Gwamnonin Najeriya Sun Hada Karfi Da Gwamnatin Tarayya Domin Murkushe 'Yan Ta'adda

Gwamnonin Najeriya Sun Hada Karfi Da Gwamnatin Tarayya Domin Murkushe 'Yan Ta'adda
Gwamnonin Najeriya Sun Hada Karfi Da Gwamnatin Tarayya Domin Murkushe 'Yan Ta'adda
 
Daga Abbakar Aleeyu Anache, 
 
Gwamnatin Najeriya da gwamnonin yankin arewa maso yammacin kasar da kuma jihar Neja sun sanar da tsara wani shirin hadin gwuiwa domin kawo karshen yan ta'adda a yankunan guda biyu.
 
Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa'i wanda ya bayyana hakan ya ce lokaci ya yi da za a yita ta Kare, inji sanarwar. 
 
El-Rufa'i yace lokaci yayi da gwamnantin Najeriya da kuma gwamnatocin jahohi za su kawo karshen yan ta'adda da suka addabi yankunan karkara da biranen kasar.