Yawaita shara a jihar Sakkwato al’umma sun nemi gwamnati ta taimaka musu
"A taimaka a kwashe mana sharar nan don kawar da annobar kwalara da cizon sauro da wasu da ba mu ma sani ba, da ba mu iya maganinta da kanmu, tun tashina shara ba ta taba yawa kamar wannan ba ko bako zai shigo gari in ta gefen nan zai zo akan yi masa misali da Bolar nan. Akwai mamaki a samu gwamnati da za ta bari a tara shara kamar haka a tsakiyar mutane a wannan lokaci na damina a barta.
Jama’ar jihar Sakkwato musamman wadanda ke kan Titin Maituta cikin birnin jiha sun nuna matukar damuwarsu yanda shara ke yawaita a ba tare da gwamnatin jihar ta yi wata hobbasar kawarda lamarin ba.
Bola takan haifar da ciruta kama da irin Kwalara da cutar cizon saura da wasu ciruta baki dake kama mutane domin cin abinci ko kazantar ruwan sha da muhali.
Titin Mai Tuta kusan shi ne cibiyar Bola a birnin jihar domin a can ake tara shara fiye da ko’ina har jami’an kula da muhali ke kwaso shara a wani wuri su kawo a wurin yanda tulin sharar ya yi yawa a wurin, tsawon lokaci ba a kwashe ta ba ne ya ja hankalin mutane da korafi kanta abin da ya sanya wakilinmu ya tattauna da mutane kan halin da suke ciki a makwabtaka da suke yi da sharar.
Tijjani Alhassan mai shekara 45 a unguwar ya ce shi mazauni unguwar ne kuma duk in da shara ke fitowa ya sani a kawo ta unguwarsu, "a wannan lokaci wurin nan ya tara sharar da ba mu taba gani irin ta ba tun da muke a unguwar nan mun kai korafi kan wannan saharar ba wani cigaba da aka samu. A takaice ba mu san lokacin da za a zo kwasar sharar nan ba har annoba mun samu wadda muke alakantawa da sharar nan.
"Duk mai zama anan hakuri yake yi da maneji domin ba dadi har Allah ya kawo lokacin da za a kwashe sharar, hira in za ka yi a waje sai ka yi amfani da ganyen dogon yaro saboda korar sauro." a cewarsa.
Ya yi kira ga gwamnati ta sanya a kwashe masu sharar ko a rage yawanta in kwasar zai yi wuya domin kiyon lafiyasu ta jiki da rayuwa.
Ibrahim Suleima mai shekara 40 ya ce zamansa na kwabcin Bola yana fuskantar kunci kala-kala ba sa cikin jindadi sun yi korafi a wuraren da yakamata amma ba a zo ba har sun dangana.
"Kungiyoyin sa-kai sukan zo taimako amma a hana su kar a ce gwamnati ta kasa, yanzu masu abincin sayarwa sun bar wannan layin da bola take, domin ko sun kasa ba wanda ke zuwa saye don gudun daukar cuta, a halin da ake ciki gidaje hudu ne suka koma kango domin wadanda ke cikin gidajen sun tashi saboda wannan sharar, har da wani mai shagon yin tagogin alminiyum ya tafiyarsa mun yi roko ba a yi ba amma dai mun san muna da hakki ga gwamnati.
"A hasashen da muka yi dakyar ba a gaji wannan shara ga wannan gwamnati mai ci ba domin da wahalar gaske ta iya kwashe sharar nan, mun so a kwashe ta tun tana tifa 30 ko 50 har ta kai 100, a yanzu a kiyasi tifar sharar dake wurin zai kai tifa 4000 kuma a rage sauranta."
Ibrahim ya ci gaba da cewa a kwanan baya an zo kwasar sharar nan muna lissafi a debi sama da tifa 270 a lokacin kamar ba a kwashi komai ba.
"Muna kira ga gwamnati ta kwashe mana in da magudanar ruwa take da kusan gidajen mutane don wadan da suka tashi su dawo, domin za a gaji wannan tulin sharar ga gwamnatin nan, za ka iya samun sharar da ta yi shekara daya da wata shida a wurin nan da ba a kwashe ba."
Ya ce sai da suka yi korafi ga hukumar kula da birnin Sakkwato kan kawo shara a mota daga wani wuri, sai suka hada kai a unguwa ba za su bari wanda ya kawo shara a mota ya zube ba sannan aka daina hakan.
"A taimaka a kwashe mana sharar nan don kawar da annobar kwalara da cizon sauro da wasu da ba mu ma sani ba, da ba mu iya maganinta da kanmu, tun tashina shara ba ta taba yawa kamar wannan ba ko bako zai shigo gari in ta gefen nan zai zo akan yi masa misali da Bolar nan. Akwai mamaki a samu gwamnati da za ta bari a tara shara kamar haka a tsakiyar mutane a wannan lokaci na damina a barta.
Alhaji Bello Jegawa wanda ya yi shekara 30 a unguwar ya ce suna cikin kalubale fiye da wata uku ba a kwashe masu shara ba, sun yi ta kai korafi ga hukuma.
"A kwanan baya matasa suka rika kunna wuta a sharar sai hayaki ya shiga gidajensu duk wani mai tsoho da yake da asma sai an fita da shi wata unguwa kafin daga baya a mayar da shi." a cewarsa
Ya yi kira ga gwamnati ta kwashe masu sharar nan domin sun san ba abin da ya gagari gwamnati matukar ta so.
Wakilinmu ya tuntubi kwamishinan ma'aikatar Muhali a jihar Sakkwato Alhaji Sagir Attahiru Bafarawa kan maganar a waya bai daga ba an yi masa sakon waya bai ce uffan ba, kuma baya ofis har zuwa hada rahoton, ba a san dalilin da ya kawo tsaiko a kwasar shara a birnin Sakkwato sama da wata uku ba.
managarciya