Neman Kujerar Shugaban Marasa Rinjaye:  A Gobe Tambuwal Zai San Matsayinsa

Neman Kujerar Shugaban Marasa Rinjaye:  A Gobe Tambuwal Zai San Matsayinsa

A yayin da majalisar dattawa ta ke shirin yin zama a ranar Talata, hankali duk ya karkata ga wadanda za su samu shugabancin bangarori. 

Rahoto ya zo daga Daily Trust cewa Michael Opeyemi Bamidele Bamidele (APC, Ekiti) da Aminu Waziri Tambuwal (PDP, Sokoto) su na kan gaba a takarar. 
A makon nan za a zabi shugaban masu rinjaye da shugaban marasa rinjaye. 
Haka zalika za a zabi sauran shugabanni shida da ake da su a majalisar. 
Sai dai Sanata Muhammad Ali Ndume (APC, Borno) da Sanata Muhammad Adamu Aliero (PDP, Kebbi) za su gwabza da Bamidele da Tambuwal. 
Ali Ndume da mataimakinsa a kwamitin yakin neman zaben Akpabio/Barau, Sanata Bamidele su na harin kujerar shugaban masu rinjaye daga APC. 
Ndume ya taka rawar gani a zaben Akpabio kuma ya taba rike wannan kujera, sai dai Sanatan na Ekiti ya fito daga yankin da ya dace a kai kujerar. 
A bangaren marasa rinjaye, wasu shugabannin jam’iyyar PDP su na goyon bayan tsohon Gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal ya kare hakkinsu. 
Sai dai Nyesom Wike da mutanensa su na yakar Tambuwal kamar yadda su ka sha bambam da jagororin jam’iyyar a zaben majalisar wakilan tarayya. 
Jaridar ta ce tsohon Gwamna kuma Sanatan Kebbi ta tsakiya a majalisar dattawa, Muhammad Adamu Aliero ya nuna ya na sha’awar wannan kujera. Aliero ya na kan wa’adinsa na hudu kenan a majalisa, ya lashe zabe a 2007, 2015, 2019 da 2023.