Don  Samar Da Maslaha Da Zaman Lafiya A Sakkwato Nake Takarar Gwamna---lbrahim Liman Sifawa

Don  Samar Da Maslaha Da Zaman Lafiya A Sakkwato Nake Takarar Gwamna---lbrahim Liman Sifawa

 

Dan takarar gwamnan Sakkwato  a jam'iyar ADP Dakta Ibrahim Muhammad Liman Sifawa ya bayyana manufarsa ta shiga siyasa da yin takarar gwamna a 2023 wanda hakan zai taimaki jama'ar jiha.

Dakta Ibrahim Liman  a taron masu ruwa da tsaki da jam'iyarsa ta kira domin soma aiyukkan kamfen takarar gwamna da hukumar zabe ta bayar da damar farawa a wannan satin ya ce duk wanda ya shigo tafiyarmu maslaha yake nufi da son ciyar da jiha a gaba da samun zaman lafiya.
"sanin kowa ne yekuwar zabe an soma kamar yadda hukuma ta aminta, hakan ke nuna mu fara aiyukkanmu da nufin janyo hankalin mutane su san kansu da hakkinsu hakan ne zai bambanta mu da sauran jam'iyyun siyasa.

"mun damu sosai ga abin da ke faruwa a jihar nan, ba wanda ya gamsu da abin da ake yi a tafiyar da gwamnati a yanzu, kuma ba wani daban zai zo ya gyara ba, mu dai ne za mu hadu don kawo gyara, hakan ya sa muka gayyaci matasa da mata musamman dake da rinjayen kuri'a su zo a hada kai don kwato hakkinmu domin gaba ta yi kyau," a cewar Dakta Sifawa.

Ya ce sun kira taron shugabanni ne domin kafa kwamitocin kamfe a hukumance domin yin aiki tare cikin mutuntawa, kuma samar da fahimtar juna don tafiya tare matukar ba mu hada kai ba akwai kalubale a gabanmu, wannan ne manufarmu a tafiyarmu.
Sifawa ya ce sun ambaci tafiyarsu da cewa sabuwar hanya domin tana da bambanci da abin da ake yi yanzu "kuma ana bukatar sakamako na daban dole ko a samu tafiya ta daban, shi ne manufa in ka gamsu da mu ka zo a yi tafiya tare, muna tafiya da mata da matasa bayan zamansu kashin bayan tafiyar dimukuradiyya kuma su ne ke shan wuyar jam'iyyun siyasa don haka muke son a jingine halin kura da shan bugu gardi da karbar kudi," in ji Dakta Liman Sifawa.