Ƴar kasuwa ta yanke jiki ta fadi bayan ta zubar da kuɗin ta N275,000 a Abuja 

Ƴar kasuwa ta yanke jiki ta fadi bayan ta zubar da kuɗin ta N275,000 a Abuja 

Wata ƴar kasuwa mai suna Gladys Ibrahim ta yanke jiki ta fadi bayan da ta yi zubar da kuɗin ta har Naira dubu  275 a babbar kasuwar Abaji da ke karamar hukumar Abaji a babban birnin tarayya Abuja a jiya Alhamis.

Wani ganau mai suna Gambo, ya ce matar ta saka hannunta a cikin jakar hannunta domin ta ciro kudin za ta biya wasu buhunan kankana da ta saya a lokacin da ta fahimci cewa babu kudin.

Ya ce a lokacin da matar, wacce ke zuwa daga Auchi a jihar Edo duk ranar kasuwa domin siyan kankana da gyada, sai aka ga ta fadi bayan da ta fahimci kudin nata ba sa cikin jakar.

Gambo ya ci gaba da cewa lamarin ya haifar da fargaba a kasuwar, inda ya ƙara da cewa har sai da wasu ‘yan kasuwa su ka zuba mata ruwa kafin ta farfado.

Kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ba ta ce komai kan lamarin ba.