Malaman Jami'o'in Najeriya 20 Suka Rasa Ransu Sakamakon Yajin Aikin ASUU

Malaman Jami'o'in Najeriya 20 Suka Rasa Ransu Sakamakon Yajin Aikin ASUU

Daga Abbakar Aleeyu Anache.

Akalla malaman jami'o'in Najeriya 20 ne suka raya rayukansu bayan sun shiga kunci na rashin albashi sakamakon yajin aikin da jami'o'in kasar ke yi.

Kusan watanni 7 kenan da gwamnatin kasar ta daina biyan malaman jami'o'in albashinsu tana mai cewa babu aiki babu albashi.

Wasu daga cikin malaman sun shaida wa sashan Hausa na RFI cewa lallai sun yi rashin mambobinsu saboda damuwar da suka shiga.

Wannan kuwa na faruwa ne sakamakon cewa malaman sun dogara ne kacokan kan albashin ganin cewa hanya daya tilo kenan da suke samun kudaden ciyar da iyali.