Bayani Kan Yadda Aka Sace Sarki Tare Da Mutane 104 a Sokoto
A Najeriya, mazauna yankin gabashin Sakkwato, na ci gaba da kokawa kan yadda matsalar rashin tsaro ke ta daɗa ƙamari a shiyyar.
Sabon Birni da Isa na daga cikin ƙananan hukumomin jihar Sokoto da suka daɗe suna fama da matsalar tsaro.
A yanzu mazauna yankin na cewa lamarin ya yi ƙamari, ta yadda kaso mai yawa na al'ummar suka yi ƙaura zuwa wasu yankuna, lamarin da ya mayar da su ƴan gudun hijira, kuma ya yi cikas ga ayyukan noma, wanda shi ne kusan dukkanin al'ummar yankin suka dogara da shi.
A tattaunawarsa da BBC, ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Sabon Birni ta arewa a majalisar wakilan Najeriya, Aminu Boza, ya ce an sace sama da kashi 90 cikin ɗari na dabbobin yankin.
Ya ce: "Idan ka tashi daga garin Marnona har zuwa Isa ba za ka samu ko mutum ɗaya da ke rayuwa a cikin garuruwan ba."
Ya bayyana cewa an tayar da ƙauyuka kimanin 50 da ke tsakanin garuruwan biyu.
Bayanai sun nuna cewa a baya-bayan nan matsalar tsaron ta yi sanadiyyar sacewa da garkuwa da mutane kimanin 150, ciki har da sarkin Sabon Birnin Gobir, Alhaji Isah Muhammad.
A cewar Aminu Boza, "(Sarkin) na kan hanyarsa ne daga Sokoto zuwa Sabon Birni ne ya ci karo da ɓarayin waɗanda suka sace shi."
Ya ƙara da cewa a yanzu haka ƴan bindigan na neman a ba su maƙudan kuɗaɗe kafin su sake shi.
Tun a shekarar 2011 ne matsalar ƴan fashin dajin ta fara ƙamari a jihohin arewa maso yammacin Najeriya.
Jihohin da lamarin ya fi ƙamari su ne Kaduna, Zamfara, Katsina da Sokoto da Naija.
Masana na ganin cewa matsalar ta taimaka wajen haifar da ƙarancin abinci, kasancewar ƴan bindigan sun kori al'umma da dama daga yankunansu.
Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da ta gabata ta ƙaddamar da wani shirin soji a yankin, sai dai har yanzu matsalar ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a makon da ya gabata, shalkwatar tsaro ta Najeriya ta ce shirin Operation Hadarin Daji na sojoji masu yaƙi da ayyukan ƴan fashin daji ya samu nasarar kashe ƴan bindiga 13 da kama wasu 23 da kuma ƙwato makamai a tsakanin makon ƙarshe na watan Yuli zuwa makon farko na watan Agusta.
Sai dai duk da wannan nasara da jami'an tsaron ke cewa suna yi kan ƴan fashin dajin, al'ummar yankin na arewa maso yamma na ci gaba da kokawa kan yadda lamarin ke ƙara ƙamari.
Ɗan majalisa Aminu Boza ya ce yanzu haka an kai wani matsayin da mutane ba su da halin karɓo ƴan'uwansu da ake garkuwa da su.
Ya ce: "Babu kuɗin da za a karɓo su. Duk mutanen da aka sace ba su da naira 10,000 a gidajensu da za a iya amfani da su."
Haka nan ya bayyana yadda rashin tsaron ke ƙara ta'azzra matsin tattalin arziƙi da al'ummar yankin ke ciki.
"Sun hana mu noma, yanzu a Sabon Birni muna da eka fiye da 20,000 wadda ba a noma ba
"Wallahi akwai mutumin da a baya yake noma kankana ta fi ta naira miliyan 20, yau babu mai iya noma dami ɗaya, sai ɗaiɗaikun mutane," in ji ɗan majalisar.
managarciya