Zargin Aikata Fyade: 'Yan Sanda a Borno Sun Kama Mutane 85

Zargin Aikata Fyade: 'Yan Sanda a Borno Sun Kama Mutane 85

‘Yan sanda a  jihar Borno sun  kama wasu mutane 85 da ake zargi da aikata laifin fyade da sauran miyagun laifuka, a kananan hukumomin Maiduguri, Jere da Biu.

Laifukan da ake zargi sun hada da hada baki wajen kisan kai da kuma fashi da makami a  tsakanin watan Oktoba da Disambar shekarar da ta gabata ta 2023.
 
Da yake gabatar da wadanda ake zargin a garin Maiduguri, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan Jihar,  ASP Hahum Daso ya bayyana cewa: “A cikin kararraki 49 da aka samu, an yanke wa mutane 27 hukunci,” yana mai cewa an yanke musu hukunci 14 tare da  gudanar da bincike, yayin da aka gurfanar da wasu 31 a gaban kotu.
 
Ya kara da cewa, rundunar hadin gwiwa da ke yaki da batagari  ta ‘yan sanda ce ta kama wadanda ake zargi da hada baki, taro ba bisa ka’ida ba, mallakar makamai da kuma zargin hannu da ta'ammali cikin miyagun kwayoyi.
 
Yayin da yake bayyana wasu daga cikin laifukan, Kakakin ya ce: "Fatima Abatcha wacce ta kware da Sayar wayoyin hannu  da kuma  Mohammed Isa za a gurfanar da su a gaban kotu bisa laifin satar wayoyin hannu."