Kotun Shari'ar Musulunci ta bayar da umarnin kama Dakta Abdul'aziz Idris

Kotun Shari'ar Musulunci ta bayar da umarnin kama Dakta Abdul'aziz Idris


Kotun Shari'ar Musulunci da ke jihar Bauchi ta sake umartar kama Dakta Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi. 
Kotun ta dauki matakin ne kan kin halartar zaman kotun don ci gaba da shari'ar da ake yi, cewar Tribune. 
Mai Shari'a, Malam Hussaini A. Turaki ya ki amincewa da korafin lauyan wanda ake kara kan umarnin Kotun Daukaka Kara a Jos. 
Bayanai sauraran korafe-korafen dukkan bangarorin, alkalin kotun ya ce dole wanda ake zargin ya gurfana a gaban kotun duk belin da aka bayar a baya. 
Lauyan masu karar, UB Umar da ke ma'aikatar Shari'a a jihar ya ce sun tura masa sako don ya halarci zaman kotun amma ya bayyana a fili cewa ba zai zo ba. 
"Mun tura masa takardar halartar kotu amma ya ki amsa gayyatar inda a bayyane ya ce ba zai zo ba. 
"Kotun ta umarce shi da ya zo kotun ya tabbatar mata me yasa ba zai zo ba a zaman da ya gabata, idan ya ba da hujjoji shikenan.
"Mun tura gayyata ya ki ya zo, mun bi duk wata hanya bai zo ba, abu na gaba shi ne shaidar kamu daga jami'an tsaro wanda za mu kawo shi zuwa ranar 24 ga watan Janairu." 
A bangarenshi, lauyan wanda ake zargin, Ahmad M Umar ya ce duk da umarnin cafke malam, ya kamata kotun ta mutunta umarnin Kotun Daukaka Kara a Jos. 
Kotun ta dage ci gaba da sauraran shari'ar har ranar 24 ga watan Janairun wannan shekara, cewar Leadership.