ya zan da wannan aman da nake ?" Hakan ya sa suka gane amai ne ya fitar da ita ba shiri, Jabeer har da yi mata sannu. Likitan ya rubuta mata magunguna ya bata shawarwari suka dawo gida.
Ko da suka dawo ba wanda ya sake komawa ta kan alert shi dai Jabeer murna yake ya ci Nusaiba da yaƙi domin duk macen daka aura idan baka haihu da ita ba ta more maka sosai. 

Nusaiba kam kwance take sai haɗawa da kwancewa take, tabbas tana son yara duk iskancinta tana son ganin jininta kuma masu tsabta don haka ne ma bata taɓa barin wani ƙato ya kusanceta ba tare da roba ba tun da take holewarta. Yanzu dai za ta iya kiran wannan lamari da, 'ga bikin zuwa ba zanin ɗaurawa'. Kursis duniyar ta ce mai cike da alatun more rayuwa, sai dai kuma cikin da zata haifa lahirar tace mai shiga tsakaninta da muggan zunubanta. Zaune ta tashi ta dafe kanta damuwa fal ranta. Duka biyun kowane nata ne, idan ta cire cikin tasan za ta iya samun wani cikin amma yaushe ? Kuma indai yanzu Kursis bata bar ta da ciki ba sai yaushe za ta bar ta da ciki, akwai buƙatar ta je gun Kursis kafin ta zo inda take, gaskiyar magana za ta haifi cikinta za ta kula da shi, ita ma tana son a kira ta da uwar wasu ko don gaba. Wannan tunanin shi ya ƙara mata ƙwarin gwiwar ji a ranta za ta iya tunkarar Kursis ɗin, don haka ta kwaɗawa Jabeer kira ya kawo mata waya.
Jabeer kam alwala ya yi domin ya yi sallar godiya ga Allah da ya azurta shi da samun albarkar zuri'a ta tsatson Nusaiba. Don haka ya yi mata gyaran murya, taɓe baki tai, domin tasan nafila yake ta godiya ga Allah shi zai zama uba nan gaba. Sai ta gyara kwanciyata domin tasan yana gamawa zai kawo mata wayar tun da ta ce ya kawo ɗin.
Haka kau  akai ya kwaso mata wayoyin duka ya kawo mata, yana ta jera mata sannu ba adadi, ta dube shi ta lumshe ido tana cewa a ranta, "Ai fa abin nema ya samu, matar ɗan sanda ta haifi ɓarawo. Yanzu zai ishe ni da tsirfar masifa shi ala dole ya yi ma mace ciki. 
Shi dai harkar sa kawai ya tambaye ta ko tana son wani abu tai banza da shi, hakan yasa ya gane bata buƙata don haka ya koma ɗaki ya shirya ya fito da shirin fita, sosai ta ji daɗi domin tana san yin waya da Kursis ko bai ce zai fita ba ita za ta fitar da shi daga gidan yanzun nan.
Ya shafi fuskarta ya ce, "Hajiyata zan fita ki kula da kanki please, idan kin ji kina san wani abu ki kira ni ko ki turamin saƙo don Allah." Da kallo ta bishi kawai don ji take kamar ta tura shi ta rufe falon. Yana fita ta tashi ta je ta rufe falon da key  duk nan bai mata ba ta shige ɗakinta ta rufe shi ma sannan ta kira number Kursis ɗin. Kira uku tana yi mata amma bata ɗauka ba, hakan na nufin Kursis fushi take da ita. Shin ba a haihuwa ita Kursis ɗin take da yara har shida? Indai har akwai adalci ai ya kamata ta taya ta murnar zama uwa ba wai ta ce ta zubar ba, kamar wani cikin shege take ɗauke da shi. Duk da cewar zaman jiran barin gidan take hakan ba zai hana ta haihu ba, ko da ranar da ta haihu ne ko ma bata haihu ba ta amince ta bar gidan idan ta samu damar bari, hakan bai shafi cikinta ba sai harkar ta da Kursis ta zuwa duniyar sama ce zata shafi cikinta? 'Gaskiya da sakel an ba mai kaza kai" dole ta binciko Kursis duk ƙasar da take domin su san mafita cikinta kam zama  daram-zaƙam tun da ya shiga ba zata cire ba sai ya zo duniya don kanshi. Ita fa a yadda take da mugun son yaran da za ta haifa ma bata ƙi duk shekara ba ta haihu, saboda dai kuɗi tana da su, babu abin da yaranta za su nema su rasa nan da shekaru da dama, to akan me za ta zubar da abin da take nemawa kuɗi dare da rana? Kai lamarin nan akwai mugun son kai tsakaninta da Kursis ma... Tai ta kai da kawowa tana zagaye ɗakin tana ci gaba da kiran number kursis ɗin ita kuma tai mirsisi ta ƙi amsa kiran domin bata jin cewar za ta iya amincewa da buƙatar Nunu na rainon ciki a zo kuma aje kan rainon yaran da za a haifa ba, sai dai idan tana haihuwa aka gama suna za ta amince su kai abin da aka haifa ƙasar Misra ai rainonsa can ya shiga karatu a can to za ta iya haƙuri ta jure hakan. Gama wannan tunanin yasa ta miƙe ta watsa ruwa ta kira waya a zo a kaita Nigeria saboda tana China a lokacin. 
Nunu ganin Kursis ta ƙi amsa wayar yasa ta sake watsa ruwa saboda wani zafi da ke bijiro mata ta nufi gidan Kursis domin ta kira ta da lambar ɗaya daga yaranta tasan za ta amsa idan ta ga su ne ke kiranta.  Faka-faka ta shirya ta faɗa mota ta bar gidan ta nufi gidan Kursis hankalinta a tashe.


             *********************

             GIDAN NAFI'U


Bayan an gama duk wasu gwaje-gwaje Likita ya tabbatar masu da tana da ciki har na wata uku, wani sanyin daɗi ya soki zuciyar Nafi'u, yayin da hawaye suka zubo ma Fati, ko shakka babu ta shiga jerin masu zaman jiran mutuwar aurensu, domin bata manta labarin da aka bata ba akan duk matar da ta haihu guda sai Nafi'u ya sake ta. Kuma ita shaida ce na iske tarin yaransa har biyar a gun mahaifiyarsa kowane uwarsa daban. Nafi'u ya dube ta cike da mamaki sai kuma ya kalli Likitan ya tuntsure da dariya ya ce,  "Ita kuma wannan kuka ne cikar farin cikinta."    Shi ma Likitan ya yi 'yar dariya kawai da yake, yasan  duk wani ka-ce-na-ce da ake kan auri sakin da Nafi'u ke yi, shi kam shi zai iya zama  shaida saboda wannan matar ita ce ta shida cif da za ta haihu a gidansa. Tausai yarinyar ke ba shi, ga shi mugun duk sanda zai aure bai taɓa auren babba sai ƙaramar yarinya tana haihuwa kuma ta yaye yaron yake sakinta. Haka nan dai Likitan ya rubuta masu magunguna ya ba su shawara kan yadda za su kula da cikin ya sallame su.

Yana lura da yadda jikin Fatin ya yi la'asar amma sai ya share sai wasu surutan banza yake wai dama an ce ciki na ƙarawa mace daɗi bai yadda ba sai yanzu, domin a tsakanin wata ukun nan ya ji sauyin yanayi mai shegen tsayawa a rai bayan ya fita gida, hatta idan wata ta rantse sai ta ba shi alheri ya shiga bai jin ya kai na Fatin maiƙo da damshi ashe ciki ne ɗan bala'i yake manne a cikin alheri kaca-kaca. Ita dai bata ce ƙala ba sai hawayen da take sharewa lokaci zuwa lokaci har suka isa ƙofar gidansu, ta ɗauka ba zai shiga ba amma abin mamaki yana gaba tana baya ma.
Suna shiga gidan mutanen gidan duk suna tsakar gida, ya washe baki kamar wani na Allah ya ci-gaba da gaida kowa, ta yi mamakin yadda akai ma suka amsa mai gaisuwar, tsabar ya fi kowa iya rashin daraja ya buɗe baki ya ce ma Mamarsu Fati, "Ya Asiya ta dawo gida? na so na kawo ta amma sai na ji ban iyawa saboda wata buƙata ta gaggawa data bijiromin a gaggauce wadda ban isa na kauce wa aikata ta ba, don haka nace ga kuɗin Napep ta taho kawai."  Kallon-kallo kawai suka dinga yi masu gidan suna jinjina ma kansu da suke surukuta da Nafi'u. Asiya dake kwance a falo tana jinsa tai banza ta ƙyale shi. Ya dubi Fatin yana murmushi ya ce,  "Madam zan wuce amma fa ki kulamin da kayana sosai ban san matsala don nasa rai nan da wata shida kin fito min da kayana." Bai jira komi ba ya juya yana murmushi ya bar gidan. Fati ta sunkuyar da kanta ƙasa hawaye na tsiyaya, wai mijinka ne ke wannan ɗibar albarkar a  gidanku gaban iyayenka da ƙannenka.  Ba wanda ya tanka mata, sai kowa ya kama harkar gaban shi aka barta tana ta kukanta ita kaɗai ba mai lallashinta. Asiya ce ta fito daga falo ta ja hannunta suka shiga ɗakinsu. Asiya ta dubi Fati tace,  "Yaya miye abin kuka ga abin da ya zama jiki, miye abin kuka ga abin da kowa ke zaman jiran faruwar sa? Yaya idan maye ya ci ya manta uwar ɗiya bai ci ta manta ba, a lokacin da Nafi'u ya zo da maganar neman aurenki kina tsaka da karatu za ki aji uku kika rufe ido kika ce ke kin ji kin gani kin yafe karatun aure za ki yi, saboda Nafi'u ya ce ba zai auri yarinyar da ta gama J.S.C.E ba, ke kuma da yake kina cikin duniyar soyayya kin makance sai kika yadda da tsarinsa, ki ka turje akan baki iya rayuwa sai da shi kin yadda ki rasa komai akan ki rasa auren Nafi'u, duk da cewa an sha yin tattaki ana gaya maki duk wadda ta je gidan Nafi'u zaman jira ne kawai ta je yi  tana haihuwa yake sakinta, amma kika turje kika tsaya kai da fata sai kin aure shi, har kina ma mutane rakin kunya.
Ban taɓa manta dukan da ake maki a gidan nan kan ki rabu da Nafi'u amma kika shafa ma idonki kwalli kika ce ba wanda ya isa ya raba ki da Nafi'u, har ƙarar su Mama ki kai babban gida gun Baba Alhaji kan a baki wanda kike so Nafi'u. A wannan hayaƙin ne Nafi'u ya shiga ya fita ya rufe bakin kowa gidan nan sai da ya aure ki. Fati ta dubi Asiya jin tace Nafi'u ya shiga ya fita. Asiya ta sake jinjina kanta tace, "Ƙwarai mijinki bin bokaye yake ba malamai ba domin wata ƙawata ta gayamin da asiri yake auren duk wadda iyayenta suka shiga tsakaninsa da aurenta kuma na yadda saboda rana guda kowa gidan nan ya koma son aurenki da Nafi'u. Babban abin da ke sawa ina jin ban iya zuwa gidanki saboda yadda ya maida ki kamar wata baiwa, sam bai jin tausanki bai san darajarki ba, kawai abin da ya sani shi ne ya kawo maki abinci ki saki ciki ki narka kawai lokaci bayan lokaci ya zo maki da buƙatar shi mijinki ne da kina so da baki so haka za ki je gare shi. Yaya Fati ki farka daga wannan shegen barcin da kike wanda bai amfana maki komai sai baƙin ciki, ki tashi tsaye kamar yadda shima ya tashi tsaye ki nuna mai banza bata kai zomo kasuwa, so nake Nafi'u yasan da cewa ko da goma ta lalace tafi biyar albarka. Akwai gun wani hatsabibin malami da Yayar ƙawata Rahama ke aikenta gun shi, ki zo mu je ko ni na je maki, ai ma shege asirin da zai koma ke ce ke juya shi bai da yadda zai yi,ai mai asirin da zai dinga jin tsoron ki kamar yadda yanzu kike jin na shi tsoron. Fati ta saki baki tana kallon Asiya cike da mamakin yaushe wannan yarinyar ta je inda bata je ba? Kodayake ilimi ma wani abu ne, don a kallo guda za a gane ilimi ya ratsa Asiya fiye da ita. Amma duk da haka ta ya za ai tai ma Nafi'u asiri bayan kodayaushe cikin yin hayaƙi yake da binne wancan yi wanka da wancan? Tabbas Nafi'u lamarinsa sai shi bata jin ko ta kai shi gun malami za ta ci nasara a kansa, sai dai kawai ta amince da waje guda ne kawai zata iya cin nasara akan sa shi ne ta shiga ta fita ta gyara Nigeriaeta yadda duk masifarsa ba zai ce ta buɗe ba balle ya sake ta ba. Idan kau tace za hau wannan layin to ko shakka babu ta shiga jerin mata masu kashe ma Nigeriarsu kuɗaɗe saboda gudun barin gidan mijinsu.  Asiya ta girgiza Fatin tace, "Yaya ke matsalarki mugun tsoro wallahi, kuma duk abin da aka saka tsoro a cikinsa ba a cin nasara don Allah ki cire komai a ranki yanzu ma ni ki tashi mu je na kai ki gun shi, kuɗi kuma idan kika tambayi Yaya Auwal nasan zai baki ba zai hana ki ba."  Hawaye suka zubowa Fati ta kama hannun Asiya ta riƙe tana cewa, "Asiya ke da kanki kin faɗi Nafi'u asiri yake, kuma ni shaida ce kan wasu abubuwan da yake gudanarwa a gida, kin ga kau idan har a tsaye yake to ba zan taɓa cin nasara a kansa ba,  sai dai na bi ma shi ta bayan gida. Nafiu mutum ne ɗan sharholiya, zai iya komai akan jin daɗi bai haɗa lamarin jin daɗin sa da komai ba, don haka zan kamo shi ta can zan gyara kaina na ci-gaba da gyara kaina naita gyara kaina sai an wayi gari Nafi'u ya gamsu da cewa na bambanta da sauran matan da yake saki saboda sun haihu. Tabbas Nafi'u ya fi son jin daɗi fiye da komai a rayuwarsa don haka ki tayani da addu'a kawai ki kuma dage da samar min kuɗaɗe a gun su yaya da su Mama shi ne kawai abin da nake neman ki taimaka min a kan shi 'yar'uwata."  Asiya ta kalli yayarta cike da tausanta kawai amma bata jin wannan hanyar za ta ɓille da ita,amma zata taya ta da addu'ar samun nasara a kan shi.  Asiyar ta ɗauko abinci suna fira suna ci har Fatin ta ci mai yawa, sannan suka koma ɗakin Mama domin Fatin ta gaisa da ita sosai saboda Nafi'u yasa komai ya tsaya a gidan. Da ƙyar Mamar ta amsa gaisuwar Fatin sai bin ta da harara take tana jin haushin son da ya kai Fati gidan miji marar kunya irin Nafi'u. Fati ta tsugunna gaban Mama tace, "Ki gafarta min Mama, tabbas har da alhakin ku ne ke bibiyata na ƙin jin maganarku na yi maku taurin kai na yi maku rashin kunya na gaya maku maganar da duk ta zo bakina akan auren Nafi'u, yau ga inda gari ya waye ni nan na shiga sahun matan da ke zaman jiran mutuwar aurensu."   Mamar ta dube ta sosai tana jin tausan ta amma bata san me yasa ba da yarinyar ta nace sai tai auren su kai mata auren ba. Tabbas su ma akwai laifinsu a cikin wannan lamarin, don haka ta yi murmushin da yafi kuka ciwo tace,  "Kowace mace bata tsallake ƙaddarar ta musamman ƙaddarar aure, Fatima na yafe maki duniya da Lahira, Babanku shi ne wanda ya buƙaci hakan tuni daman nice na hana. Allah Ya yi maku  albarka Ya tabbatar maku da alheri a rayuwarku baki ɗaya."  Farin ciki ya bayyana akan fuskarsu baki ɗaya, Fati na jin kamar ta rage wasu kaya masu nauyi daga kanta.

Sai yamma lis, Nafi'u ya shigo har cikin gidan yana ta washe baki kamar mai tallar makilin ya, dubi Asiya dake yi ma Fati kitso ya ce, "Wai ku baku jin wa'azi ne? Kodayake nasan kuna ji da mugun taurin kaine irin naku na mata, shi ya sa ku ke yadda kuka ga dama ba yadda mazajenku ke so ba. Yanzu ban da an raina ni miye na yi mata waɗannan kantama-kantaman kitson? Wannan fa daga gani ba zai daɗin ko ɗaura kallabi ba balle a shafa da hannu ba. Gaskiya a kwance shi a yi mata ƙanana kuma a yi wasu a ƙeya a saki wasu a gaban kanta yadda dai iya wuya duk inda na leƙa akwai inda hannu kai sauka yasa albarka. Ba zan iya rigar wahala ba ni, ina gani za a cuce ni nayi shiru ba." 
Asiya ta tsaya da kitson tana kallon Nafi'u saboda lamarinsa akwai ɗaure kai sosai, sai dai a yadda take ji a ranta ko zai mutu ba za ta kwance wanda ya iske suna yi ba, domin saura guda a gama kitson, ina laifi kitson da ya yi guda ashirin (20) shi ne zai kira da kantama-kantaman don wulaƙanci?.  Ita kam Fati duk da ranta ya sosu sai ta samu kanta da cewa Fatin, "Ki yi haƙuri a kwance a yi wanda yake so ɗin don Allah."  Asiya ta buga tsaki ta miƙe tsaye ta dube su baki ɗaya ta shige ɗakinta bata ce komai ba. Nafi'u ya duƙa ya taɓa kitson ya rabka salatin da sai da mutanen cikin ɗaki suka fito waje ya ce,  "Wallahi Madam ba za ki ɗauke ni ƙaton sakarai ba, kodayaushe ina gaya maki ina san ƙananan kitso a zubo wasu gaba wasu baya shi ne za ki zauna ai maki wannan kitson ?"   Mama ce ta kasa daurewa ta dube shi tace,  "Nafi'u lafiya ka ke wannan ɗibar albarkar a tsakar gidan nan? Idan matarka ka zo ɗauka mata ka tasa ta gaba ku wuce ba sai ka yi mana rashin ta ido ba."   Nafi'u ya dubi Mama da fuskar mamaki, ko dama can fa ita fa sai da malam ya kai ruwa fama kafin ya samo lagon 'yar banza, don haka ne ma malam ya ce mai kar da ya dinga haye mata komai na iya faruwa. Tunanin wannan yasa ya dubi Fati rai ɓace ya ce, "Taso mu tafi gida ke !  Mamar ta taɓe baki ta juya, Asiya ta miƙo mata hijabinta da niƙabinta dama bata cire safarta ba, ta amsa ta kasa furta ko kalma guda. Haka ta saka ta bi shi ba ko waige suka fice daga gidan tana jin ƙunar zuciya sosai.
Ganin kamar za tai kuka yasa ya kama hannunta ya ce, "Haba Madam, yanzu ke ranki ɓaci ya yi ma maimakon ki ban haƙuri kan abin da kika ja min sai ma ki haɗe rai kamar za ki yi kuka? Kin san dai ba zan bari a cuce ni ba, duk abin da bai min ba tsab zan kauda shi daga rayuwata don haka ba zan zaman jiran cutarwa a gareni ba. Ni mu je ma gidan akwai sabon darasin da na samo ki koya da kyau yau akwai zuwa duniyar sama mai lasisi. Gaya min balango ko tsire wanne za mu siya ne, don idan muka isa gidan can ban jin zan sake fitowa saboda so nake ki jefa ni cikin alherin ki mai shegen daɗin nan."  Gabanta ya faɗi, ita kam yanzu bata sha'awar ya kasance ta sam, ji take ta tsani kusantar ga shi idan ya fara bai san ya daina ba, ga tsirfar masifa sai ya gama laguda  mutum ya gama bin shi ta ko'ina ya sarrafa ya motsa ko'ina sannan yake shiga cikin duniyar samar, itama idan ya shiga don mugunta da sauri da ƙarfi da gudu duk yake haɗewa ya yi lokaci guda. Wata barazanar ma ita ce sai ya jima bai zo ba idan ya zo ma zai iya ci-gaba ko a jikinsa ga shi ya dinga sa ta tana ƙazanta domin sai dai ta kira hakan da ƙazanta shi kam ko kunya bai ji zai baje ya kama kwaɗa ihu yana sambatun da maƙwabta na jinsa.
Kan hanya ya tsaya ya yi masu siyayya sannan suka isa gida. Ko da suka zauna ya tashi har wani rawar jiki yake ya haɗa masu ruwan wanka suna fitowa ya baje masu naman da ya siyo,  tana ci kamar bata son ci ya dube ta yana kai yankan nama a baki ya ce,  "Watau Madam ki gane wani abu man, shi fa shiga cikin alherin dole ne, don haka gwara ki buɗe ciki ki kwashi nama ki sha madara iya madara saboda na ji daɗin kwasarki da kyau idan ba haka ba ke ce za ki kwashi ɓacin rai, saboda dai ni ko sama da ƙasa za su haɗu sai na kai geji don haka ne ma na tanadar maki komai kina ganin balangun nan ma mai romo-romo na siyo saboda yafi ratsa jikin mace ya zama sinadari.  Fati dai tana jin shi amma har a ranta bata san wannan lamari sai dai tasan cikin sauƙi zai mata wulaƙanci wanda ya fi duka zafi kamar na rannan ya barta ya tafi wajen wata ya kwana ya dawo yana miƙa yana gyatsa shi ala dole ya ƙoshi. Haka nan ta sha madarar ta ci balangun ta wanke hannu ta je ta saka kayan barci riga da wando dogaye ta kwanta tana jiran tsammani. Sai da ya gama komai sannan ya shigo kallo guda ya yi mata ya daka mata tsawar da ta sa ta tashi zaune tana kallonsa. Cikin masifa yake cewa,  "Ke karfa ki ɗauke ni ƙaton sakarai mana, taya za ki saka waɗannan zurma-zurman kayan barcin saboda ki kashe min feeling ke ga muguwa ko, to maza ki tashi ki sauya kayan barci ki saka ƙanana masu bayyana min kayana gumina halalina a fili duk cikin haƙƙina ne, amma saboda ke ga muguwa kin san dai ban san kina saka min kaya manya musamman da dare amma ke da yake kin fi ɗan iska iya iskanci gwara ba bugu ba zagi ki ke sarrafa ni ta hanyar yi mun muguwar shigar da ke kashe min nishaɗi ko? Hawaye suka zubo mata ta rasa me za ta ce, sai kawai ta tashi ta buɗe inda kayan barcinta suke ta dube shi tace, "Wanne kake so ciki na aka saka?"  Da kan shi ya zo ya ɗaukar mata wata fingilalliyar riga iya gwiwa fara ce tas, mai hudoji komai na jikin mutum a bayyane ya ce ta saka ta. 
Har ta fara kiciniyar saka rigar ya ce,  "Dakata Madam ban ji kina ƙamshi ta ko'ina ba, maza ki feshe jikinki da turarukan barci saura ki saka masu ƙarfi wallahi sai jikinki ya gaya maki."  Hata ta sake jan jiki ta isa gaban mirror ta dinga bin jikinta tana dilkewa da turaruka masu sanyin ƙamshi ta fesa turaren baki, saboda kiss naga cikin babban abin da ke kai Nafi'u duniyar sama yana san kissing yana son ta ko'ina ya ji ana ruɗa shi da sumbata ana kuma ɗan ja yi mai tafiyar tsutsa da sauransu to duk muguntar sa sai ya kai geji don haka da ta fara galabaita take zuwa makasarsa kai tsaye ta datse Film ɗin. Tunanin hakan yasa ta ji dama-dama ta gama shirya wa fes yana tsaye yana kallonta ya ga me za tai, ita kuma sanin hali yasa ta afka jikinsa ta fara manna mai kiss ta ko'ina suka faɗa kan gado labarin ya sauya zuwa na manyan fatake masu zuwa duniyar sama.  Sai dai wannan karon Fati duk yadda ta so ta jure lamarin Nafi'u kasawa tai ƙarshe ma sai wani uban amai ya taso mata, wanda yasa dole Ogan ya sauka ta ruga toilet ta cigaba da sheƙa amai.  Da ƙyar ya samu ya dawo hayyacinsa ya biyo ta, shi ya zuba mata ruwa ta wanke fuskarta ya cire mata rigarta ya shiga watsa mata ruwa da nufin yi mata wanka amma saboda rashin tausai sai kawai ya juya ta shi ala dole nan ma wani sabon style ne ana wanka. Ji take komai ya fice ta har ga Allah ta tsani abin da yake mata, amma bata isa ta bayyana mai ko ta nuna mai ba, don haka sai kawai ta sakar mai komai ya yi ya gaji ya barta ta huta. Ya jima bai ƙyale ta ba sai da don kan shi ya tabbatar da cewa duk wani maganin da ya je ya siya ya sha ya maida kuɗinsa sannan ya yi wanka ya fice ya barta nan tana maida numfashi. Tana wanka tana hawaye har ta kammala ta fice zuwa ɗakin. Har ya kwanta ya ja bargo ya rufe jikinsa, kayan da ta saka da farko tai niyyar maidawa amma gudun wata masifar sai ta sauya wasu zuwa riga mai gajeren wando ta sake fesa turare ta haye gadon ta kwanta tana jin alamar zazzaɓi na son sauko mata, a son samunta ta kwanta cikin jikinsa amma shi bai san mace ta raɓe shi idan zai barci ya fi son ya yi baje-baje kawai bai son jin kowa kusa da shi, hakan na takura mata amma bata da yadda za tai dole ta takure waje guda ta ƙudundune tana jiran ikon Allah kawai.

Can cikin dare ciwo ya ishe ta zazzaɓi ga mararta sai katsawa take kamar me, ta ja jiki ta matsa kusa da shi tana tada shi ya tashi bata lafiya.

Tsaki ya ja ya dube ta idonsa cike da barci ya ce,  "Ai fa na bani daga jin kina da ciki shike nan kuma sai tsirfa kala-kala  daga wannan sai waccan za ki fara tsiro min da su ko. To wallahi tun wuri ki yi ma kanki karatun ta natsu ba wannan ne ciki na farko ba da na taɓa yi ba, wannan shi ne na shidda cikin da na yi wa mace na sunna idan kau aka koma wancan ɓangaren kau ba zan iya ƙirgawa ba, don haka ki san matsaya. Jin haka yasa ta koma inda take ta yi bulum kawai tana sauraren ikon Allah. 
 Sai wajen asuba sannan barci ya sace ta.

Tun da safe ya sake lalubo ta wai karin safe, da ƙyar take iya buɗe idonta ta dube shi hawaye na tsiyayowa a gefen idanunta tace, "Ka yi haƙuri ka rufa min asiri ban da lafiya ban yi barci ba sai yanzun da asuba sannan barci ya kwashe ni."  Yi yai kamar bai ji ta ba, ya ci-gaba da abin da yake jin shi ne daidai sai kuma zafin jikinta ya takura mai sosai ya ja tsaki ya tashi baki ɗaya ya shige toilet ya watsa ruwa ya fito ya shirya zai fice ya ce,  "Ki yi min fankasu ko alkubus ki min miyar agushi kar ki sa nama kisa min ganda da kifi ." Bai jira amsarta ba ya sa kai ya fice daga gidan.
Kuka take da ƙarfi babu mai lallashinta, sai da ta ci kukanta ta more sannan ta juya ta cigaba da barcinta.

Nafi'u na fita ya je can gidansu domin ya gaida iyayen sa ya ga yaransa ya basu kuɗin kalaci (breakfast) kamar yadda yake yi kowace rana, idan ya je da safe zai ba su kuɗin breakfast da na abincin rana da dare kuma ya ce su ci tuwon da ake yi a gidan.
Hajiyarsu ta kalle shi tana son su yi magana amma ya kama yara sai kutsun wasa suke kamar wasu yara baki ɗaya. Ganin bai da niyyar barin yaran yasa ta ce ma yaran su fita za tai magana da Babansu.  Bayan sun fita ta duni Nafi'u sosai tace,  "Yanzu kai abin da kake kyautawa ne, ace cikin garin nan babu wani labari da ake sai naka. Gidan suna gidan biki duk labarinka kawai ake da taro ya taru, shin ba za ka natsu ka san me kake yi ba, anya kuwa kana son ka gama duniya lafiya?"  Ya sosa ƙeya ya ce,  "Hajiya kar dai surutun mutane ya fara tasiri a kanku, ai ni ko a jikina saboda dai ba haram na aikata ba, Allah shi ya halarta yin aure haka shi ya halarta saki, don haka duk masu magana ku bar su da maganarsu tun da ban taɓa zuwa nace su cika min sisin kwabo ba idan zan yi auren ba. Kuma ban da ma mutane suna sun su latsa ni kaf garin nan nine kawai mai sakin aure Hajiya. Ni dai don Allah kar ki bari mutane su shiga tsakaninki da ɗanki. 
Sai Hajiyar ta rasa bakin magana duk da cewar akwai wata maganar bayan wannan da take son yi mai amma tasan yadda ya taso mata daga wannan ita ma waccan haka zai taso mata amma duk da haka sai ta zakuɗa zamanta tace,  "Amma miye gaskiyar labarin da ake na tsakaninka da yaran gidan Audu niƙa ne?"   Ya zuba mata ido na seconds sai kuma ya girgiza kai ya ce,  "Kai mutane wallahi shi ya sa talauci ke ta cin ubansu, su fa waɗannnan yaran taimako ne tsakanina da su, kuma a matsayin su na mata bai kamata su nemi taimakona ba na kasa taimaka masu ba, don haka kowace ta zo gareni nake taimaka mata su kuma mutane sun saka idanu suna ta ƙananan maganganu kan hakan, shi ne har sai da aka zo maku da maganar ashe ita ma bayan waccan ta farkon ?"  Dama haka ta zata don haka tace kalle shi tace, "Allah Ya kyauta, amma dai ka sani duk abin da kai Allah na ganinka kuma kai ma ka haifa don haka abin da ka aikata ma yaran wasu kaima za a aikata ma yaranka." 
Yana sosa ƙeya ya tashi ya fice yana cewa"Allah Yasa mu dace dai." Ta bishi da amin.

Yana fita kai tsaye shagonsa ya buɗe da yake  a jikin gidansu yake nan yake saida kayayyaki na provision bai ma saida ɗai-ɗai sai carton-carton yake saidawa. Zaman sa ke da wuya ya fitar da wayarsa ya kira Nafisa ɗaya daga cikin yaran gidan Audu niƙa, ya ce ta same shi a shago yanzu kuma ta sako zani kawai ta zumbulo hijabi babba har ƙasa. Ya kunna kallon da ya zame ma shi jiki na iskanci ya ci-gaba da yi yana zabura yana narkewa kan kujerar da yake zaune.  Yana cikin kallon Nafisar ta shigo tana shigowa ya ce, ta rufe ƙofar shagon ɗaya ta bar ɗaya a buɗe, haka ta yi kam.

Nafisa yarinya ce ƙarama wadda bata wuce shekarau goma sha shida ba, ita ce ƙaramar budurwa dai a gidansu sauran duk manya ne tana da yayye huɗu mata ringis kuma duk tare suke rayuwa a gidan ba wadda tai aure a cikinsu. Kodayake da me za su yi auren ma, komi kai ke yi ma kanka a gidan indai ka gama primary school to shike nan kai za ka ci-gaba da jan rayuwarka har ka dinga taimakawa iyayen. Hakan yasa yaran su duka maza suka buɗe masu ido, Nafi'u na cikin manyan gwaskayen da suka buɗe wa yaran idanu, domin shi su dukkansu ya haɗe ba wadda bai mu'amala da ita, kowace yaga dama kira yake kuma zuwa take. Sai dai yafi son hulɗa da Nafisa saboda tafi su ƙaranta kuma shi ne namiji na farko da ya fara ratsa Nigeriarta, don haka kafin ya kula yayyenta ya kula ta sau biyar. 
Ranar farko da ya fara amfana da ita Yayarta Hafsa ce ta aiko ta gun shi ya amsar mata Naira dubu (1000) za ta sai abinci, lokacin yana tsaka da kallon wani video na yadda ake shigar yarinya daga shekara 15, duk ya bi ya ruɗe domin babu abin da yake so irin ya ji ya nufi hanya ya ji ta a tsuke gam, sai ya ji tamkar hanyar zuwa Makkah ce yake bi ba ko sisinsa. Tai ta sallama bai ma san tana yi ba hankalinsa na kan wayarsa hannayensa na cikin wandonsa sai nishi yake kamar da gaske shike aikin ba na cikin kallon ba. Sai da ta dage sosai ta sake kwaɗa sallama sannan ya ankara ya ɗago idanunsa da su kai jajir ya watsa mata, sai ya ka kamar ita ce ma a cikin videon da yake kallo. Da wata irin shaƙaƙƙiyar murya ya dube ta ya ce,  "Me zan baki?" Ta dube shi duk da take yarinya amma tasan me yake kallo domin tana ganin yayyenta na kalla duk dare suna nishi har ma idan suna cikin kallon suna aje kallon su dinga yi ma juna abin da suka kalla cikin kallon. Tace mai, "Yaya ce ta ce na zo na amsar mata Naira dubu (1000) za ta sai abinci." Ya dube ta da kyau ya ce, "Ke kin ci abincin ne?"  Ta girgiza kai alamar bata ci ba. Ya ce to shigo daga ciki man kin tsaya a nan sai ka ce zan cinye ki?"   Kai tsaye ta shige domin tana son jin abin da yayyenta ke ji idan suna labarinsu na sunje sun saki kaya an masu alheri sai ta ji ina ma ace ita ce ta saki kayan akai mata alherin nan.  Ganin cewar bai yiwuwa ya samu abin da yake so cikin jin daɗi da nishaɗi yasa ya bata kuɗin ya ce mata ta kai ta dawo ta raka shi wani waje daga can zai sai mata abinci ya kuma bata kuɗi ta aje idan za tai wani abu ta dinga ɗauka. Jin hakan yasa murna ta kama Nafisa tai maza ta kaima Yayarta kuɗin ta dawo ya ɗauke ta a mota bai tsaya ko'ina ba sai wani sabon hotel da aka buɗe, bai damu da tsadar hotel ɗin ba saboda yasan abin da zai ci ma mai tsada ne. 

Bai sha wahalar yi mata bayani ko faɗin manufarsa ba, har ma ya fara jin a ransa anya kuwa wani shegen bai riga shi sanin makamar yarinyar nan ba. Sai dai ya daure ya ce ta je tai wanka ta wanke bakinta sosai ta dawo yana jiranta. Bayan ta fito daga wankan ne ya bata wani mai sai ƙamshi yake ya ce ta shafa ya fesa mata turare sannan ya kashe hasken ɗakin ya jawo ta a hankali yana ayyano matakan da aka bi wajen yarinyar daya gama kallo yana bi akan ta.  Da yake yana da shegen wayau ba kai tsaye ya je ƙuryar ɗakin nata ba sai da ya gama yi mata duk wani salo da wasa da shi bai  taɓa yi ma wata mace shi ba sai ita, ya kuma lura ta gama fita daga Nigeria ta koma Pakistan sannan a hankali ya je inda yake son zuwa. Abin farin cikin kuma ya iske da gaske ba wanda ya taɓa kai ziyara a gun sai shi. Tabbas yarinyar tana da juriya da bajinta sosai domin ta sha wahala a hannunsa amma ta jure hakan yasa da ya gama ya ji yana son ƙarawa ya barta a ɗakin ya ce tai barci kafin ya dawo idan ta tashi ga abinci nan ta ci ya fice ya kira Yayarta a waya ta zo ya sake amsar wani ɗakin ya kai ta can ya ida sauke mata nauyinsa baki ɗaya. Ya sallame ta ya dawo gun Nafisar ya iske tana cin abinci ta gama ya zaro kuɗi ya bata ya ce ta tashi ya maida ta gida, amma zai biya ya sai mata magani kan hanya... Wannan shi ne asalin haɗuwarsa da Nafisa su kam sauran duk su ne suka kawo mai kansu da kansu har shagonsa shi kuma ya amsa tayi don haka bai damu da surutun mutane ba sam, su kansu yaran sun taɓa nuna mai basu yadda ba yana tare da su suna gida ɗaya ba, ya ce to su je su duka kar wadda ta sake nemansa ganin cewa su duka suna ƙaruwa da shi ya sa suka bar maganar suka tafi a hakan, kuma ko banza idan su kai ciki shi ne ke taimaka masu cikin na zubewa don haka suka manta da maganar suna gida ɗaya kowacce burinta ace ita ce yake nema dai. Lokacin da suka ankara da Nafisar ta shiga jerin su sunyi mata faɗa wai ta zama munafuka ta kai kanta inda bata kai ba, saboda son abin duniya, sannu a hankali kuma ita ma suka jefa ta team ɗin su na tashar dare wanda tun suna sa ta tana taimaka masu su ba mai yi mata komai har ta zama 'yar gari a cikinsu tayi a yi mata.

Tana shiga ta zauna akan cinyarsa ya tallabe ta ta baya yana latsa ta tana gantsarewa ya ce,  "Naga kwana biyun nan sai cika kike fa musamman nan, ya nuna breast ɗin ta anya kuwa ba wani labari a cikin nan naki kuwa? Kuma fa na lura jarabarki ta ƙara ƙarfi mu je na ganki sosai gaskiya yau dai nasan ko na yi ajiya ne ban sani ba." Dariya tai ta miƙe tsaye don abin da ya kawo ta kenan gunshi kwanakin nan tana yawan jin sha'awa bi da bi wadda 'yan'uwanta ba su iya taimaka mata akan ta duk yadda za su taru kanta sai dai ta rage hanya amma ba don ta je geji ba shi ne kawai yake kai ta geji saboda ƙarshe ne a duniyar sama.
Suna shiga hotel ɗin aka tabbatar ma shi da an yi gyara yanzu sun daina bada short time sai full time shima sun ƙara farashi sai kawai ya dawo ya ja motar ya je unguwar da students ke kama gida ya ce yana son ɗaki aka gaya mai kuɗin ya lissafa ya ga gwara ya kama ɗaki na shekara akan ya dinga zuwa yana biyan 30k a kwana ɗaya kacal. Nan da nan ya amshi ɗaki ya je ya siyo katifa zanin gado da labule da komai ya dawo shi da ita suka gyara ɗakin  fes sannan ya kawo abinci suka ci ya ja ta suka faɗa duniyar su ta sama. Ya sake jaddada zarginsa akan ta yadda yaga yarinyar na neman ƙure shi, sai da ya yi da gaske sannan suka daidaita hakan yasa suna gamawa ya kai ta gun abokinsa Likita ya ce a duba ta ko ta kamu ne. Gwajin farko aka gano ɗan ƙaramin ciki maƙale  Likitan ya ce a cire koko? Suka kalli juna kowa da abin da yake ji a ransa, ita kam tana tsoron a gane tana da ciki duk da tasan iyaka dai ai mata faɗa ba mai dukanta amma surutun mutane yafi dukan ciwo ai, sai dai kuma yanzu da take da cikin nan tafi jin daɗin abin da suke da Nafi'u sosai, duk rana bata ƙi su yi sau biyar ba saboda yadda take ji a jikinta. Kenan masu ciki na kashewa wannan azabar daɗi har ina.
Shi kuma a nashi tunanin kamar a bar shi ya kai ko wata uku ne sai ya cire shi saboda yanzu yafi samun natsuwa sosai musamman da ya lura da ita kuma Fati nata cikin mugu ne bai san sex kwata-kwata idan ma ya ce zai dinga mata mata tabbas zai asarar sa, shi kam bai taɓa zubar da cikin da ya biya kuɗi aka shaida na shi ne, don haka kawai ya bar na Nafisar zuwa wani time sai ya dinga ɗagawa Fati ƙafa . Wannan shawarar ita ya ɗauka don haka ba a cire cikin ba suka dawo.

Ta yi mamaki sosai da sai bayan sallar Azahar ta tashi, kuma maigidan bai dawo ba, ta ji daɗin yadda ta tashi wasai ba inda ke mata ciwo don haka cikin sauri ta watsa ruwa tai sallah ta nufi kichine cikin sa'ar gaske ta ji tana bala'in son cin fankasun don haka cikin sauri ta haɗa komai ta ɗora har miyar. Kafin ka ce me ta gama, ta zubo mai isarta ta dawo falo ta zauna tana ci tana jin tamkar nama take ci haka ta ji, girkin ya yi mata daɗi sosai.  Tana gama ci ta gyara gidan ta dawo falon ta zauna ta kunna kallo tana jin tamkar bata da sauran damuwa, sam rashin dawowarsa bai ɓata mata rai ba, sai ma take jin dama sai dare zai dawo gidan da ta ji daɗi sosai. Tana cikin tunanin ya faɗo falon don sallama bata cikin abin da yasan da zamanta a rayuwarsa. 
Kallo guda ya yi mata yasan ta koma normal kenan dai mugun cikin ne bai san yana kai mai ziyara. Ya taɓe baki tunawa da Nafisa nata cikin jiranshi yake kodayaushe. Bai bi takan abincin da ta haɗa ma shi ba kawai kwanciya ya yi barci ya kwashe shi. 
Asiya ce tai sallama don haka ta ɗauki tabarma ta kai masu can hanyar ƙofar gida inda ba zai ji me suke cewa ba. Bayan sun zauna Asiya ta ɗebo fankasu ta dawo tana ci tana yi wa Fati bayanin magungunan data kawo mata kusan rabin baƙar leda, wasu ta sha da madara wasu ta sha da zuma wasu ma matsi za tai da su. Fati ta ji daɗin maganin musamman da ta ji daga gun Mama suke. Asiya ta dubi Fati ta taɓe baki tace, "Hala Mala'ikan naki yana ciki ne da har bamu iya zama a falo sai nan?" Fati tai dariyar masifar Asiya, ita Nafi'u ke ma abu amma Asiya ta fita jin haushin shi. Cikin 'yar dariya tace,  "Bai jima da dawowa ba barci yake ban san mu dame shi da hayaniya ne kawai ba don wani abu ba "  Asiya ta sake taɓe baki tace, ya dai kai su idan kaya ne, amma wallahi daga yanzu ni ya gama yi min wulaƙanci na ƙyale shi duk abin da ya yi min sai na rama domin ke daban Asiya daban, da ace aurena yake ma da yanzu na daidaita mai hankali ya dawo jikinsa domin na lura bai da hankali bai san yammacin takashinsa ba... Maganar ta ƙare ganin Fati ta zabura tana kallon gefe Asiya na juyawa suka haɗa ido huɗu da Nafi'u daga shi sai gajeren wando yana kallonsu ranshi a ɓace fuska a turbine. Fati ta duba ƙasa za ta fara ba shi haƙuri Asiya tai caraf ta tada ta zaune tace, "Yaya kar ki ba shi haƙuri domin ba abin da ki kai mai, nice nan na yi mai ldan ma yi mai na yi kuma ba zan ba shi haƙuri ba duk abin da zai yi ya yi daidai nake da shi."
Wata mahaukaciyar dariya Nafi'u yasa ya nufi gidan ya saka sakata ya kulle shi ya  dawo yana kallonsu idanunsa kamar za su faɗo.


To ko me zai faru a gaba, ku biyo Haupha dai don jin yadda za ta kaya.


Haupha........