Gwamnatin tarayya za ta dawo da ci gaba da aikin titin Abuja zuwa Kano

Gwamnatin tarayya za ta dawo da ci gaba da aikin titin Abuja zuwa Kano

Ministan ayyuka, David Umahi ya ce gwamnatin tarayya za ta dinga biyan kamfanin gine-gine na Julius Berger Naira Biliyan 20 duk wata domin kammala aikin titin Abuja zuwa Kano nan da watanni 14.

Kilo mita 82 ne dai ya rage na kammaluwar aikin da aka fara shi tsawon shekaru.

Ministan a yayin ganawa da kamfanin domin duba yadda ake gudanar da aikin, ya koma kan matsalar kudi da ta kawo tasgaro wajen kammalauwar manyan tituna da gwamnatin ta gada.

A wata sanarwa da mai taimaka masa kan fannin yada labarai, Orji Uchenna Orji ya fitar, Ministan ya yi bayanin cewa ayyukan da suka gada sun hada da: Titin da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano   da Titin Legas zuwa Ibadan kashi na 2 da gadar Niger.

Ministan ya sha alwashin kammala ayyukan nan bada jimawa ba.

Tun lokacin tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ne dai aka bada kwangilar aikin gina titin.