Sokoto:Kotu Ta Tsige Ɗan Majalisar Tarayya, Ta Umarci Hukumar INEC Ta Shirya Sabon Zaɓe

Sokoto:Kotu Ta Tsige Ɗan Majalisar Tarayya, Ta Umarci Hukumar INEC Ta Shirya Sabon Zaɓe

 

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisa ta tsige ɗan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar Yabo da Shagari, Umar Yusuf  Yabo. 

Kotun ta kuma umarci Umar Yabo (Ɗanmaje) ya biya wanda ya shigar da ƙara N500,000 a matsayin ladan wahalar da shi. 
Shugaban kwamitin alkalai uku na kotun mai shari'a  Ashu A. Ewah ne ya karanto hukuncin, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito. 
Ya bayyana zaɓen da aka yi a mazaɓar Yabo/Shagari a matsayin wanda bai kammalu ba. 
Sauran alkalan da suka yanke hukuncin sun haɗa da mai shari'a Helen N. Hamman Joda da mai shari'a Ali T. Changbo. 
Mai shari'a Ewah ya bayyana cewa zaɓen da INEC ta gudanar a 2023 da wanda ta ƙarasa a ranar 3 ga watan Fabrairu, 2024 cike yake da magudi. 
Sakamakon haka ya umarci hukumar zaɓen ta sake shirya ƙarishen zaɓe cikin watanni uku masu zuwa domin tantance sahihin ɗan majalisar Yabo da Shagari.
Manema Labarai sun tattaro cewa za a gudanar da sabon zaɓen a rumfuna huɗu a ƙananan hukumomin Yabo da Shagari.
Runfunan zaɓen sun hada da Dagawa Maji Kira, Dagawa Mai Zane, Shiyar Magaji, Kesoji Shiyar Hakimi, Jaredi Maji Kira, da Mazoji. 
Bugu da kari, kotun ta umarci INEC da ta karɓe takardar shaidar cin zabe da ta ba Umar Yusuf Yabo. 
Magoya bayan PDP a yankin suna ganin ba wani abin tayar da hankali  a hukuncin domin suna da damar daukaka kara a kotu ta gaba, in ba a yi nasara ba suna iya cin zaben su kamar yadda suka samu a farko.