Home Uncategorized Fetur Zai Iya Haura N400, Gwamnoni Sun Bada Shawarar Gaggauta Janye Tallafi 

Fetur Zai Iya Haura N400, Gwamnoni Sun Bada Shawarar Gaggauta Janye Tallafi 

8
0

 

Mai girma Gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya bada shawarar a gaggauta cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya take biya. 

Vanguard tace Gwamnan ya yi wannan kira ne a wajen taron NESG da ake yi a garin Abuja.
Da aka tambayi gwamnan na jihar Kaduna a kan abin da ya kamata gwamnatin tarayya tayi, sai yace a gaggauta watsi da tsarin tallafin man fetur. 
Gwamnan yace gwamnonin jihohin kasar nan 36, jami’an gwamnatin tarayya da majalisar tattalin arziki sun amince a cire tallafin tun Satumban 2021. 
Nasir El-Rufai yake cewa ya yi mamaki da gwamnatin Muhammadu Buhari ta ki dabbaka wannan matsaya duk da matsalar da biyan tallafin ya jawo. 
A cewar Gwamnan, daukar nauyin farashin fetur da gwamnatin Najeriya take yi, ya jefa kasar a cikin kalubale, baya ga rashin gaskiya da ake tafkawa. 
A rahoton Leadership, an ji El-Rufai da takwarorinsa na Edo da Gombe, Gwamna Inuwa Yahaya da Gwamna Godwin Obaseki sun yi wannan kira. 
Gwamnonin jihohin sun ce ya kamata gwamnatin tarayya tayi maza-maza ta dakatar da tsarin biyan tallafin fetur, kuma a inganta wutar lantarki. 
A wannan taro wanda shi ne na 28 a tarihi, gwamnonin sun nemi gwamnatin Muhammadu Buhari mai-ci da ta sauya fasalin tattalin arzikin Najeriya. 
Yayin da El-Rufai ya dage kan harkar man fetur, rahoton yace Mai girma Obaseki ya nuna damuwarsa a kan sha’anin lantarki domin a samu ayyukan yi. 
Shi kuma Gwamna Inuwa na jihar Gombe yace ya kamata a canza fasalin kasa ta yadda kowace jiha za ta amfana da bangaren da tayi fice kan ‘yaruwarta.
A baya kun ji labari shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna gwamnatin tarayya tana kashe makudan kudi a kan tallafin man fetur duk shekara. 
Shugaban kasar yake cewa gwamnatinsa ta batar da N1.5tr a cikin watannin shidan farkon 2022. Wannan ne ya sa aka cire tallafin daga kasafin kudin badi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here