Gobara ta tashi a gidan Gwamnatin Katsaina
Wata gobara ta tashi da safiyar yau Litinin a ɗaya daga cikin zaurukan gidan Gwamnatin Jihar Katsina.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa zauren na haɗe ne da ofishin gwamnan jihar Katsina, inda gwamnan ke ganin mutane masu muhimmanci da suke ziyartarsa.
Babu cikakken bayani kan abin da ya haddasa gobarar da kuma yawan ɓarnar da ta yi.
Rahotanni sun ce Gwamna Dikko Umaru Radda na yankin Funtua lokacin da gobarar ta tashi.
Ya je halartar tattaunawa ne da mutanen yankin domin jin abin da suke buƙata.
managarciya