Yanda Ake Milk Samosa Mai Daɗin Gaske

Yanda Ake Milk Samosa Mai Daɗin Gaske

Yanda Ake Milk Samosa 

Kayan da ake bukata: 

Nama
Filawa
Tattasai/albasa
Gishiri
Maggi
Nonstick frying pan.

Yanda zaki hada: zaki wanke Naman ki ki Dora kan wuta ya dahu sosai, Sai ki sauke idan ya huce Sai ki daka Naman kaman zakiyi dambun nama, Sai ki yi jajjagen tattasai da albasa ki Dora kan wuta ki tafasa ruwan ya shanye.

Sai ki hada tattasan da nama ki saka maggi daidai dandanon ki. Sai ki dauko filawa ki kwaba shi ruwa ruwa Kaman kunu.

Sai ki Dora frying pan din ki kan wuta ki shafa kullun kan frying pan din zai taso sama Sai ki cire ki Dora kan try, Sai ki sa Yuka ki yanka shi biyu Sai ki saka nama ciki kiyi rolling.

Haka zaki yi har ki gama  Sai ki soya.

Daga Safiya Usman