Zan tabbatar da tsaro ya samu  kafin na sauka -- Buhari

Zan tabbatar da tsaro ya samu  kafin na sauka -- Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya sha alwashin kawo ƙarshen matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta kafin cikar wa’adin mulkinsa.

BBC ta ruwaito cewa shugaba Buhari, ya furta hakan ne a wurin bikin bayar da lambobin girmamawa ga mashahuran mutanen da gwamnati ta karrama a birnin tarayya Abuja.

Ya ce yana son ya jaddada alwashin da ya sha a lokacin bikin tunawa da ranar samun ƴancin kan Najeriya na cewar burinsa shi ne ya miƙa wa shugabannin da za a zaɓa ragamar mulki ba tare da matsalar tsaro ba.

Haka kuma ta ruwaito cewa, yayin taron, shugaban ya ƙara da tunasar da waɗanda suka samu lambar girmamawar cewa ba an ba su ita ba ne domin kwalliya, sai domin tunatsr da su nauyin da ke kansu a matsayin su na ƴan ƙasa nagari.