Gwamnonin Arewa Da Suke da Iyaka Da Kasar Nijar, Sun Nunawa Tinubu Illar Yakar Kasar

Gwamnonin Arewa Da Suke da Iyaka Da Kasar Nijar, Sun Nunawa Tinubu Illar Yakar Kasar

Daga Comr Abba Sani Pantami.

A yau Lahadi mai girma Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi  FCA, da mai Girma Gwamnan jihar Katsina Dr. Dikko Umaru Radda tare da sauran Gwamnonin jihohin Kebbi, Sokoto da Yobe da suka hada iyaka da kasar Nijar, sun gana da Shugaban kasar Najeriya Bola Ahmad Tunubu kan yunkurin shugaban kasar da ya tura neman amincewar majalisa na yakar kasar Nijar.

Gwamnonin sun yiwa shugaban kasar bayanin irin yadda lamarin zai shafi mutanan jihohin su, na illar da hakan zai haifar ga makomar al'ummarsu da suke da iyakar kasar da Nijar.

Mutanen arewa ba su maraba da wannan matakin amfani da soja ganin yanda kowa yasan yaki Yana daidaita kasa ne ya kawo masu ci baya sosai.

Gwamnoni masu iyaka da Nijar suna ganin da an yi yaki mutanensu za su cutu matuka musamman yanda ake fama da matsalar tsaro a jihohinsu.