Yadda Ake Hada SOYAYYAR SHINKAFA

Yadda Ake Hada SOYAYYAR SHINKAFA
BASAKKWACE'Z KITCHEN
 
 
  SOYAYYAR SHINKAFA
 
INGREDIENTS
Shinkafa
Karas
Koren wake
Tattasai
Attarugu
Albasa
Magi
Kori
Garin tafarnuwa da citta
barkono
butter
 
 
METHOD
A ɗora tukunya da ruwa a cikinta har sai ya tafasa sannan a Ɗauko shinkafa  a wanke a zuba a ciki. Idan ta dan tafasa kamar mintina talatin , sai a sauke a wanke da  ruwa a tsame ta a matsami ruwan ya tsane. 
 
A sake ɗora wata tukunyar a wuta sannan a zuba butter   a yayyanka albasa a zuba ta soyu sosai. Sannan  a ɗauko garin citta da tafarnuwa da magi da kori sai a ci gaba da gaurayawa. Sannan a zuba su karas da koren tattasai da attarugu da shinkafar sannan sai a gauraya sai a rage wuta a rufe tukunyar da marufi na tsawon minti 20 sannan a ɗauko busashen barkono wanda ba a daka ba a sa a sama,ya ƙara minti goma sannan a sauke 
 
 
08167151176
MRSBASAKKWACE