'Yan Sanda Sun Kama Matashi Ɗan Shekara 18 Kan Zargin Kashe Abokinsa a Kano

'Yan Sanda Sun Kama Matashi Ɗan Shekara 18 Kan Zargin Kashe Abokinsa a Kano

Rundunar 'Yan Sandan Najeriya Sun Cefke Wani Matashi Dan Shekara 18 Kan Zargin Kisan Abokinsa,

Daga Abbakar Aleeyu Anache

Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Kano ta cafke wani matashi ɗan shekara 18, Saminu Bala, bisa zargin kisan abokinsa a Kofar Mazugal a birnin Kano.

Daily Trust ta rawaito cewa Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da kisan cewa cacar-baki ce ta ɓarke tsakanin Bala da marigayi Ibrahim Khalil sai shi Bala ɗin ya daki Khalil, lamarin da ya janyo mutuwar sa.