Dattawan Arewa Sun Koka Akan Yadda Ake Kashe Yan Arewa A Kudancin Nijeriya

Dattawan Arewa Sun Koka Akan Yadda Ake Kashe Yan Arewa A Kudancin Nijeriya

 

Kungiyar Dattawan Arewa NEF, ta bayyana matukar damuwarta kan yadda ake ta samun yawaitar batanci da kashe-kashen yan Arewa a Kudancin Najeriya, musamman Kudu maso Gabas. Rahoton Daily Trust Daraktan yada labarai da bayar da shawarwari na NEF, Dr Hakeem Baba-Ahmed ne ya bayyana matsayin kungiyar a cikin wata sanarwa a jiya. 

Hukumar ta NEF ta ce, Kisan da aka yi wa ‘yan kasar Nijar kwanan nan a Jihar Imo, anyi shine bisa tunanin yan yankin Arewa ne, 
Wanda lamari ya shafi cin zarafi, kama mutane ba bisa ka’ida ba, hare-hare da kashe ‘yan Najeriya daga yankin Arewa. 
Sanarwar ya kara da cewa da alama kungiyoyin da ke kai wa ‘yan Arewa hari suna samun kwarin guiwa ne daga shurun shuwagabanni da rashin daukar matakan da suka dace daga jami’an tsaro. Kungiyar NEF ta sake jawo hankalin jama’a kan illolin da ke tattare da kara ta’azzara al’amura da tada hankali. 
Kungiyar ta yi kira ga jami'an tsaro da duk wasu masu ruwa da tsaki da su kare rayukka da dukiyar mutanen Arewa dake zaune a Kudancin Nijeriya.