Sallah: A cikin shekara daya Amadun Alu ya gina sabuwar Sokoto-----Sarkin Sudan Jabo
Sarkin Sudan a sakonsa na barka da sallah ga Gwaamnan Sokoto ya nuna farincikinsa ga jagorancin Dakta Ahmad Aliyu
Dan kishin jihar Sokoto Alhaji Nuraddeen Atahiru Jabo waton Sarkin Sudan na Jabo ya bayyana yanda Gwamnan Sokoto Dakta Ahmad Aliyu Sokoto ya mayarda jihar a cikin karamin lokaci kasa da shekara daya da rantsar da shi matsayin gwamnan Sokoto.
Sarkin Sudan a sakonsa na barka da sallah ga Gwaamnan Sokoto ya nuna farincikinsa ga jagorancin Dakta Ahmad Aliyu ya ce a cikin shekara daya Amadun Alu ya gina sabuwar Sokoto mai dauke da cigaba, domin shi mutum ne mai fada da cikawa.
“Wannan gwamnati tana ta fitowa da shiraruwa da tsare-tsare da suke da matukar muhimmanci ga rayuwar talakkan Sokoto.
“Duk da matsalolin tattalin arziki da ake fama da su a Duniya da Nijeriya ba su hana Gwamna Amadu yin wasu aiyukka da suka kara bunkasa birnin jiha, domin ganin ya shiga cikin mayan birane da aka kawata ake tinkaho da su a Nijeriya.
“Gwamna nada kaifin basirar samar da abubuwa sabbi na cigaba kusan kowa ya sallama Dakta Ahmad Aliyu ya cika alkawalin da ya dauka na gina sabuwar jihar Sokoto, saura da mi a cigaba da yi masa addu’a aiyukkan da ya dauko Allah ya ba shi karfin guiwa kammala su domin Sakkwatawa su kara more romon Dimukuradiyya,” kalaman Nuraddeen Jabo.
managarciya