Kashe Malami a Zamfara: yadda aka kama 'yan sa-kai 10
Daga Nabila Khamis.
Mambobin kungiyoyin 'yan sa kai guda 10 ne aka samu nasarar damkewa bisa zarginsu da kashe sanannen Malamin addinin Musulunci a jihar Zamfara.
Sheikh Abubakar Hassan Mada ana zargin 'yan sa kan da yi mashi kisan gilla ne a garinshi na Mada da ke karamar hukumar mulki ta Gusau a ranar Talata.
A wani bayani da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara Sulaiman Bala Idris ya fitar ya bayyana cewa wadanda ake zargin da aika-aikar 'yan sa kai ne ba mambobin bayar da kariya ga al'ummar jihar ba ne na CPG.
Bayanin ya ci gaba da cewa 'yan sa kan da aka kama basa daga cikin wadanda gwamnati ta dauka kuma ta basu horo domin gudanar da aiyukan samar da tsaro domin basu cikin dakarun CPG na jihar.
Ya ce gwamnatin jihar Zamfara ta samu wani labari mai ratsa zuciya a kan kisan gillar da aka yi ma Shehin Malamin a garin Mada. Inda ta bayyana shi a matsayin abin takaici da ya kamata a kare abkuwar shi.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar Zamfara ta dauki wannan al'amari da muhimmanci kuma a shirye take ta tabbatar duk masu hannu ga wannan aika-aikar sun girbi abin da suka shuka.
Ya kara da cewa tuni binciken farko-farko da 'yansanda suka gudanar ya gano cewa daya daga cikin 'yan-sa-kai da aka kama tsohon dalibin Shehin Malamin da aka kashe ne.
managarciya