Ana fargabar tashin bama-bamai Uku a cikin mako guda a jihar Zamfara

Ana fargabar tashin bama-bamai Uku a cikin mako guda a jihar Zamfara

Ana fargabar tashin bama-bamai Uku a cikin mako guda a jihar Zamfara

Al’ummomin karamar hukumar Maru da ke jihar Zamfara sun samu tashin bama-bamai uku a cikin mako guda, lamarin da ya sanya fargabar karuwar ayyukan ‘yan ta’adda a jihar.

Fashewar ta uku ya faru ne da safiyar Juma’a lokacin da wata motar daukar kaya dauke da hatsi ta taka bam din da ake zargin ‘yan bindiga ne suka dasa a kan hanyar Gusau zuwa Dansadau.

Wani dan yankin mai suna Mannir Sani wanda ke cikin motar daukar kaya ya ce bama-bamai biyu sun tashi a lokaci guda.

Sani ya ce, Ina cikin motar tare da wasu fasinjoji, kwatsam ba zato ba tsammani wasu bama-bamai guda biyu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne suka dasa suka tashi a wurare daban-daban a kan hanyar.

Daya daga cikin bama-baman ya tashi ne a kan titin Dansadau da Malamawa, wani kuma ya faru ne a kan titin Malele, duk a gundumar Dansadau.”

Ya ce ranar Juma’a za su je kasuwar Dansadau domin sayo hatsi a lokacin da lamarin ya faru.

 Abbakar Aleeyu Anache