Yan bindiga sun kaddamar da sabbin hare-hare a Jihar Kebbi
Daga Abbakar Aleeyu Anache.
Rahotanni daga jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya sun bayyana cewa yan ta'adda sun kai hari a kauyen Tadurga a karamar hukumar Zuru.
Mazauna kauyen sun shaida wa Abbakar Aleeyu Anache cewa yan bindigar sun kai harin ne a kan babura sama da 100 tare da bude wa wuta ga al'ummar kauyen da misalin karfe 7 na daren ranar Litinin.
Wasu mazauna yankin sun ce sakamakon tsananin tashin hankali wasu sun tsere cikin daji wasu kuma yan bindigar sun tafi da su.
Kebbi na daya daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalolin rashin tsaro da hare-haren yan bindiga.
managarciya